Sourate: Suratul An’am

Verset : 61

وَهُوَ ٱلۡقَاهِرُ فَوۡقَ عِبَادِهِۦۖ وَيُرۡسِلُ عَلَيۡكُمۡ حَفَظَةً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ تَوَفَّتۡهُ رُسُلُنَا وَهُمۡ لَا يُفَرِّطُونَ

“Kuma Shi ne wanda Yake da iko a kan bayinsa, kuma Yana aiko muku masu tsaro, har zuwa lokacin da mutuwa za ta zo wa xayanku, sai manzanninmu su karvi ransa, kuma su ba sa yin sakaci



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 35

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ إِمَّا يَأۡتِيَنَّكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي فَمَنِ ٱتَّقَىٰ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Ya ku ‘yan’adam, idan har manzanni suka zo muku daga cikinku, suna karanta muku ayoyina, to duk wanda ya yi taqawa, kuma ya kyautata aiki, to babu jin tsoro tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Sourate: Suratu Hud

Verset : 69

وَلَقَدۡ جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞۖ فَمَا لَبِثَ أَن جَآءَ بِعِجۡلٍ حَنِيذٖ

Haqiqa kuma mazanninmu sun zo wa Ibrahimu da albishir, suka ce: “Aminci (a gare ku)”, ya ce: “Aminci (a gare ku kuma).” To bai zauna ba sai da ya kawo musu soyayyen xan maraqi



Sourate: Suratu Hud

Verset : 77

وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗا وَقَالَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَصِيبٞ

Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luxu, sai aka vata masa rai saboda su, kuma zuciyarsa ta yi qunci saboda su[1], ya kuma ce: “Wannan rana ce mawuyaciya!”


1- Watau ya shiga damuwa domin ya san mutanensa ba za su qyale su ba.


Sourate: Suratun Nahl

Verset : 2

يُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرُوٓاْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ

Yana saukar da mala’iku da wahayi na umarninsa ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa da cewa,: “Ku yi gargaxi cewa,, lalle ba wani abin bauta sai Ni, to sai ku kiyaye dokokina.”



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 102

قُلۡ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلۡقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ

Ka ce: “Ruhul Qudusi (watau Mala’ika Jibrilu) ne ya saukar da shi daga Ubangijinka da gaskiya don ya tabbatar da waxanda suka yi imani (a kan dugadugansu), kuma shiriya ne da albishir ga Musulmai.”



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 75

ٱللَّهُ يَصۡطَفِي مِنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلٗا وَمِنَ ٱلنَّاسِۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Allah Yana zavar manzanni daga mala’iku kuma daga mutane. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani



Sourate: Suratus Shu’ara

Verset : 193

نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ

Ruhi amintacce (watau Jibrilu) ne ya sauko da shi



Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 31

وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُوٓاْ إِنَّا مُهۡلِكُوٓاْ أَهۡلِ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِۖ إِنَّ أَهۡلَهَا كَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Lokacin kuwa da manzanninmu suka zo wa Ibrahimu da albishir[1], sai suka ce: “Lalle mu masu hallaka mutanen wannan alqaryar ne, lalle mutanenta sun kasance azzalumai.”


1- Albishir na samun haihuwar xansa Ishaq () da kuma jikansa Ya’aqub ().


Sourate: Suratul Ankabut

Verset : 33

وَلَمَّآ أَن جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗاۖ وَقَالُواْ لَا تَخَفۡ وَلَا تَحۡزَنۡ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهۡلَكَ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luxu, sai ya yi baqin ciki da zuwansu, zuciyarsa kuma ta quntata saboda su[1], sai suka ce da shi: “Kada ka ji tsoro, kuma kada ka damu; lalle mu masu tserar da kai ne tare da iyalinka, sai matarka kawai da ta kasance cikin waxanda za su yi saura (a hallaka su tare)


1- Domin jiye musu tsoron mugun halin mutanensa musamman saboda mala’ikun sun zo a cikin kamanni na mutane maza.


Sourate: Suratu Faxir

Verset : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ جَاعِلِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلًا أُوْلِيٓ أَجۡنِحَةٖ مَّثۡنَىٰ وَثُلَٰثَ وَرُبَٰعَۚ يَزِيدُ فِي ٱلۡخَلۡقِ مَا يَشَآءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mahaliccin sammai da qasa Mai sanya mala’iku manzanni masu fukafukai bibbiyu da masu uku-uku da kuma masu huxu-huxu. Yakan kuma qara abin da Ya ga dama ga halittar[1]. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai


1- Don haka akwai mala’iku masu fukafukai fiye da huxu, ya kuma qara wa wanda ya ga dama kyau ko wata gava.


Sourate: Suratuz Zukhruf 

Verset : 80

أَمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيۡهِمۡ يَكۡتُبُونَ

Ko suna tsammanin cewa Mu ba Ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu suna tare da su suna rubutawa



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 24

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ

Shin labarin baqin Ibrahimu masu girma[1] ya zo maka?


1- Su ne mala’iku da Allah ya aiko.


Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 25

إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ

Lokacin da suka shiga wurinsa sai suka ce: “Muna maka sallama;” ya ce: “Aminci ya tabbata gare ku, (ku) mutane ne da ba sanannu ba.”



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 26

فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ

Sai ya saxaxa da sauri zuwa ga iyalinsa, sai ya zo da wani xan maraqi mai mai



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 27

فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ

Sai ya kusanta shi gare su, ya ce: “Yanzu ba za ku ci ba?”



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 28

فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ

(Da suka qi ci) sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata;” suka kuma yi masa albishir da samun yaro mai ilimi[1]


1- Watau Annabi Ishaq ().


Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 29

فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ

Sannan sai matarsa ta gabato su cikin wata qara, sai ta mari fuskarta ta ce: “Yanzu tsohuwa bakarara (ita ce za ta haihu?)”



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 30

قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ

Suka ce, “Kamar haka Ubangijinki Ya ce, lalle Shi Mai hikima ne, Masani.”



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 31

۞قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ

(Ibrahimu) ya ce: “To me yake tafe da ku, ya ku waxannan manzanni?”



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 32

قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ

Suka ce: “Lalle mu an aiko mu ne zuwa ga wasu mutane masu manyan laifuka[1]


1- Su ne mutanen Annabi Lux () masu neman maza da sha’awa.


Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 33

لِنُرۡسِلَ عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن طِينٖ

“Don mu zuba musu qonannun duwatsu na tavon (wuta)



Sourate: Suratuz Zariyat

Verset : 34

مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُسۡرِفِينَ

“Waxanda aka yi wa alama daga wurin Ubangijinka saboda mavarnata.”



Sourate: Qadar

Verset : 4

تَنَزَّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِم مِّن كُلِّ أَمۡرٖ

Mala’iku da Jibrilu suna ta saukowa da dukkanin al’amura a cikinsa da izinin Ubangijinsu