Sourate: Suratul Baqara

Verset : 200

فَإِذَا قَضَيۡتُم مَّنَٰسِكَكُمۡ فَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَذِكۡرِكُمۡ ءَابَآءَكُمۡ أَوۡ أَشَدَّ ذِكۡرٗاۗ فَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا وَمَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖ

To idan kun gama ayyukanku na Hajji, to ku yi ta ambaton Allah kamar yadda kuke ambaton iyayenku, ko ambaton (Allah) ya fi yawa. To daga cikin mutane akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijimu, Ka ba mu (rabo) a nan duniya”, kuma a lahira ba shi da wani rabo



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 201

وَمِنۡهُم مَّن يَقُولُ رَبَّنَآ ءَاتِنَا فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ حَسَنَةٗ وَقِنَا عَذَابَ ٱلنَّارِ

Kuma daga cikinsu akwai wanda yake cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu kyakkyawa a nan duniya, kuma Ka ba mu kyakkyawa a lahira, Ka kuma tsare mu daga azabar wuta.”



Sourate: Suratul Baqara

Verset : 202

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّمَّا كَسَبُواْۚ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Waxannan suna da babban rabo na daga abin da suka aikata, kuma Allah Mai gaggawar hisabi ne



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 14

زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ ٱلشَّهَوَٰتِ مِنَ ٱلنِّسَآءِ وَٱلۡبَنِينَ وَٱلۡقَنَٰطِيرِ ٱلۡمُقَنطَرَةِ مِنَ ٱلذَّهَبِ وَٱلۡفِضَّةِ وَٱلۡخَيۡلِ ٱلۡمُسَوَّمَةِ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ وَٱلۡحَرۡثِۗ ذَٰلِكَ مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلۡمَـَٔابِ

An qawata wa mutane son sha’awace-sha’awace na mata da ‘ya’ya da dukiya mai yawa abar tarawa ta zinariya da azurfa da kuma kiwatattun dawaki da dabbobi na gida da amfanin gona. Waxannan duk morewa ce ta rayuwar duniya; Allah kuwa a wurinsa ne kyakkyawar makoma take



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 77

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَشۡتَرُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَأَيۡمَٰنِهِمۡ ثَمَنٗا قَلِيلًا أُوْلَـٰٓئِكَ لَا خَلَٰقَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَلَا يُكَلِّمُهُمُ ٱللَّهُ وَلَا يَنظُرُ إِلَيۡهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَلَا يُزَكِّيهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle waxanda suke musanya alqawarin Allah da rantse-rantsensu da wani xan farashi qanqani, waxannan ba su da wani rabo a lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (duba na rahama) ba a ranar alqiyama, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai raxaxi



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 85

وَمَن يَبۡتَغِ غَيۡرَ ٱلۡإِسۡلَٰمِ دِينٗا فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡهُ وَهُوَ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karva daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 145

وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّـٰكِرِينَ

Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za Mu ba shi daga gare ta, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za Mu ba shi daga gare ta. Kuma da sannu za Mu saka ma masu godiya



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 176

وَلَا يَحۡزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡكُفۡرِۚ إِنَّهُمۡ لَن يَضُرُّواْ ٱللَّهَ شَيۡـٔٗاۚ يُرِيدُ ٱللَّهُ أَلَّا يَجۡعَلَ لَهُمۡ حَظّٗا فِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٌ

Kuma kada waxanda suke gaggawar shiga cikin (ayyukan) kafirci, su fusata ka. Haqiqa su ba za su cutar da Allah komai ba. Allah Ya yi nufin ba zai sanya musu wani rabo a lahira ba; kuma suna da azaba mai girma



Sourate: Suratu Ali-Imran

Verset : 198

لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا نُزُلٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۗ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّلۡأَبۡرَارِ

Amma waxanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan liyafa ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mafi alheri ga masu biyayya



Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 77

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ قِيلَ لَهُمۡ كُفُّوٓاْ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُمۡ يَخۡشَوۡنَ ٱلنَّاسَ كَخَشۡيَةِ ٱللَّهِ أَوۡ أَشَدَّ خَشۡيَةٗۚ وَقَالُواْ رَبَّنَا لِمَ كَتَبۡتَ عَلَيۡنَا ٱلۡقِتَالَ لَوۡلَآ أَخَّرۡتَنَآ إِلَىٰٓ أَجَلٖ قَرِيبٖۗ قُلۡ مَتَٰعُ ٱلدُّنۡيَا قَلِيلٞ وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّمَنِ ٱتَّقَىٰ وَلَا تُظۡلَمُونَ فَتِيلًا

Shin ba ka ganin waxanda aka ce da su: “Ku kame hannayenku kuma ku tsayar da salla kuma ku bayar da zakka?”[1] To yayin da aka wajabta musu yaqi, sai ga wani vangare daga cikinsu suna jin tsoron mutane kamar yadda suke jin tsoron Allah, ko ma fiye da hakan. Kuma sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, don me Ka wajabta mana yin yaqi, me ya hana Ka jinkirta mana zuwa wani lokaci makusanci?” Ka ce: “Jin daxin duniya kaxan ne, lahira kuwa ita ce mafi alheri ga wanda ya yi taqawa, kuma ba za a zalunce ku ba, ko da gwargwadon zaren qwallon dabino ne.”


1- Watau wasu daga cikin sahabbai waxanda suke ta roqon a farlanta musu jihadi, amma ana nuna musu su bar wannan maganar, su dai tsayar da salla su ba da zakka.


Sourate: Suratun Nisa’i

Verset : 134

مَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ ثَوَابُ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

Duk wanda ya kasance yana son ladan duniya, to ladan duniya da na lahira duk a hannun Allah suke. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani



Sourate: Suratul An’am

Verset : 32

وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۖ وَلَلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face wasa da sharholiya; kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 147

وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡۚ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxanda kuma suka qaryata ayoyinmu da haxuwa a ranar alqiyama, ayyukansu sun rushe. Shin kuwa za a yi musu wani sakamako ne in ba abin da suka kasance suna aikatawa ba?



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 169

فَخَلَفَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ خَلۡفٞ وَرِثُواْ ٱلۡكِتَٰبَ يَأۡخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا ٱلۡأَدۡنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغۡفَرُ لَنَا وَإِن يَأۡتِهِمۡ عَرَضٞ مِّثۡلُهُۥ يَأۡخُذُوهُۚ أَلَمۡ يُؤۡخَذۡ عَلَيۡهِم مِّيثَٰقُ ٱلۡكِتَٰبِ أَن لَّا يَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّ وَدَرَسُواْ مَا فِيهِۗ وَٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Sai waxansu bara-gurbi suka maye bayansu, sun gaji littafin (Attaura), suna karvar abin duniya, suna kuma cewa: “Za a gafarta mana.” Kuma idan wani abin duniyar irinsa ya zo musu sai su sake karvar sa. Shin yanzu ba a xauki alqawari daga wurinsu ba a cikin littafin (Attaura) cewa, kada su faxi wata magana game da Allah sai gaskiya, kuma sun karanta abin da yake cikinsa? Kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga dukkan waxanda suke da taqawa. Shin ba za ku hankalta ba?



Sourate: Suratut Tauba

Verset : 38

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَا لَكُمۡ إِذَا قِيلَ لَكُمُ ٱنفِرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱثَّاقَلۡتُمۡ إِلَى ٱلۡأَرۡضِۚ أَرَضِيتُم بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مِنَ ٱلۡأٓخِرَةِۚ فَمَا مَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا قَلِيلٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, me ya same ku ne idan aka ce da ku ku fita yaqi saboda Allah sai ku yi nauyin jiki? Yanzu kun zavi rayuwar duniya a kan ta lahira? Ai jin daxin rayuwar duniya abu ne qanqani dangane da na lahira



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 62

أَلَآ إِنَّ أَوۡلِيَآءَ ٱللَّهِ لَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

