Capítulo: Suratu Hud

Verso : 114

وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّـٰكِرِينَ

Ka kuma tsai da salla farkon rana da qarshenta da kuma farkon dare. Lalle kyawawan (ayyuka) suna shafe munana. Wannan tunasarwa ne ga masu tunawa



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 115

وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka yi haquri, domin lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 116

فَلَوۡلَا كَانَ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِن قَبۡلِكُمۡ أُوْلُواْ بَقِيَّةٖ يَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡفَسَادِ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّنۡ أَنجَيۡنَا مِنۡهُمۡۗ وَٱتَّبَعَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَآ أُتۡرِفُواْ فِيهِ وَكَانُواْ مُجۡرِمِينَ

Ina ma da a ce an samu mutanen kirki daga tsarekun da suka gabace ku da za su riqa hana yaxuwar varna a bayan qasa? Sai ‘yan kaxan kawai (aka samu) daga waxanda Muka tserar cikinsu. Waxanda kuma suka yi zalunci sai suka bi abin da aka wadata su da shi, suka kuwa zamanto masu laifi



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 117

وَمَا كَانَ رَبُّكَ لِيُهۡلِكَ ٱلۡقُرَىٰ بِظُلۡمٖ وَأَهۡلُهَا مُصۡلِحُونَ

Kuma Ubangijinka bai kasance mai hallaka alqarya ba da zalunci alhali kuwa mutanenta suna masu gyara



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 118

وَلَوۡ شَآءَ رَبُّكَ لَجَعَلَ ٱلنَّاسَ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗۖ وَلَا يَزَالُونَ مُخۡتَلِفِينَ

Kuma da Ubangijinka Ya ga dama da lalle Ya yi mutane al’umma xaya (a kan addini xaya). Ba kuwa za su gushe suna masu savawa juna ba



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 119

إِلَّا مَن رَّحِمَ رَبُّكَۚ وَلِذَٰلِكَ خَلَقَهُمۡۗ وَتَمَّتۡ كَلِمَةُ رَبِّكَ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama. A kan haka kuwa Ya halicce su; kuma Kalmar Ubangijinka ta tabbata (cewa): Lalle zan cika Jahannama da aljannu da mutane baki xaya



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 120

وَكُلّٗا نَّقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلرُّسُلِ مَا نُثَبِّتُ بِهِۦ فُؤَادَكَۚ وَجَآءَكَ فِي هَٰذِهِ ٱلۡحَقُّ وَمَوۡعِظَةٞ وَذِكۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

Muna labarta maka kowanne daga labarun manzanni, abin da za Mu kwantar da zuciyarka da shi. Gaskiya kuwa ta zo maka cikin wannan (Surar) da izina da gargaxi ga muminai



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 121

وَقُل لِّلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ ٱعۡمَلُواْ عَلَىٰ مَكَانَتِكُمۡ إِنَّا عَٰمِلُونَ

Kuma ka ce da waxanda ba sa yin imani: “Ku yi aiki a irin hanyarku, mu ma za mu yi aiki (a irin tamu)



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 122

وَٱنتَظِرُوٓاْ إِنَّا مُنتَظِرُونَ

“Kuma ku saurara, haqiqa (mu ma) masu sauraro ne.”



Capítulo: Suratu Hud

Verso : 123

وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ يُرۡجَعُ ٱلۡأَمۡرُ كُلُّهُۥ فَٱعۡبُدۡهُ وَتَوَكَّلۡ عَلَيۡهِۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Kuma (sanin) gaibu na sammai da na qasa na Allah ne, kuma gare Shi ake komar da dukkanin al’amari. To ka bauta masa kuma ka dogara gare Shi. Ubangijinka kuwa ba gafalalle ba ne ga abin da kuke aikatawa



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 1

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

ALIF LAM RA[1]. Waxannan ayoyi ne na Littafi mabayyani


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 2

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Lalle Mu Muka saukar da shi Alqur’ani da (harshen) Larabci don ku hankalta



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 3

نَحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ أَحۡسَنَ ٱلۡقَصَصِ بِمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ

Mu ne Muke labarta maka (labari) mafi kyan labartawa ta hanyar yi maka wahayin wannan Alqur’ani, ko da yake gabaninsa kana cikin marasa sanin(sa)



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 4

إِذۡ قَالَ يُوسُفُ لِأَبِيهِ يَـٰٓأَبَتِ إِنِّي رَأَيۡتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوۡكَبٗا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ رَأَيۡتُهُمۡ لِي سَٰجِدِينَ

(Ka tuna) lokacin da Yusufu ya ce da babansa[1]: “Ya babana, lalle na yi mafarkin taurari goma sha xaya da rana da wata[2], na gan su suna yi min sujjada.”


