وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَيۡنَ شُرَكَآؤُكُمُ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ
Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tattara su gaba xaya, sannan Mu ce da waxanda suka yi shirka: “Ina abokan tarayyarku waxanda kuka kasance kuna riyawa?”
ثُمَّ لَمۡ تَكُن فِتۡنَتُهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ وَٱللَّهِ رَبِّنَا مَا كُنَّا مُشۡرِكِينَ
Sannan fitinarsu ba ta zamo komai ba, face cewar da suka yi: “Wallahi, ya Ubangijinmu, ba mu kasance masu yin shirka ba!”
ٱنظُرۡ كَيۡفَ كَذَبُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡۚ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Duba ka ga yadda suka yi wa kansu qarya. Kuma abin da suka kasance suna qirqira ya vace musu
وَمِنۡهُم مَّن يَسۡتَمِعُ إِلَيۡكَۖ وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءُوكَ يُجَٰدِلُونَكَ يَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake sauraren ka; kuma Mun sanya murafai a zukatansu, ta yadda ba za su iya fahimtar sa ba, haka kuma a kunnuwansu akwai wata toshiya. Kuma in da za su ga kowace irin aya ce, ba za su yi imani da ita ba. Har ma idan sun zo maka suna jayayya da kai, (sai) waxanda suka kafirta su riqa cewa: “Ai wannan ba komai ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko.”
وَهُمۡ يَنۡهَوۡنَ عَنۡهُ وَيَنۡـَٔوۡنَ عَنۡهُۖ وَإِن يُهۡلِكُونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡ وَمَا يَشۡعُرُونَ
Kuma suna hana (mutane) sauraren sa (Alqur’ani), kuma su kansu suna qara nesanta da shi; kuma ba kowa suke hallakarwa ba face kawunansu, sai dai su ba sa jin hakan
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَى ٱلنَّارِ فَقَالُواْ يَٰلَيۡتَنَا نُرَدُّ وَلَا نُكَذِّبَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّنَا وَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Da kuma za ka ga lokacin da ake tsayar da su a gaban wuta, sai su ce: “Kaiconmu, ina ma da za a mayar da mu (duniya), to da ba za mu sake qaryata ayoyin Ubangijinmu ba, kuma za mu zamanto cikin muminai.”
بَلۡ بَدَا لَهُم مَّا كَانُواْ يُخۡفُونَ مِن قَبۡلُۖ وَلَوۡ رُدُّواْ لَعَادُواْ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
A’a, ba haka ba ne, abin da suke voyewa a da shi ne ya bayyana a gare su[1]; kuma in da za a mayar da su, to da sun koma kan abin da aka hana su. Kuma lalle su tabbas maqaryata ne
1- A duniya suna voye gaskiyar manzancin Annabi () duk da cewa sun san gaskiyarsa.
وَقَالُوٓاْ إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ
Kuma suka ce: “Ba wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya, kuma mu ba waxanda za a sake tashin mu ba ne.”
وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ وُقِفُواْ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ قَالَ أَلَيۡسَ هَٰذَا بِٱلۡحَقِّۚ قَالُواْ بَلَىٰ وَرَبِّنَاۚ قَالَ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ
Kuma in da za ka ga lokacin da aka tsayar da su a gaban Ubangjinsu; ya ce: “Shin ashe wannan ba gaskiya ne ba?” Sai su ce: “Gaskiya ne, muna rantsuwa da Ubangijinmu.” Sai Ya ce: “To ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci.”
قَدۡ خَسِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱللَّهِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةٗ قَالُواْ يَٰحَسۡرَتَنَا عَلَىٰ مَا فَرَّطۡنَا فِيهَا وَهُمۡ يَحۡمِلُونَ أَوۡزَارَهُمۡ عَلَىٰ ظُهُورِهِمۡۚ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ
Haqiqa waxanda suka qaryata haxuwa da Allah sun yi hasara; har sai lokacin da alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, sai su ce: “Kaiconmu kan irin sakacin da muka yi a cikinta (duniya),” alhalin kuwa suna xauke da kayan laifukansu a bayansu. Ku saurara, abin da suka xauka na laifi ya munana matuqa
وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا لَعِبٞ وَلَهۡوٞۖ وَلَلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face wasa da sharholiya; kuma lalle gidan lahira shi ne mafi alheri ga waxanda suke kiyaye dokokin (Allah). Shin ba za ku hankalta ba?
