Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 112

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا قَرۡيَةٗ كَانَتۡ ءَامِنَةٗ مُّطۡمَئِنَّةٗ يَأۡتِيهَا رِزۡقُهَا رَغَدٗا مِّن كُلِّ مَكَانٖ فَكَفَرَتۡ بِأَنۡعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلۡجُوعِ وَٱلۡخَوۡفِ بِمَا كَانُواْ يَصۡنَعُونَ

Allah kuma Ya ba da misali da wata alqarya[1] wadda ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali, arzikinta yana zo mata a yalwace ta kowanne wuri, sai ta kafirce wa ni’imomin Allah, to sai Allah Ya xanxana mata masifar yunwa da tsoro saboda abin da suka kasance suna aikatawa


1- Watau garin Makka.


Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 113

وَلَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مِّنۡهُمۡ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَهُمۡ ظَٰلِمُونَ

Haqiqa kuma Manzo ya zo musu daga cikinsu, sai suka qaryata shi, to sai azaba ta afka musu alhali suna azzalumai



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 114

فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

To ku ci halal mai daxi daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma ku gode ni’imomin Allah in kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 115

إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Abin da kawai Ya haramta muku (shi ne) mushe da jini (mai kwarara) da naman alade da kuma abin da aka yanka da (sunan) wanin Allah; amma wanda ya matsu (ya ci) ba yana mai zalunci ko qetare iyaka ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 116

وَلَا تَقُولُواْ لِمَا تَصِفُ أَلۡسِنَتُكُمُ ٱلۡكَذِبَ هَٰذَا حَلَٰلٞ وَهَٰذَا حَرَامٞ لِّتَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ

Kuma saboda abin da harsunanku suke bayyanawa na qarya kada ku riqa cewa, wannan halal ne, wannan kuma haram ne, don ku yi wa Allah qarya. Lalle waxanda suke qirqira wa Allah qarya ba sa rabauta



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 117

مَتَٰعٞ قَلِيلٞ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

(Wannan) jin daxi ne qanqani (a duniya), kuma suna da azaba mai raxaxi



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 118

وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُواْ حَرَّمۡنَا مَا قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ مِن قَبۡلُۖ وَمَا ظَلَمۡنَٰهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Kuma Mun haramta wa Yahudawa abin da Muka labarta maka tun tuni[1]; ba Mu kuwa zalunce su ba, sai dai kuma kansu suka zalunta


1- Shi ne abin da ya zo a ciki Suratul An’am, aya ta 146.


Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 119

ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٌ

Sannan lalle Ubangijinka (Mai gafara ne) ga waxanda suka aikata mummuna a cikin jahilci sannan suka tuba bayan haka suka kuma gyara, lalle Ubagijinka Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 120

إِنَّ إِبۡرَٰهِيمَ كَانَ أُمَّةٗ قَانِتٗا لِّلَّهِ حَنِيفٗا وَلَمۡ يَكُ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Lalle Ibrahimu ya zama abin koyi ne mai biyayya ga Allah mai kauce wa varna, bai kuma zamanto daga masu shirka ba



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 121

شَاكِرٗا لِّأَنۡعُمِهِۚ ٱجۡتَبَىٰهُ وَهَدَىٰهُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Mai godiya ne ga ni’imarsa (wato Allah), Ya zave shi, Ya kuma shirye shi zuwa ga tafarki madaidaici



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 122

وَءَاتَيۡنَٰهُ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Mun kuma ba shi kyakkyawa a duniya; lalle kuma shi a lahira tabbas yana daga cikin salihai



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 123

ثُمَّ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ أَنِ ٱتَّبِعۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِيمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Sannan Muka yi maka wahayi cewa, ka bi addinin Ibrahimu mai kauce wa varna; bai kuwa zamanto daga masu shirka ba



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 124

إِنَّمَا جُعِلَ ٱلسَّبۡتُ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

An farlanta (girmama ranar) Asabar kawai a kan waxanda suka yi savani game da ita. kuma lalle Ubangijinka tabbas zai yi hukunci tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna savani a game da shi



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 125

ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 126

وَإِنۡ عَاقَبۡتُمۡ فَعَاقِبُواْ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبۡتُم بِهِۦۖ وَلَئِن صَبَرۡتُمۡ لَهُوَ خَيۡرٞ لِّلصَّـٰبِرِينَ

Idan za ku yi uquba to ku yi uquba da kwatankwacin abin da aka yi muku uquba da shi. Kuma lalle idan kuka yi haquri to tabbas shi ne ya fi alheri ga masu haquri



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 127

وَٱصۡبِرۡ وَمَا صَبۡرُكَ إِلَّا بِٱللَّهِۚ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَلَا تَكُ فِي ضَيۡقٖ مِّمَّا يَمۡكُرُونَ

Kuma ka yi haquri, ba kuwa za ka iya haqurin ba sai da taimakon Allah. Kada ranka ya vaci a kansu, kada kuma ka zama cikin qunci game da makircin da suke qullawa



Capítulo: Suratun Nahl

Verso : 128

إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحۡسِنُونَ

Lalle Allah Yana tare da waxanda suka yi taqawa da kuma waxanda suke masu kyautatawa ne