1- Babansa shi ne Annabi Ya’aqub () xan Annabi Ishaq () xan Annabi Ibrahim ().


2- Taurari goma sha xaya su ne ‘yan’uwansa goma sha xaya; rana kuwa tana nufin mahaifiyarsa; wata kuwa yana nufin mahaifinsa Annabi Ya’aqub ().


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 5

قَالَ يَٰبُنَيَّ لَا تَقۡصُصۡ رُءۡيَاكَ عَلَىٰٓ إِخۡوَتِكَ فَيَكِيدُواْ لَكَ كَيۡدًاۖ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Ya ce: “Ya xana, kada ka labarta mafarkinka ga ‘yan’uwanka, sai su shirya maka makirci; lalle Shaixan maqiyi ne mai bayyana qiyayya ga mutum



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 6

وَكَذَٰلِكَ يَجۡتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأۡوِيلِ ٱلۡأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَعَلَىٰٓ ءَالِ يَعۡقُوبَ كَمَآ أَتَمَّهَا عَلَىٰٓ أَبَوَيۡكَ مِن قَبۡلُ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

“Kamar haka ne kuma Ubangijinka zai zave ka Ya kuma sanar da kai wani abu daga fassarar mafarkai, Ya kuma cika ni’imarsa a gare ka da kuma ga iyalin Ya’aqubu kamar yadda tun tuni Ya cika ta ga iyayenka Ibrahimu da Is’haqa. Lalle Ubangijinka Masani ne Mai hikima.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 7

۞لَّقَدۡ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخۡوَتِهِۦٓ ءَايَٰتٞ لِّلسَّآئِلِينَ

Haqiqa akwai ayoyi ga matambaya dangane da (labarin) Yusufu shi da ‘yan’uwansa



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 8

إِذۡ قَالُواْ لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰٓ أَبِينَا مِنَّا وَنَحۡنُ عُصۡبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

(Ka tuna) lokacin da (‘yan’uwan) suka ce: “Lalle Yusufu da xan’uwansa[1] babanmu ya fi son su da mu, ga mu kuwa jama’a masu yawa. Lalle babanmu yana cikin kuskure mabayyani


1- Shi ne Binyaminu, xan’uwansa ne shaqiqi.


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 9

ٱقۡتُلُواْ يُوسُفَ أَوِ ٱطۡرَحُوهُ أَرۡضٗا يَخۡلُ لَكُمۡ وَجۡهُ أَبِيكُمۡ وَتَكُونُواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ قَوۡمٗا صَٰلِحِينَ

“Ku kashe Yusufu ko kuma ku jefa shi wata qasa, (yin haka) zai juyo muku fuskar babanku, sai kuma ku kasance salihai bayansa[1].”


1- Watau su tuba su nemi yafiyar Allah ().


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 10

قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ لَا تَقۡتُلُواْ يُوسُفَ وَأَلۡقُوهُ فِي غَيَٰبَتِ ٱلۡجُبِّ يَلۡتَقِطۡهُ بَعۡضُ ٱلسَّيَّارَةِ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ

Wani mai magana daga cikinsu ya ce: “Kada ku kashe Yusufu, ku jefa shi cikin duhun kururrumar rijiya, wasu ayarin matafiya za su tsince shi, in har haka za ku yi.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 11

قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَا مَا لَكَ لَا تَأۡمَ۬نَّا عَلَىٰ يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُۥ لَنَٰصِحُونَ

Suka ce: “Ya babanmu, me ya sa ne ba ka amince mana game da Yusufu, alhali kuwa lalle mu ba shakka masu kula da shi ne?