A saurara, lalle waliyyan Allah babu wani tsoro a gare su, kuma ba za su yi wani baqin ciki ba



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 63

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

(Su ne) waxanda suka yi imani kuma suka kasance masu kiyaye dokokin Allah



Sourate: Suratu Yunus

Verset : 64

لَهُمُ ٱلۡبُشۡرَىٰ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ لَا تَبۡدِيلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Suna da albishir a rayuwar duniya da kuma ta lahira. Babu wani sauyi ga kalmomin Allah. Wannan shi ne babban rabo



Sourate: Suratu Hud

Verset : 15

مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيۡهِمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فِيهَا وَهُمۡ فِيهَا لَا يُبۡخَسُونَ

Waxanda suke nufin rayuwar duniya da qawace-qawacenta, to za Mu ba su cikakken sakamakon ayyukansu a cikinta, kuma ba za a tauye musu (komai ba)



Sourate: Suratu Hud

Verset : 16

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَيۡسَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا ٱلنَّارُۖ وَحَبِطَ مَا صَنَعُواْ فِيهَا وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxannan su ne waxanda ba su da komai a lahira sai wuta; kuma abin da suka aikata a cikinta (duniyar) ya rushe, kuma abin da suke aikatawa ya lalace



Sourate: Suratu Yusuf 

Verset : 57

وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

Kuma lalle ladan lahira shi ya fi ga waxanda suka yi imani kuma suka zamanto suna kiyaye dokokin (Allah)



Sourate: Suratu Yusuf 

Verset : 109

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡقُرَىٰٓۗ أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۗ وَلَدَارُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ba Mu kuma aiko (manzanni) a gabaninka ba sai maza ‘yan birni waxanda Muke yi wa wahayi. Me ya sa (kafirai) ba za su yi tafiya ba a bayan qasa don su ga yadda qarshen waxanda suka rigaye su ya kasance? Lalle kuwa gidan lahira shi ya fi ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?



Sourate: Suratur Ra’ad

Verset : 26

ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ

Allah ne Yake shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yake kuma quntatawa (ga wanda Ya ga dama. (Kafirai) kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, rayuwar duniya kuwa ba komai ba ce illa xan jin daxi kaxan dangane da na lahira



Sourate: Suratur Ra’ad

Verset : 34

لَّهُمۡ عَذَابٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَقُّۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Suna da wata azaba a rayuwar duniya; kuma lalle azabar lahira ita ta fi tsanani; ba su kuwa da wani mai kare su daga (azabar) Allah



Sourate: Suratu Ibrahim

Verset : 27

يُثَبِّتُ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡقَوۡلِ ٱلثَّابِتِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَيُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلظَّـٰلِمِينَۚ وَيَفۡعَلُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ

Allah Yana tabbatar da waxanda suka yi imani a kan magana tabbatacciya a rayuwar duniya da kuma a lahira; Yana kuma vatar da azzalumai. Allah kuma Yana aikata abin da Ya ga dama



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 22

إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٞ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ

Abin bautarku Abin bauta ne Xaya, sai dai waxanda ba sa yin imani da ranar lahira zukatansu masu musun hakan ne, kuma su masu girman kai ne



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 41

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْ لَنُبَوِّئَنَّهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Waxanda kuma suka yi hijira saboda Allah bayan an zalunce su lalle za Mu shirya musu kyakkyawar (rayuwa) a duniya; ladan lahira kuma ya fi girma da a ce sun kasance suna sane da (haka)



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 96

مَا عِندَكُمۡ يَنفَدُ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٖۗ وَلَنَجۡزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓاْ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Abin da yake wurinku yana qarewa; abin da kuwa yake wurin Allah wanzajje ne. Lalle kuwa tabbas za Mu saka wa waxanda suka yi haquri ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 97

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Sourate: Suratun Nahl

Verset : 107

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Wannan kuwa (ya faru) saboda su sun fi son rayuwar duniya a kan ta lahira, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai