Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 96

إِنَّ أَوَّلَ بَيۡتٖ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكٗا وَهُدٗى لِّلۡعَٰلَمِينَ

Lalle farkon xaki da aka tanada don mutane (su yi ibada a cikinsa) shi ne wanda yake cikin Bakka[1], (xaki ne) mai albarka, kuma shiriya ne ga talikai


1- Watau Xakin Ka’aba da yake garin Makka mai alfarma.


Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 35

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِيمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا ٱلۡبَلَدَ ءَامِنٗا وَٱجۡنُبۡنِي وَبَنِيَّ أَن نَّعۡبُدَ ٱلۡأَصۡنَامَ

(Ka tuna) kuma lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan gari (Makka) ya zama amintacce, kuma Ka nesantar da ni da ‘ya’yana daga bauta wa gumaka



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 36

رَبِّ إِنَّهُنَّ أَضۡلَلۡنَ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِۖ فَمَن تَبِعَنِي فَإِنَّهُۥ مِنِّيۖ وَمَنۡ عَصَانِي فَإِنَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

“Ya Ubangijina, lalle su (gumakan) sun vatar da mutane masu yawa; wanda kuwa ya bi ni to lalle shi yana tare da ni; wanda kuma ya sava mini to lalle Kai Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 37

رَّبَّنَآ إِنِّيٓ أَسۡكَنتُ مِن ذُرِّيَّتِي بِوَادٍ غَيۡرِ ذِي زَرۡعٍ عِندَ بَيۡتِكَ ٱلۡمُحَرَّمِ رَبَّنَا لِيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ فَٱجۡعَلۡ أَفۡـِٔدَةٗ مِّنَ ٱلنَّاسِ تَهۡوِيٓ إِلَيۡهِمۡ وَٱرۡزُقۡهُم مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَشۡكُرُونَ

“Ya Ubangijinmu, lalle ni na zaunar da wasu daga zuriyata a wani kwari wanda ba a shuka a cikinsa[1] kusa da Xakinka mai alfarma; ya Ubangijinmu don su tsai da salla, to Ka sanya zukatan mutane su riqa karkatowa zuwa gare su, kuma Ka arzuta su da ‘ya’yan itace don su gode (maka)


1- Watau kuyangarsa Hajara () da xansa Isma’ilu (). Ya zaunar da su garin Makka da izinin Allah ().


Sourate: Suratul Balad

Verset : 1

لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Na rantse da wannan gari (na Makka)



Sourate: Suratul Balad

Verset : 2

وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ

Alhali kuwa kai an halatta maka wannan gari[1]


1- Watau an halatta masa kashe wanda ya cancanci kisa a garin Makka. Ko kuma ana nufin Allah ya yi rantsuwa da Makka musamman lokacin da Annabi () yake zaune a cikinta.


Sourate: Suratut Tin

Verset : 3

وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ

Da wannan garin amintacce (watau Makka)