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 12

أَرۡسِلۡهُ مَعَنَا غَدٗا يَرۡتَعۡ وَيَلۡعَبۡ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

“Ka tura shi gobe tare da mu ya yi kiwo, ya kuma yi wasa, lalle kuma mu tabbas za Mu kiyaye shi.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 13

قَالَ إِنِّي لَيَحۡزُنُنِيٓ أَن تَذۡهَبُواْ بِهِۦ وَأَخَافُ أَن يَأۡكُلَهُ ٱلذِّئۡبُ وَأَنتُمۡ عَنۡهُ غَٰفِلُونَ

Ya ce: “Lalle tabbas tafiyarku da shi za ta baqanta mini rai, ina kuma tsoron kyarkeci ya cinye shi ba da saninku ba.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 14

قَالُواْ لَئِنۡ أَكَلَهُ ٱلذِّئۡبُ وَنَحۡنُ عُصۡبَةٌ إِنَّآ إِذٗا لَّخَٰسِرُونَ

Suka ce: “Lalle idan kyarkeci ya cinye shi ga mu kuwa muna da yawa kuma majiya qarfi to ashe lalle mun tave.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 15

فَلَمَّا ذَهَبُواْ بِهِۦ وَأَجۡمَعُوٓاْ أَن يَجۡعَلُوهُ فِي غَيَٰبَتِ ٱلۡجُبِّۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ لَتُنَبِّئَنَّهُم بِأَمۡرِهِمۡ هَٰذَا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

To lokacin da suka tafi da shi suka kuma haxu a kan su saka shi cikin duhun kururrumar rijiya. Muka kuma yi masa wahayi (da cewa): “Wallahi (wata rana) za ka ba su labarin wannan al’amari nasu alhali su ba sa jin (haka zai faru).”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 16

وَجَآءُوٓ أَبَاهُمۡ عِشَآءٗ يَبۡكُونَ

Suka kuwa dawo wa babansu da lisha suna kuka



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 17

قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَآ إِنَّا ذَهَبۡنَا نَسۡتَبِقُ وَتَرَكۡنَا يُوسُفَ عِندَ مَتَٰعِنَا فَأَكَلَهُ ٱلذِّئۡبُۖ وَمَآ أَنتَ بِمُؤۡمِنٖ لَّنَا وَلَوۡ كُنَّا صَٰدِقِينَ

Suka ce: “Ya babanmu, mun tafi muna wasan rige muka kuma bar Yusufu wurin kayanmu, sai kyarkeci ya cinye shi. Ba kuwa za ka gaskanta mu ba ko da muna da gaskiya.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 18

وَجَآءُو عَلَىٰ قَمِيصِهِۦ بِدَمٖ كَذِبٖۚ قَالَ بَلۡ سَوَّلَتۡ لَكُمۡ أَنفُسُكُمۡ أَمۡرٗاۖ فَصَبۡرٞ جَمِيلٞۖ وَٱللَّهُ ٱلۡمُسۡتَعَانُ عَلَىٰ مَا تَصِفُونَ

Suka kuma zo da jinin qarya a rigarsa[1]. (Babansu) ya ce: “Ba haka ba ne, zuciyarku dai ta shirya muku wani abu. Saboda haka (ba ni da wani abin yi) sai haquri nagari; Allah kuma Shi ne wanda ake neman taimakonsa a kan abin da kuke sifantawa.”


1- Watau suka zo da rigar Yusufu cava-cava da jini don su tabbatar da gaskiyarsu, amma sun manta dabba ba za ta cinye mutum ba ba tare da yayyaga tufafin jikinsa ba.


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 19

وَجَآءَتۡ سَيَّارَةٞ فَأَرۡسَلُواْ وَارِدَهُمۡ فَأَدۡلَىٰ دَلۡوَهُۥۖ قَالَ يَٰبُشۡرَىٰ هَٰذَا غُلَٰمٞۚ وَأَسَرُّوهُ بِضَٰعَةٗۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Da wasu ayarin matafiya suka zo sai suka tura mai nemo musu ruwa, sai ya zura gugansa (a rijiyar); sai ya ce: “Abin farin ciki ya same ni, wannan yaro ne;” suka kuma voye shi a matsayin kayan kiri. Allah kuwa Masanin abin da suke aikatawa ne



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 20

وَشَرَوۡهُ بِثَمَنِۭ بَخۡسٖ دَرَٰهِمَ مَعۡدُودَةٖ وَكَانُواْ فِيهِ مِنَ ٱلزَّـٰهِدِينَ

Suka kuma sayar da shi araha da ‘yan dirhamai qirgaggu, suka zamanto kuma suna masu tsantsami game da shi