Sourate: Suratul Baqara

Verset : 210

هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن يَأۡتِيَهُمُ ٱللَّهُ فِي ظُلَلٖ مِّنَ ٱلۡغَمَامِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَقُضِيَ ٱلۡأَمۡرُۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

Shin ko akwai abin da suke jira ne, in ban da Allah Ya zo musu a cikin waxansu inuwoyi na gizagizai da mala’iku, sai a zartar da al’amari? Kuma zuwa ga Allah ne ake mayar da al’amura



Sourate: Suratul Furqan

Verset : 25

وَيَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلسَّمَآءُ بِٱلۡغَمَٰمِ وَنُزِّلَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ تَنزِيلًا

Kuma (ka tuna) ranar da sama za ta kekkece da girgije, kuma a saukar da mala’iku gungu-gungu



Sourate: Suratuz Zumar

Verset : 67

وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِيعٗا قَبۡضَتُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُ مَطۡوِيَّـٰتُۢ بِيَمِينِهِۦۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Ba su kuma girmama Allah ba kamar yadda Ya cancanta a girmama Shi, alhali qasa ga baki xayanta tana cikin Damqarsa ranar alqiyama, sammai kuma suna nannaxe a Hannunsa na dama. Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma xaukaka game da abin da suke yin shirka (da shi)



Sourate: Suratur Rahman

Verset : 37

فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةٗ كَٱلدِّهَانِ

Sannan idan sama ta kekkece ta zama jajir kamar jar fata[1]


1- Watau saboda an gusar da hasken taurarin cikinta gaba xaya.


Sourate: Suratur Rahman

Verset : 38

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ

Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?