قَدۡ نَعۡلَمُ إِنَّهُۥ لَيَحۡزُنُكَ ٱلَّذِي يَقُولُونَۖ فَإِنَّهُمۡ لَا يُكَذِّبُونَكَ وَلَٰكِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ
Haqiqa Muna da cikakkiyar masaniyar cewa, lalle irin abin da suke faxa yakan baqanta maka rai; to a gaskiya su ba kai suke qaryatawa ba, sai dai azzalumai suna jayayya ne da ayoyin Allah
وَلَقَدۡ كُذِّبَتۡ رُسُلٞ مِّن قَبۡلِكَ فَصَبَرُواْ عَلَىٰ مَا كُذِّبُواْ وَأُوذُواْ حَتَّىٰٓ أَتَىٰهُمۡ نَصۡرُنَاۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِ ٱللَّهِۚ وَلَقَدۡ جَآءَكَ مِن نَّبَإِيْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle haqiqa an qaryata waxansu manzanni a gabaninka, sai suka yi haquri a kan qaryata su da aka yi, kuma an cutar da su, har sai da taimakonmu ya zo musu. Kuma babu wanda ya isa ya musanya kalmomin Allah. Kuma lalle haqiqa wani sashi na labarin manzanni ya zo maka
وَإِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكَ إِعۡرَاضُهُمۡ فَإِنِ ٱسۡتَطَعۡتَ أَن تَبۡتَغِيَ نَفَقٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ سُلَّمٗا فِي ٱلسَّمَآءِ فَتَأۡتِيَهُم بِـَٔايَةٖۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَمَعَهُمۡ عَلَى ٱلۡهُدَىٰۚ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ
Kuma idan bijirewarsu ta dame ka, to idan har kana iya haqa rami a cikin qasa, ko kuma (ka samu) wani tsani ka hau sama, don ka zo musu da wata aya, (to ka yi hakan). Kuma in da Allah Ya ga dama, tabbas da Ya tara su gaba xaya a kan shiriya. Don haka kada ka kasance cikin jahilai
۞إِنَّمَا يَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ يَسۡمَعُونَۘ وَٱلۡمَوۡتَىٰ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ ثُمَّ إِلَيۡهِ يُرۡجَعُونَ
Lalle masu ji su ne kawai suke amsa (kiranka). Matattu kuwa Allah zai tashe su (ranar alqiyama), sannan zuwa gare Shi za a mayar da su
وَقَالُواْ لَوۡلَا نُزِّلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يُنَزِّلَ ءَايَةٗ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ
Kuma suka ce: “Ina ma da an saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ?” Ka ce: “Lalle Allah Mai iko ne a kan Ya saukar da kowace irin aya, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka).”
وَمَا مِن دَآبَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا طَـٰٓئِرٖ يَطِيرُ بِجَنَاحَيۡهِ إِلَّآ أُمَمٌ أَمۡثَالُكُمۚ مَّا فَرَّطۡنَا فِي ٱلۡكِتَٰبِ مِن شَيۡءٖۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يُحۡشَرُونَ
Kuma babu wata dabba da take tafiya a bayan qasa, kuma babu wani tsuntsu da yake tashi da fukafukansa, face (su ma) al’ummomi ne irinku. Ba Mu yi sakacin barin wani abu ba a cikin littafi, sannan kuma zuwa ga Ubangijinsu ne za a tara su
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا صُمّٞ وَبُكۡمٞ فِي ٱلظُّلُمَٰتِۗ مَن يَشَإِ ٱللَّهُ يُضۡلِلۡهُ وَمَن يَشَأۡ يَجۡعَلۡهُ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Waxanda suka qaryata ayoyinmu su kurame ne, kuma bebaye ne, suna cikin duffai. Wanda Allah Ya ga dama sai Ya vatar da shi, wanda kuwa Ya ga dama sai Ya xora shi a kan tafarki madaidaici
قُلۡ أَرَءَيۡتَكُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُ ٱللَّهِ أَوۡ أَتَتۡكُمُ ٱلسَّاعَةُ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَدۡعُونَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ka ce; “Ku ba ni labari, idan da a ce azabar Allah za ta zo muku ko alqiyama ta zo muku, shin wanin Allah za ku kira, in har kun kasance masu gaskiya?”
