وَقَالَ ٱلَّذِي ٱشۡتَرَىٰهُ مِن مِّصۡرَ لِٱمۡرَأَتِهِۦٓ أَكۡرِمِي مَثۡوَىٰهُ عَسَىٰٓ أَن يَنفَعَنَآ أَوۡ نَتَّخِذَهُۥ وَلَدٗاۚ وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلِنُعَلِّمَهُۥ مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِۚ وَٱللَّهُ غَالِبٌ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِۦ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Wanda ya saye shi kuma daga Masar[1] ya ce da matarsa: “Ki kyautata mazauninsa, muna fatan ya amfane mu, ko kuwa mu riqe shi a matsayin xa.” (Allah Ya ci gaba da cewa): Kamar haka Muka tabbatar da Yusufu a bayan qasa don kuma Mu sanar da shi fassarar mafarkai. Allah kuwa Mai rinjaye ne a bisa al’amarinsa, sai dai yawancin mutane ba sa ganewa
1- Shi ne babban minista mai kula da tattalin arziki na qasar Masar, ana masa laqabi da Azizu.
وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥٓ ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lokacin kuma da qarfinsa ya kawo sai Muka ba shi hikima da ilimi. Kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
وَرَٰوَدَتۡهُ ٱلَّتِي هُوَ فِي بَيۡتِهَا عَن نَّفۡسِهِۦ وَغَلَّقَتِ ٱلۡأَبۡوَٰبَ وَقَالَتۡ هَيۡتَ لَكَۚ قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ رَبِّيٓ أَحۡسَنَ مَثۡوَايَۖ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Wadda kuma yake xakinta ta yi qoqarin ya yi lalata da ita, ta kuwa kukkulle qofofi, ta kuma ce: “To ka zo mana!” Ya ce: “Allah Ya kiyashe ni! Lalle shi mai gidana ne, ya kyautata mazaunina. Lalle yadda al’amarin yake su azzalumai ba sa rabauta.”
وَلَقَدۡ هَمَّتۡ بِهِۦۖ وَهَمَّ بِهَا لَوۡلَآ أَن رَّءَا بُرۡهَٰنَ رَبِّهِۦۚ كَذَٰلِكَ لِنَصۡرِفَ عَنۡهُ ٱلسُّوٓءَ وَٱلۡفَحۡشَآءَۚ إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Lalle kuma ta yi niyyar ta rarumo shi, shi kuma ya yi niyyar karkata gare ta, ba don ya ga wata hujja ta Ubangijinsa ba. Kamar haka (Muka nuna masa hujjar) don Mu kawar da mummunan aiki da varna daga gare shi. Lalle shi yana daga bayinmu zavavvu
وَٱسۡتَبَقَا ٱلۡبَابَ وَقَدَّتۡ قَمِيصَهُۥ مِن دُبُرٖ وَأَلۡفَيَا سَيِّدَهَا لَدَا ٱلۡبَابِۚ قَالَتۡ مَا جَزَآءُ مَنۡ أَرَادَ بِأَهۡلِكَ سُوٓءًا إِلَّآ أَن يُسۡجَنَ أَوۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Suka kuma yiwo rige wajen qofa, sai kuwa ta yaga rigarsa daga baya, kuma suka ci karo da mijinta daf da qofar, ta ce: “Ba wani sakamakon da ya cancanta ga wanda ya yi nufin mummunan abu da iyalinka in ban da kawai a xaure shi, ko kuwa a yi masa azaba mai raxaxi.”
قَالَ هِيَ رَٰوَدَتۡنِي عَن نَّفۡسِيۚ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن قُبُلٖ فَصَدَقَتۡ وَهُوَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ
(Annabi Yusufu) ya ce: “Ita ce ta neme ni”. Wani shaida kuwa daga danginta ya shaida (cewa): “Idan an yaga rigarsa ta gaba, to ta yi gaskiya shi kuwa yana cikin masu qarya
وَإِن كَانَ قَمِيصُهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٖ فَكَذَبَتۡ وَهُوَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ
“Idan kuwa an yaga rigarsa ta baya, to ta yi qarya shi kuwa yana daga masu gaskiya.”
