Sourate: Suratu Yunus

Verset : 76

فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰذَا لَسِحۡرٞ مُّبِينٞ

To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wurinmu sai suka ce: “Lalle wannan tabbas tsafi ne bayyananne.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 77

قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمۡۖ أَسِحۡرٌ هَٰذَا وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّـٰحِرُونَ

Musa ya ce: “Yanzu kwa riqa ce wa gaskiya (tsafi) lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara?”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 78

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَلۡفِتَنَا عَمَّا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا نَحۡنُ لَكُمَا بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka raba mu da abin da muka sami iyayenmu a kansa, ku kuma (kai da Haruna) ku zamanto ku ne masu girma a bayan qasa? Mu kam ba za mu yi imani da ku ba!”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 79

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

Fir’auna kuma ya ce: “Ku zo mini da duk wani qwararren matsafi.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 80

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ

To lokacin da matsafan suka zo, sai Musa ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 81

فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

To lokacin da suka jefa (kayan tsafinsu), sai Musa ya ce: “Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne; lalle ko Allah zai vata shi. Lalle Allah ba Ya gyara aikin mavarnata



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 82

وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

“Allah zai tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa masu manyan laifuka sun qi.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 83

فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٞ مِّن قَوۡمِهِۦ عَلَىٰ خَوۡفٖ مِّن فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِمۡ أَن يَفۡتِنَهُمۡۚ وَإِنَّ فِرۡعَوۡنَ لَعَالٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

To ba wanda ya yi imani da Musa sai wasu ‘yan samari daga mutanensa don tsoron kada Fir’auna da mutanensa su azabtar da su. Kuma lalle Fir’auna ya tabbata mai girman kai ne a bayan qasa. Lalle kuma shi yana cikin mavarnata



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 84

وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰقَوۡمِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيۡهِ تَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّسۡلِمِينَ

Musa kuma ya ce: “Ya ku mutanena, idan har kun yi imani da Allah, to a gare Shi kawai za ku dogara in kun kasance Musulmai



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 85

فَقَالُواْ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَا رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Sai suka ce: “Ga Allah kaxai muka dogara. Ya Ubangijinmu, kada ka sanya mu zama fitina ga mutane azzalumai



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 86

وَنَجِّنَا بِرَحۡمَتِكَ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

“Ka kuma tserar da mu da rahamarka daga mutane kafirai.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 87

وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوۡمِكُمَا بِمِصۡرَ بُيُوتٗا وَٱجۡعَلُواْ بُيُوتَكُمۡ قِبۡلَةٗ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma Muka yi wa Musa wahayi shi da xan’uwansa cewa: “Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla.” Ka kuma yi wa muminai albishir (da samun nasara)



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 88

وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَآ إِنَّكَ ءَاتَيۡتَ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَأَهُۥ زِينَةٗ وَأَمۡوَٰلٗا فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِكَۖ رَبَّنَا ٱطۡمِسۡ عَلَىٰٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ وَٱشۡدُدۡ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُواْ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ

Musa kuma ya ce: “Ya Ubangijinmu, lalle Ka bai wa Fir’auna da mutanensa kayan ado da kuma dukiyoyi a rayuwar duniya; ya Ubangijimu, don su vatar (da jama’a) daga hanyarka; ya Ubangijimu, Ka shafe dukiyoyinsu Ka kuma qeqasar da zukatansu ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raxaxi.”



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 89

قَالَ قَدۡ أُجِيبَت دَّعۡوَتُكُمَا فَٱسۡتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

(Allah) Ya ce: “Haqiqa an amsa addu’arku, sai ku tsaya qyam (a kan tafarkinku), kada kuwa ku bi hanyar waxanda ba sa sanin (gaskiya).”



Sourate: Suratu Hud

Verset : 96

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu da hijjoji bayyanannu



Sourate: Suratu Hud

Verset : 97

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ فِرۡعَوۡنَۖ وَمَآ أَمۡرُ فِرۡعَوۡنَ بِرَشِيدٖ

Zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai suka bi umarnin Fir’auna; amma kuma umarnin Fir’auna ba a kan hanya yake ba



Sourate: Suratu Hud

Verset : 110

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi, sai aka sassava a game da shi. Ba don kuwa wata kalma da ta rigaya daga Ubangijinka ba, to lalle da an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle suna cikin matuqar kokwanto game da shi (Alqur’ani)



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 5

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ أَنۡ أَخۡرِجۡ قَوۡمَكَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ وَذَكِّرۡهُم بِأَيَّىٰمِ ٱللَّهِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ

Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu cewa: “Ka fitar da mutananka daga duffai zuwa ga haske, kuma ka tunatar da su ni’imomin Allah (da ya yi musu).” Lalle game da wannan da akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haquri, mai yawan godiya



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 6

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ أَنجَىٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ وَيُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ

Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da Ya tserar da ku daga mutanen Fir’auna, suna gana muku azaba, suna kuma yanyanka ‘ya’yanku, kuma suna raya matayenku. A game da wannan da akwai bala’i mai girma daga Ubangijinku



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 7

وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكُمۡ لَئِن شَكَرۡتُمۡ لَأَزِيدَنَّكُمۡۖ وَلَئِن كَفَرۡتُمۡ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٞ

“Kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar da ku: “Lalle idan kuka gode wa (ni’imata) tabbas zan qara muku; idan kuwa kuka butulce, to lalle azabata tabbas mai tsanani ce.”



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 8

وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِن تَكۡفُرُوٓاْ أَنتُمۡ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ حَمِيدٌ

Musa kuma ya ce: “Idan kuka kafirce, ku da waxanda suke a bayan qasa baki xaya, to lalle Allah tabbas Mawadaci ne, Sha-yabo.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 2

وَءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَلَّا تَتَّخِذُواْ مِن دُونِي وَكِيلٗا

Kuma Mun bai wa Musa Littafi Muka kuma sanya shi ya zama shiriya ga Banu Isra’ila cewa: “Kada ku riqi wani wakili ba ni ba.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 101

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا

Kuma haqiqa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 102

قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا

(Musa) ya ce: “Haqiqa ka sani ba wanda ya saukar da waxannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da qasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”



Sourate: Suratul Isra’i

Verset : 103

فَأَرَادَ أَن يَسۡتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ فَأَغۡرَقۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعٗا

Sai ya yi nufin ya girgiza su a qasar (ta Masar don ya fitar da su daga ciki), to sai Muka nutsar da shi da duk wanda yake tare da shi gaba xaya



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 60

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَىٰهُ لَآ أَبۡرَحُ حَتَّىٰٓ أَبۡلُغَ مَجۡمَعَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ أَوۡ أَمۡضِيَ حُقُبٗا

Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da yaronsa: “Ba zan dakata da (tafiyata) ba har sai na kai mahaxar kogunan nan biyu, ko kuwa in zarce har tsawon shekaru[1].”


1- Daga nan har zuwa qarshen aya ta 82 Allah () ya ba da labarin tafiyar Annabi Musa () neman ilimi wajen Annabi Khadir (). Yaronsa shi ne Annabi Yusha’u ().


Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 61

فَلَمَّا بَلَغَا مَجۡمَعَ بَيۡنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ سَرَبٗا

To lokacin da suka isa mahaxar tasu (watau kogunan) sai suka manta da kifinsu wanda ya kama hanyarsa a cikin kogi kamar xakin qarqashin qasa



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 62

فَلَمَّا جَاوَزَا قَالَ لِفَتَىٰهُ ءَاتِنَا غَدَآءَنَا لَقَدۡ لَقِينَا مِن سَفَرِنَا هَٰذَا نَصَبٗا

To lokacin da suka wuce (wannan wuri) sai (Musa) ya ce da yaronsa: “Kawo mana abincinmu, haqiqa mun haxu da wahala cikin wannan tafiya tamu.”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 63

قَالَ أَرَءَيۡتَ إِذۡ أَوَيۡنَآ إِلَى ٱلصَّخۡرَةِ فَإِنِّي نَسِيتُ ٱلۡحُوتَ وَمَآ أَنسَىٰنِيهُ إِلَّا ٱلشَّيۡطَٰنُ أَنۡ أَذۡكُرَهُۥۚ وَٱتَّخَذَ سَبِيلَهُۥ فِي ٱلۡبَحۡرِ عَجَبٗا

Sai (yaron) ya ce: “Ba ka gani ba lokacin da muka fake a daidai dutsen nan ai sai na manta da kifin, ba kuwa wani ne ya mantar da ni shi ba sai Shaixan, ya hana ni in tuna. Sai kuma ya kama hanyarsa cikin kogi, abin mamaki!”



Sourate: Suratul Kahf 

Verset : 64

قَالَ ذَٰلِكَ مَا كُنَّا نَبۡغِۚ فَٱرۡتَدَّا عَلَىٰٓ ءَاثَارِهِمَا قَصَصٗا

(Musa) ya ce: “Wannan da ma shi ne abin da muke nema”, Sai suka koma da baya suna bin sawunsu (ta inda suka fito)