بَلۡ إِيَّاهُ تَدۡعُونَ فَيَكۡشِفُ مَا تَدۡعُونَ إِلَيۡهِ إِن شَآءَ وَتَنسَوۡنَ مَا تُشۡرِكُونَ
Ba haka ba ne, (Allah) Shi kaxai za ku kira, sai Ya yaye abin da kuke roqonsa a kai idan Ya ga dama, kuma za ku manta abin da kuke haxa Allah da shi wajen bauta
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمۡ يَتَضَرَّعُونَ
Kuma lalle Mun aika da (manzanni) zuwa ga al’ummomin da suka gabace ka, sai Muka xora musu tsananin talauci da cutuka ko sa qasqantar da kai
فَلَوۡلَآ إِذۡ جَآءَهُم بَأۡسُنَا تَضَرَّعُواْ وَلَٰكِن قَسَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
To me ya hana lokacin da musibarmu ta zo musu, su qasqantar da kai? Sai dai kuma zukatansu ne suka qeqashe, Shaixan kuma ya qawata musu abin da suka kasance suna aikatawa
فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِۦ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِمۡ أَبۡوَٰبَ كُلِّ شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ إِذَا فَرِحُواْ بِمَآ أُوتُوٓاْ أَخَذۡنَٰهُم بَغۡتَةٗ فَإِذَا هُم مُّبۡلِسُونَ
To yayin da suka yi watsi da abin da aka yi musu wa’azi da shi, sai Muka buxe musu qofofin kowane irin abu, har zuwa lokacin da suka yi fariya da abin da aka ba su, sai Muka damqe su ba zato ba tsammani, sai ga su suna masu yanke qauna (daga kowane alheri)
فَقُطِعَ دَابِرُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْۚ وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Da haka ne aka tumvuke tushen waxanda suka yi zalunci. Kuma yabo da kirari sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai
قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَخَذَ ٱللَّهُ سَمۡعَكُمۡ وَأَبۡصَٰرَكُمۡ وَخَتَمَ عَلَىٰ قُلُوبِكُم مَّنۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَأۡتِيكُم بِهِۗ ٱنظُرۡ كَيۡفَ نُصَرِّفُ ٱلۡأٓيَٰتِ ثُمَّ هُمۡ يَصۡدِفُونَ
Ka ce: “Ku ba ni labari, yanzu idan Allah zai xauke jinku da ganinku, kuma Ya xora murfi a zukatanku, wane abin bauta ne wanda ba Allah ba, da zai dawo muku da shi?” Duba ka ga yadda Muke sarrafa ayoyi, amma duk da haka suna bijirewa
قُلۡ أَرَءَيۡتَكُمۡ إِنۡ أَتَىٰكُمۡ عَذَابُ ٱللَّهِ بَغۡتَةً أَوۡ جَهۡرَةً هَلۡ يُهۡلَكُ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Ka ce: “Ku ba ni labari, idan da azabar Allah za ta zo muku ba zato ba tsammani ko kuma cikin sani, to shin za a hallakar da (wasu) ba azzaluman mutane ba?”
وَمَا نُرۡسِلُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَۖ فَمَنۡ ءَامَنَ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ
Kuma ba ma aiko da manzanni sai suna masu bushara masu gargaxi; sannan duk wanda ya yi imani kuma ya kyautata aiki, to babu tsoro a tattare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba
وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَمَسُّهُمُ ٱلۡعَذَابُ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ
Waxanda kuwa suka qaryata ayoyinmu, azaba za ta shafe su saboda abin da suka kasance suna yi na fasiqanci
قُل لَّآ أَقُولُ لَكُمۡ عِندِي خَزَآئِنُ ٱللَّهِ وَلَآ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ وَلَآ أَقُولُ لَكُمۡ إِنِّي مَلَكٌۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُۚ أَفَلَا تَتَفَكَّرُونَ
Ka ce: “Ni ba zan ce da ku a wajena taskokin Allah suke ba, kuma ni ban san gaibu ba, kuma ni ba zan ce da ku ni mala’ika ne ba; ni ba abin da nake bi sai abin da aka yi mini wahayinsa.” Ka ce: “Yanzu makaho da mai gani za su yi daidai? To me ya sa ba za ku yi tunani ba?”
وَأَنذِرۡ بِهِ ٱلَّذِينَ يَخَافُونَ أَن يُحۡشَرُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ لَيۡسَ لَهُم مِّن دُونِهِۦ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ لَّعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ
Kuma ka yi gargaxi da shi (Alqur’ani) ga waxanda suke jin tsoron a tattara su a gaban Ubangijinsu, ba su da wani majivincin lamari in ba Shi ba, kuma ba su da wani mai ceto, don su kiyaye dokokin Allah