فَلَمَّا رَءَا قَمِيصَهُۥ قُدَّ مِن دُبُرٖ قَالَ إِنَّهُۥ مِن كَيۡدِكُنَّۖ إِنَّ كَيۡدَكُنَّ عَظِيمٞ
To yayin da (mijin nata) ya ga an yaga rigarsa ta baya ne, sai ya ce: “Lalle wannan yana daga irin makircinku; lalle makircinku kuwa yana da girma.”
يُوسُفُ أَعۡرِضۡ عَنۡ هَٰذَاۚ وَٱسۡتَغۡفِرِي لِذَنۢبِكِۖ إِنَّكِ كُنتِ مِنَ ٱلۡخَاطِـِٔينَ
“Kai Yusufu, ka kau da kai daga wannan (magana). Ke kuma ki nemi gafarar laifinki, lalle ke kin zamanto daga masu laifi.”
۞وَقَالَ نِسۡوَةٞ فِي ٱلۡمَدِينَةِ ٱمۡرَأَتُ ٱلۡعَزِيزِ تُرَٰوِدُ فَتَىٰهَا عَن نَّفۡسِهِۦۖ قَدۡ شَغَفَهَا حُبًّاۖ إِنَّا لَنَرَىٰهَا فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Waxansu mata kuma a cikin garin suka ce: “Matar Azizu tana neman yaron gidanta; tsananin son sa ya rufe mata zuciya; lalle mu dai muna ganin ta a kan kuskure mabayyani.”
فَلَمَّا سَمِعَتۡ بِمَكۡرِهِنَّ أَرۡسَلَتۡ إِلَيۡهِنَّ وَأَعۡتَدَتۡ لَهُنَّ مُتَّكَـٔٗا وَءَاتَتۡ كُلَّ وَٰحِدَةٖ مِّنۡهُنَّ سِكِّينٗا وَقَالَتِ ٱخۡرُجۡ عَلَيۡهِنَّۖ فَلَمَّا رَأَيۡنَهُۥٓ أَكۡبَرۡنَهُۥ وَقَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّ وَقُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا مَلَكٞ كَرِيمٞ
Lokacin da ta ji irin tsegungumansu, sai ta aika musu (da gayyata), ta kuma tanadar musu wurin zaman cin abinci, kuma ta bai wa kowacce xayarsu wuqa, ta kuma ce (da Annabi Yusufu): “Fita ka gilma ta gabansu.” Lokacin da suka gan shi sai suka girmama shi suka yanyanke hannayensu, suka kuma ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah; ai wannan ba mutum ba ne; wannan babban mala’ika ne kawai!”
قَالَتۡ فَذَٰلِكُنَّ ٱلَّذِي لُمۡتُنَّنِي فِيهِۖ وَلَقَدۡ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ فَٱسۡتَعۡصَمَۖ وَلَئِن لَّمۡ يَفۡعَلۡ مَآ ءَامُرُهُۥ لَيُسۡجَنَنَّ وَلَيَكُونٗا مِّنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ
Ta ce: “To wannan shi ne wanda kuka zarge ni a kansa. Haqiqa kuma na neme shi sai ya qi yarda; Wallahi kuwa in bai aikata abin da na umarce shi ba, to za a sa shi kurkuku, kuma lalle zai zamanto cikin wulaqantattu.”
قَالَ رَبِّ ٱلسِّجۡنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِۖ وَإِلَّا تَصۡرِفۡ عَنِّي كَيۡدَهُنَّ أَصۡبُ إِلَيۡهِنَّ وَأَكُن مِّنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ
(Annabi Yusufu) Ya ce: “Ya Ubangijina, kurkuku shi ya fi soyuwa a gare ni kan abin da suke nema na da shi. Idan kuwa ba Ka ije mini makircinsu ba, to zan karkata gare su kuma in zama cikin jahilai.”
