وَعَلَّمَ ءَادَمَ ٱلۡأَسۡمَآءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمۡ عَلَى ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ فَقَالَ أَنۢبِـُٔونِي بِأَسۡمَآءِ هَـٰٓؤُلَآءِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Kuma sai (Allah) Ya koya wa Adamu dukkan sunaye (na abubuwa) sannan Ya kawo su gaban mala’iku, sai Ya ce: “Ku faxa min sunayen waxannan abubuwan in kun zamanto masu gaskiya.”
كَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِيكُمۡ رَسُولٗا مِّنكُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِنَا وَيُزَكِّيكُمۡ وَيُعَلِّمُكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُعَلِّمُكُم مَّا لَمۡ تَكُونُواْ تَعۡلَمُونَ
Kamar yadda Muka aiko muku da wani manzo daga cikinku, yana karanta muku ayoyinmu, kuma yana tsarkake ku, kuma yana koyar da ku Littafi da Hikima[1], kuma yana koyar da ku abin da a da can ba ku sani ba
1- Hikima, ita ce sunnar Annabi ().
وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ
“Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila
وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ وَرَحۡمَتُهُۥ لَهَمَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيۡءٖۚ وَأَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمۡ تَكُن تَعۡلَمُۚ وَكَانَ فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ عَظِيمٗا
Ba don falalar Allah da rahamarsa a kanka ba kuwa, lalle da waxansu jama’a daga cikinsu sun yi niyyar su vatar da kai, ba kuwa kowa za su iya vatarwa ba sai dai kawunansu; kuma ba za su cuce ka da komai ba. Kuma Allah Ya saukar maka da Littafi da hikima, kuma Ya sanar da kai abin da a da ba ka sani ba. Kuma falalar Allah mai girma ce gare ka
لَّـٰكِنِ ٱللَّهُ يَشۡهَدُ بِمَآ أَنزَلَ إِلَيۡكَۖ أَنزَلَهُۥ بِعِلۡمِهِۦۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَشۡهَدُونَۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًا
Amma Allah Yana shaida game da abin da Ya saukar maka; Ya saukar da shi ne da iliminsa; haka mala’iku ma suna shaidawa. Kuma Allah Ya isa Mai shaida
وَإِذَا سَمِعُواْ مَآ أُنزِلَ إِلَى ٱلرَّسُولِ تَرَىٰٓ أَعۡيُنَهُمۡ تَفِيضُ مِنَ ٱلدَّمۡعِ مِمَّا عَرَفُواْ مِنَ ٱلۡحَقِّۖ يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّـٰهِدِينَ
Kuma idan sun ji abin da aka saukar wa wannan Manzo, za ka ga idanunsu suna zubar da hawaye, saboda abin da suka gane na gaskiya; suna cewa: “Ya Ubangijinmu, mun yi imani, don haka Ka rubuta mu cikin masu shaidawa
هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلشَّمۡسَ ضِيَآءٗ وَٱلۡقَمَرَ نُورٗا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
Shi ne Wanda Ya sanya muku rana ta zamo mai haske da kuma wata ya zamo mai haskakawa, Ya kuma sanya shi mai masaukai don ku san adadin shekaru da kuma (sanin) lissafi (na lokuta). Allah bai halicci wannan ba sai da gaskiya. Yana bayyana ayoyi ne ga mutanen da suke da sani
وَلَمَّا دَخَلُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَهُمۡ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغۡنِي عَنۡهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍ إِلَّا حَاجَةٗ فِي نَفۡسِ يَعۡقُوبَ قَضَىٰهَاۚ وَإِنَّهُۥ لَذُو عِلۡمٖ لِّمَا عَلَّمۡنَٰهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
To lokacin da suka shiga ta inda babansu ya umarce su, (wannan) ba zai maganta musu komai ba daga Allah, sai dai wata buqata ce a zuciyar Yakubu da ya samu biyanta. Lalle kuma shi tabbas mai ilimi ne na abin da Muka sanar da shi, sai dai yawancin mutane ba su sani ba
فَبَدَأَ بِأَوۡعِيَتِهِمۡ قَبۡلَ وِعَآءِ أَخِيهِ ثُمَّ ٱسۡتَخۡرَجَهَا مِن وِعَآءِ أَخِيهِۚ كَذَٰلِكَ كِدۡنَا لِيُوسُفَۖ مَا كَانَ لِيَأۡخُذَ أَخَاهُ فِي دِينِ ٱلۡمَلِكِ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ نَرۡفَعُ دَرَجَٰتٖ مَّن نَّشَآءُۗ وَفَوۡقَ كُلِّ ذِي عِلۡمٍ عَلِيمٞ
Sai ya fara da (binciken) jakunkunansu kafin jakar xan’uwansa; sannan ya fito da shi (mudun) daga jakar xan’uwansa. Kamar haka Muka shirya wa Yusufu; ba zai yiwu ya riqe xan’uwansa ba a shari’ar Sarkin (Masar), sai dai idan Allah Ya ga dama. Muna xaukaka darajojin waxanda Muka ga dama ne. Kuma duk wani mai ilimi akwai wanda yake samansa a ilimi
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنۡ أَمۡرِ رَبِّي وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ إِلَّا قَلِيلٗا
Suna kuma tambayar ka game da ruhi. Ka ce da su: “Shi ruhi yana daga al’amarin Ubangijina, ba abin da aka ba ku na ilimi sai xan kaxan.”
فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا
To sai suka sami wani bawa daga bayinmu wanda Muka bai wa rahama daga gare Mu, kuma Muka koyar da shi wani ilimi daga wajenmu
وَلُوطًا ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗا وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَت تَّعۡمَلُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَٰسِقِينَ
Luxu kuma Muka ba shi hukunci da ilimi, Muka kuma tserar da shi daga alqaryar nan da (mutanenta) suka zamanto suna aikata munanan ayyuka. Lallai su sun kasance mutanen banza ne fasiqai
فَفَهَّمۡنَٰهَا سُلَيۡمَٰنَۚ وَكُلًّا ءَاتَيۡنَا حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَسَخَّرۡنَا مَعَ دَاوُۥدَ ٱلۡجِبَالَ يُسَبِّحۡنَ وَٱلطَّيۡرَۚ وَكُنَّا فَٰعِلِينَ
Sai Muka ganar da Sulaimanu shi (hukuncin)[1]. Kuma dukkaninsu Mun ba su annabta da ilimi. Muka kuma hore wa Dawuda duwatsu da tsuntsaye, suna tasbihi tare da shi. Mun kuwa kasance Masu aikata (haka)
1- Da farko Annabi Dawud () ya yi hukunci da cewa, manomin zai karvi dabbobin a madadin amfanin gonarsa da suka cinye. Amma sai Sulaiman () ya sake hukunci da cewa, manomin zai riqe dabbobin yana amfanuwa da su har zuwa lokacin da masu dabbobin za su sake noma musu gonarsa ta dawo kamar farko sai su karvi dabbobinsu.
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسۡتَوَىٰٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lokacin kuma da ya kai ganiyar qarfinsa ya kuma kammala, sai Muka ba shi hukunci da ilimi. Kamar haka kuwa Muke saka wa masu kyautatawa
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
Waxanda kuwa aka bai wa ilimi sai suka ce: “Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu haquri.”
بَلۡ هُوَ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ فِي صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّـٰلِمُونَ
A’a, shi dai (Alqur’ani) ayoyi ne bayyanannu (da suke) cikin zukatan waxanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ
Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma sassavawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi
وَيَرَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ ٱلۡحَقَّ وَيَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Waxanda aka bai wa ilimi kuma suna ganin abin da aka saukar maka daga Ubangijinka shi ne gaskiya, kuma yana shiryarwa ne zuwa hanyar (Allah) Mabuwayi, Sha-yabo
أَفَمَن زُيِّنَ لَهُۥ سُوٓءُ عَمَلِهِۦ فَرَءَاهُ حَسَنٗاۖ فَإِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۖ فَلَا تَذۡهَبۡ نَفۡسُكَ عَلَيۡهِمۡ حَسَرَٰتٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا يَصۡنَعُونَ
Yanzu wanda aka qawata wa mummunan aikinsa ya gan shi kyakkyawa (zai yi daidai da wanda Allah Ya shiryar)? To lalle Allah Yana vatar da wanda Ya ga dama Ya shiryi wanda Ya ga dama; saboda haka kada ka halakar da kanka don baqin ciki game da su. Lalle Allah Masanin abin da suke aikatawa ne
أَمَّنۡ هُوَ قَٰنِتٌ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ سَاجِدٗا وَقَآئِمٗا يَحۡذَرُ ٱلۡأٓخِرَةَ وَيَرۡجُواْ رَحۡمَةَ رَبِّهِۦۗ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلَّذِينَ يَعۡلَمُونَ وَٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَۗ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Shin yanzu wanda yake shi mai ibada ne a cikin sa’o’in dare, yana sujjada yana kuma tsayawa, yana tsoron ranar lahira yana kuma qaunar rahamar Ubangijinsa (zai yi daidai da wanda ba haka yake ba?) Ka ce: “Yanzu waxanda suke da sani za su yi daidai da waxanda ba su da sani? Ma’abota hankula ne kawai suke wa’azantuwa
وَيُدۡخِلُهُمُ ٱلۡجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمۡ
Ya kuma shigar da su Aljannar da Ya sanar da ita gare su
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَكُمۡ تَفَسَّحُواْ فِي ٱلۡمَجَٰلِسِ فَٱفۡسَحُواْ يَفۡسَحِ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَإِذَا قِيلَ ٱنشُزُواْ فَٱنشُزُواْ يَرۡفَعِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ دَرَجَٰتٖۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan aka ce da ku: “Ku yalwata a wuraren zama,” to sai ku yalwata, Allah zai yalwata muku[1]; idan kuma aka ce: “Ku tashi (daga wurinku)[2],” to sai ku tashi, Allah zai xaga darajojin waxanda suka yi imani daga cikinku da waxanda aka bai wa ilimi. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne
1-  Watau zai buxa musu a rayuwarsu ta duniya da ta lahira.
2-  Watau domin wani aiki na addini ko wata buqata da ta taso.            
ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ
Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne mafi karamci
ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ
Wanda Ya koyar ta (hanyar) alqalami
عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ
Ya koyar da mutum abin da bai sani ba