Capítulo: Suratul Fil

Verso : 1

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصۡحَٰبِ ٱلۡفِيلِ

Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya yi wa ma’abota giwa[1] ba?


1- Watau runduna ce ta mayaqa daga qasar Yaman qarqashin jagorancin Abrahata, suka nufo Makka da niyyar rushe Xakin Ka’aba. A tare da su akwai wata babbar giwa. Allah ya hallaka su baki xaya..


Capítulo: Suratul Fil

Verso : 2

أَلَمۡ يَجۡعَلۡ كَيۡدَهُمۡ فِي تَضۡلِيلٖ

Ashe bai mayar da makircinsu cikin watsewa ba?



Capítulo: Suratul Fil

Verso : 3

وَأَرۡسَلَ عَلَيۡهِمۡ طَيۡرًا أَبَابِيلَ

Ya kuma aiko musu da tsuntsaye dodo-dodo?



Capítulo: Suratul Fil

Verso : 4

تَرۡمِيهِم بِحِجَارَةٖ مِّن سِجِّيلٖ

Suna jifan su da duwatsu na qonanniyar laka?



Capítulo: Suratul Fil

Verso : 5

فَجَعَلَهُمۡ كَعَصۡفٖ مَّأۡكُولِۭ

Sai da Ya mayar da su kamar karmami da aka cinye[1]?


1- Wannan babban abu ya auku ne a shekara ta 571 bayan haihuwar Annabi Isa (). A shekarar ne aka haifi Manzon Allah ().