فَٱسۡتَجَابَ لَهُۥ رَبُّهُۥ فَصَرَفَ عَنۡهُ كَيۡدَهُنَّۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
To sai Ubangijinsa Ya amsa masa, sai Ya ije masa makircin nasu. Lalle Shi ne Mai ji kuma Masani
ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا رَأَوُاْ ٱلۡأٓيَٰتِ لَيَسۡجُنُنَّهُۥ حَتَّىٰ حِينٖ
Sannan bayan duk sun ga ayoyin (da suke wanke Yusufu daga zargi) sai suka ga dai cewa lalle gara su xaure shi har zuwa wani lokaci
وَدَخَلَ مَعَهُ ٱلسِّجۡنَ فَتَيَانِۖ قَالَ أَحَدُهُمَآ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَعۡصِرُ خَمۡرٗاۖ وَقَالَ ٱلۡأٓخَرُ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَحۡمِلُ فَوۡقَ رَأۡسِي خُبۡزٗا تَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِنۡهُۖ نَبِّئۡنَا بِتَأۡوِيلِهِۦٓۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Wasu samari su biyu kuma suka shiga kurkukun tare da shi; xaya daga cikinsu ya ce: “Lalle na yi mafarki ina matsar giya.” Xayan kuma ya ce: “Lalle na yi mafarki ina xauke da gurasa a kaina, tsuntsaye suna caccakar ta. Ba mu labarin fassararsa; lalle muna ganin ka kana cikin mutane nagari.”
قَالَ لَا يَأۡتِيكُمَا طَعَامٞ تُرۡزَقَانِهِۦٓ إِلَّا نَبَّأۡتُكُمَا بِتَأۡوِيلِهِۦ قَبۡلَ أَن يَأۡتِيَكُمَاۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّيٓۚ إِنِّي تَرَكۡتُ مِلَّةَ قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ
Ya ce: “Babu wani abinci da za a kawo muku sai na iya ba ku labarinsa tun ma kafin a kawo muku shi. Wannan yana daga abin da Ubangijina Ya sanar da ni; lalle ni na bar hanyar mutanen da ba sa ba da gaskiya da Allah, su kuma suna masu kafircewa da ranar lahira
وَٱتَّبَعۡتُ مِلَّةَ ءَابَآءِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشۡرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ عَلَيۡنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ
“Na kuma bi hanyar iyayena Ibrahimu da Is’haqa da kuma Yaqubu. Bai kamace mu ba a ce mu tara wani abu da Allah. Wannan yana daga falalar Allah a gare mu da kuma sauran mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa godewa
يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ ءَأَرۡبَابٞ مُّتَفَرِّقُونَ خَيۡرٌ أَمِ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ
“Ya abokaina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah Xaya Mai rinjaye?
مَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ أَسۡمَآءٗ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
“Ba komai kuke bauta wa ba- bayan Allah- sai wasu sunaye da kuka qaga ku da iyayenku, waxanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba. Hukunci na Allah ne kawai; Ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kaxai. Wannan shi ne addini miqaqqe, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka)
يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ أَمَّآ أَحَدُكُمَا فَيَسۡقِي رَبَّهُۥ خَمۡرٗاۖ وَأَمَّا ٱلۡأٓخَرُ فَيُصۡلَبُ فَتَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِن رَّأۡسِهِۦۚ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ٱلَّذِي فِيهِ تَسۡتَفۡتِيَانِ
“Ya abokaina na kurkuku, amma xaya daga cikinku zai riqa shayar da mai gidansa giya ne; amma xaya kuwa za a tsire shi ne, sannan tsuntsaye su zo su riqa cakar kansa. An zartar da al’amarin da kuke fatawa game da shi.”
