Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 46

۞وَلَا تُجَٰدِلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡۖ وَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَأُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَإِلَٰهُنَا وَإِلَٰهُكُمۡ وَٰحِدٞ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ

Kuma kada ku yi jayayya da ma’abota littafi (Yahudu da Nasara) sai ta hanyar da ta fi kyau, sai dai waxanda suka yi zalunci daga cikinsu; kuma ku ce: “Mun yi imani da abin da aka saukar mana da kuma abin da aka saukar muku, kuma Abin bautarmu da Abin bautarku Xaya ne, kuma mu masu miqa wuya ne gare Shi.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 47

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَۚ فَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۖ وَمِنۡ هَـٰٓؤُلَآءِ مَن يُؤۡمِنُ بِهِۦۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلۡكَٰفِرُونَ

Kamar haka kuma Muka saukar maka da Alqur’ani. To waxanda Muka bai wa littafi (a gabaninka) suna imani da shi; daga waxannan kuma (wato mutanen Makka) akwai wanda yake imani da shi. Ba kuwa mai musun ayoyinmu sai kafirai



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 48

وَمَا كُنتَ تَتۡلُواْ مِن قَبۡلِهِۦ مِن كِتَٰبٖ وَلَا تَخُطُّهُۥ بِيَمِينِكَۖ إِذٗا لَّٱرۡتَابَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ

Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafinsa ba (wato Alkur’ani), kuma ba ka rubuta shi da hannun damanka; da kuwa haka ya faru, to da sai masu qaryatawa su shiga kokwanto



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 49

بَلۡ هُوَ ءَايَٰتُۢ بَيِّنَٰتٞ فِي صُدُورِ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا ٱلظَّـٰلِمُونَ

A’a, shi dai (Alqur’ani) ayoyi ne bayyanannu (da suke) cikin zukatan waxanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 50

وَقَالُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَٰتٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡأٓيَٰتُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Suka kuma ce: “Me ya hana a saukar masa da wasu ayoyi daga Ubangijinsa?” Ka ce (da su): “Ayoyi suna wurin Allah ne kawai, ni kuma ba kowa ba ne face mai gargaxi, mai bayyana (gargaxin).”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 51

أَوَلَمۡ يَكۡفِهِمۡ أَنَّآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ يُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَرَحۡمَةٗ وَذِكۡرَىٰ لِقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu bai ishe su ba cewa, Mun saukar maka da Littafi da ake karanta musu shi? Lalle a game da wannan tabbas akwai rahama da kuma tunatarwa ga mutanen da suke yin imani



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 52

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ شَهِيدٗاۖ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ وَكَفَرُواْ بِٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku; Yana sane da abin da yake cikin sammai da qasa. Waxanda kuwa suka yi imani da qarya suka kuma kafirce wa Allah, waxannan su ne asararru.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 53

وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَوۡلَآ أَجَلٞ مُّسَمّٗى لَّجَآءَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ وَلَيَأۡتِيَنَّهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Suna kuma neman ka da ka gaggauto musu da azaba. Ba don kuwa akwai lokaci na musamman (da aka tanada) ba, tabbas da azabar ta zo musu, kuma tabbas da za ta zo musu ne ba zato ba tsammani, alhali ba su sani ba



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 54

يَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةُۢ بِٱلۡكَٰفِرِينَ

Suna (kuma) neman ka da ka gaggauto musu da azaba, alhali kuwa Jahannama tabbas mai kewaye kafirai ce



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 55

يَوۡمَ يَغۡشَىٰهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۡ وَيَقُولُ ذُوقُواْ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

A ranar da azaba za ta lulluve su ta samansu da ta qarqashin qafafuwansu, kuma (Allah) Ya ce (da su): “Ku xanxani abin da kuka kasance kuna aikatawa.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 56

يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ أَرۡضِي وَٰسِعَةٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱعۡبُدُونِ

Ya ku bayina waxanda suka yi imani, lalle qasata yalwatacciya ce, to Ni kaxai sai ku bauta Mini



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 57

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۖ ثُمَّ إِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

Kowanne rai zai xanxani mutuwa; sannan wurinmu za a mayar da ku



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 58

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ غُرَفٗا تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ نِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ

Waxanda kuma suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, lallai za Mu zaunar da su cikin manya-manyan gidaje a Aljanna (waxanda) qoramu za su riqa gudana ta qarqashinsu suna madawwama a cikinsu. Madalla da ladan masu aiki (nagari)



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 59

ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

(Su ne) waxanda suka yi haquri, kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogara



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 60

وَكَأَيِّن مِّن دَآبَّةٖ لَّا تَحۡمِلُ رِزۡقَهَا ٱللَّهُ يَرۡزُقُهَا وَإِيَّاكُمۡۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Sau tari ga dabba nan da ba za ta iya xaukar arzikinta ba, Allah ne Yake arzuta ta har da ku. Shi ne Mai ji, Masani



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 61

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۖ فَأَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Tabbas da za ka tambaye su: “Wane ne ya halicci sammai da qasa, ya kuma hore rana da wata?” To tabbas za su ce: “Allah ne.” To ta yaya ake karkatar da su (daga kaxaita Shi)?



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 62

ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُ لَهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Allah Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, Ya kuma quntata masa. Lalle Allah Masanin komai ne



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 63

وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِ مَوۡتِهَا لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡقِلُونَ

Kuma tabbas da za ka tambaye su: “Wane ne ya saukar da ruwa daga sama, sai ya raya qasa da shi bayan mutuwarta?” Lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Alhamdu Lillahi.” A’a, yawancinsu dai ba sa hankalta



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 64

وَمَا هَٰذِهِ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَآ إِلَّا لَهۡوٞ وَلَعِبٞۚ وَإِنَّ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَ لَهِيَ ٱلۡحَيَوَانُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Kuma wannan rayuwar duniya ba komai ba ce face sharholiya da wasa. Kuma lalle (rayuwar) gidan lahira ita ce rayuwa, in da sun kasance sun sani



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 65

فَإِذَا رَكِبُواْ فِي ٱلۡفُلۡكِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ إِذَا هُمۡ يُشۡرِكُونَ

To idan suka hau jiragen ruwa sukan roqi Allah suna masu tsantsanta addini a gare Shi; to lokacin da Ya tserar da su zuwa tudu sai ga su suna yin shirka



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 66

لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ وَلِيَتَمَتَّعُواْۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

Don su kafirce wa abin da Muka ba su, kuma don su ji daxi; to da sannu za su sani



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 67

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا جَعَلۡنَا حَرَمًا ءَامِنٗا وَيُتَخَطَّفُ ٱلنَّاسُ مِنۡ حَوۡلِهِمۡۚ أَفَبِٱلۡبَٰطِلِ يُؤۡمِنُونَ وَبِنِعۡمَةِ ٱللَّهِ يَكۡفُرُونَ

Yanzu ba su ga cewa, Mu Muka sanya musu Harami amintacce ba, alhali kuwa ana ta fauce mutane a kewayensu[1]? Shin yanzu sa riqa yin imani da qarya su kuma riqa kafirce wa ni’imar Allah?


1- Watau ana ta kai musu hare-hare ana kashe su, ana kama su ribatattun yaqi, a mayar da su bayi.


Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 68

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُۥٓۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡكَٰفِرِينَ

Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama?



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 69

وَٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ فِينَا لَنَهۡدِيَنَّهُمۡ سُبُلَنَاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَمَعَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Waxanda kuma suka yi jihadi saboda Mu to tabbas za Mu shiryar da su hanyoyinmu[1], kuma lalle Allah Yana tare da masu kyautatawa


1- Watau hanyoyin Allah na alheri, su samu dacewa da bin tafarki madaidaici.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 2

غُلِبَتِ ٱلرُّومُ

An yi galaba a kan Rumawa[1]


1- Watau Farisawa masu bautar wuta sun yi galaba a kan Rumawa masu bin addinin Annabi Isa () a wani yaqi da ya varke tsakaninsu.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 3

فِيٓ أَدۡنَى ٱلۡأَرۡضِ وَهُم مِّنۢ بَعۡدِ غَلَبِهِمۡ سَيَغۡلِبُونَ

A qasa mafi kusa (da su), su kuma da sannu za su yi galaba (a kan Farisa) bayan galabar da aka yi a kansu



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 4

فِي بِضۡعِ سِنِينَۗ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ مِن قَبۡلُ وَمِنۢ بَعۡدُۚ وَيَوۡمَئِذٖ يَفۡرَحُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ

A cikin ‘yan tsirarun shekarun (da ba su kai goma ba). Al’amari a da can da nan gaba na Allah ne. A wannan ranar ne muminai za su yi farin ciki



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 5

بِنَصۡرِ ٱللَّهِۚ يَنصُرُ مَن يَشَآءُۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Da samun nasar Allah (a kan Farisa). Shi Yake taimakon wanda Ya ga dama; domin kuwa Shi ne Mabuwayi, Mai rahama



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 6

وَعۡدَ ٱللَّهِۖ لَا يُخۡلِفُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

(Wannan ya kasance) alqawarin Allah ne; Allah ba Ya sava alqawarinsa, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka) ba