Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 144

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۚ أَتُرِيدُونَ أَن تَجۡعَلُواْ لِلَّهِ عَلَيۡكُمۡ سُلۡطَٰنٗا مُّبِينًا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku riqi kafirai a matsayin masoya ku bar muminai. Shin kuna so ku ba wa Allah wata hujja mabayyaniya ne a kanku?



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 145

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا

Lalle munafuqai suna cikin matakin qarshe na can qarqashin wuta, kuma ba za ka tava sama musu wani mataimaki ba



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 146

إِلَّا ٱلَّذِينَ تَابُواْ وَأَصۡلَحُواْ وَٱعۡتَصَمُواْ بِٱللَّهِ وَأَخۡلَصُواْ دِينَهُمۡ لِلَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَسَوۡفَ يُؤۡتِ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَجۡرًا عَظِيمٗا

Sai fa waxanda suka tuba, kuma suka gyara aikinsu, kuma suka yi riqo ga igiyar Allah; kuma suka tsantsanta addininsu don Allah; to waxannan suna tare da muminai; kuma Allah zai bai wa muminai lada mai girma



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 147

مَّا يَفۡعَلُ ٱللَّهُ بِعَذَابِكُمۡ إِن شَكَرۡتُمۡ وَءَامَنتُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ شَاكِرًا عَلِيمٗا

Me Allah zai yi da azabtar da ku idan har kun yi godiya kuma kun yi imani? Allah kuwa Ya kasance Mai godiya ne, Mai yawan sani