وَقَالَ لِلَّذِي ظَنَّ أَنَّهُۥ نَاجٖ مِّنۡهُمَا ٱذۡكُرۡنِي عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَىٰهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ ذِكۡرَ رَبِّهِۦ فَلَبِثَ فِي ٱلسِّجۡنِ بِضۡعَ سِنِينَ
Kuma ya ce wa wanda ya tabbatar da cewa shi zai tsira daga cikinsu: “Ka tuna wa mai gidanka ni;” sai Shaixan ya mantar da shi tuna wa mai gidan nasa, sai ya zauna a kurkuku ‘yan shekaru
وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ إِنِّيٓ أَرَىٰ سَبۡعَ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعَ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖۖ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ أَفۡتُونِي فِي رُءۡيَٰيَ إِن كُنتُمۡ لِلرُّءۡيَا تَعۡبُرُونَ
Sarki kuma ya ce (da jama’arsa): “Lalle na yi mafarkin shanu guda bakwai masu qiba da wasu bakwan qanjamammu suna cinye su da kuma zangarnu guda bakwai koraye da wasu bakwai busassu. Ya ku manyan malamai, ku sanar da ni fassarar mafarkin nan nawa in kun iya fassara mafarki.”
قَالُوٓاْ أَضۡغَٰثُ أَحۡلَٰمٖۖ وَمَا نَحۡنُ بِتَأۡوِيلِ ٱلۡأَحۡلَٰمِ بِعَٰلِمِينَ
Suka ce: “Ai (wannan) kwashe-kwashen mafarki ne (kawai); mu kuma ba masana fassarar mafarki ne ba.”
وَقَالَ ٱلَّذِي نَجَا مِنۡهُمَا وَٱدَّكَرَ بَعۡدَ أُمَّةٍ أَنَا۠ أُنَبِّئُكُم بِتَأۡوِيلِهِۦ فَأَرۡسِلُونِ
Wanda kuwa ya tsiran nan daga cikinsu, ya kuma tuna bayan zamani mai tsawo, ya ce: “Ni zan ba ku labarin fassararsa; to ku aike ni.”
يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفۡتِنَا فِي سَبۡعِ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعِ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖ لَّعَلِّيٓ أَرۡجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَعۡلَمُونَ
(Ya zo kurkuku ya ce): “Ya Yusufu, ya mai riqon gaskiya, ka ba mu fatawar (mafarki) game da shanu bakwai masu qiba ga wasu bakwan qanjamammu suna cinye su, da kuma zangarnu guda bakwai korayr da wasu bakwai busassu, don in koma wajen mutanen (da suka turo ni) saboda su sani.”
قَالَ تَزۡرَعُونَ سَبۡعَ سِنِينَ دَأَبٗا فَمَا حَصَدتُّمۡ فَذَرُوهُ فِي سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تَأۡكُلُونَ
(Annabi Yusufu) ya ce: “Za ku yi noma shekara bakwai a jere; to abin da kuka girba sai ku bar shi a zangarniyarsa, sai kaxan daga abin da za ku ci
ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ سَبۡعٞ شِدَادٞ يَأۡكُلۡنَ مَا قَدَّمۡتُمۡ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تُحۡصِنُونَ
“Sannan bayan wannan wasu (shekarun) bakwai masu tsanani za su zo su cinye abin da kuka tanada a cikinsu, sai xan kaxan daga abin da kuke adanawa
ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَامٞ فِيهِ يُغَاثُ ٱلنَّاسُ وَفِيهِ يَعۡصِرُونَ
“Sannan kuma wata shekara za ta zo wadda a cikinta ne mutane za su sami ruwa, a cikinta ne kuma za su tatsi (abubuwan sha).”
وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ ٱئۡتُونِي بِهِۦۖ فَلَمَّا جَآءَهُ ٱلرَّسُولُ قَالَ ٱرۡجِعۡ إِلَىٰ رَبِّكَ فَسۡـَٔلۡهُ مَا بَالُ ٱلنِّسۡوَةِ ٱلَّـٰتِي قَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّۚ إِنَّ رَبِّي بِكَيۡدِهِنَّ عَلِيمٞ
Sarki kuwa ya ce: “Ku zo min da shi.” Lokacin da xan aiken ya zo masa (ya ce Sarki na kira), sai ya ce: “Koma wurin mai gidanka ka tambaye shi, mene ne halin matan da suka yanyanke hannayensu? Lalle Ubangijina Yana sane da makircinsu.”