Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 31

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا قَالُواْ قَدۡ سَمِعۡنَا لَوۡ نَشَآءُ لَقُلۡنَا مِثۡلَ هَٰذَآ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu sai su ce: “Haqiqa mun ji, ai da mun ga dama ba shakka da mun faxi irin wannan, wannan ba komai ba ne sai tatsuniyoyin mutanen da.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 32

وَإِذۡ قَالُواْ ٱللَّهُمَّ إِن كَانَ هَٰذَا هُوَ ٱلۡحَقَّ مِنۡ عِندِكَ فَأَمۡطِرۡ عَلَيۡنَا حِجَارَةٗ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ أَوِ ٱئۡتِنَا بِعَذَابٍ أَلِيمٖ

Ka tuna kuma lokacin da suka ce: “Ya Allah, idan wannan (Alqur’ani) ya zamanto gaskiya ne daga wurinka yake, to sai Ka yi mana ruwan duwatsu daga sama ko kuma Ka kawo mana da wata azaba mai raxaxi.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 33

وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُعَذِّبَهُمۡ وَأَنتَ فِيهِمۡۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ مُعَذِّبَهُمۡ وَهُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ

Allah kuwa bai zamanto Mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikinsu, kuma Allah ba zai yi musu azaba ba alhali suna neman gafara



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 34

وَمَا لَهُمۡ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ ٱللَّهُ وَهُمۡ يَصُدُّونَ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَمَا كَانُوٓاْ أَوۡلِيَآءَهُۥٓۚ إِنۡ أَوۡلِيَآؤُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُتَّقُونَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Me zai hana Allah Ya yi musu azaba alhali su suna hana mutane zuwa Masallaci mai alfarma, alhali kuwa ba su zamanto masu qaunar Sa na haqiqa ba. Masu qaunar Sa na haqiqa su ne masu taqawa, sai dai yawancinsu ba sa sanin (haka)



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 35

وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمۡ عِندَ ٱلۡبَيۡتِ إِلَّا مُكَآءٗ وَتَصۡدِيَةٗۚ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡفُرُونَ

Kuma sallarsu a Xakin (Ka’aba) ba ta zamanto ba sai fito da tafi. Sai ku xanxani azaba saboda abin da kuka zamanto kuna yi na kafirci



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 36

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ لِيَصُدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيۡهِمۡ حَسۡرَةٗ ثُمَّ يُغۡلَبُونَۗ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحۡشَرُونَ

Lalle waxanda suka kafirta suna kashe dukiyoyinsu don su toshe hanyar Allah. To da sannu za su kashe ta (dukiyar) sannan ta zama nadama a gare su, sannan kuma a rinjaye su. Waxanda kuwa suka kafirta a Jahannama za a tattara su



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 37

لِيَمِيزَ ٱللَّهُ ٱلۡخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ وَيَجۡعَلَ ٱلۡخَبِيثَ بَعۡضَهُۥ عَلَىٰ بَعۡضٖ فَيَرۡكُمَهُۥ جَمِيعٗا فَيَجۡعَلَهُۥ فِي جَهَنَّمَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Don Allah Ya ware mummuna daga kyakkyawa, Ya kuma haxa mummuna wani a kan wani, sannan Ya tattara shi gaba xaya cikin Jahannama. Waxannan su ne asararru



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 38

قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِن يَنتَهُواْ يُغۡفَرۡ لَهُم مَّا قَدۡ سَلَفَ وَإِن يَعُودُواْ فَقَدۡ مَضَتۡ سُنَّتُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Ka ce da waxanda suka kafirta idan suka daina, to za a gafarta musu abin da ya riga ya wuce, idan kuma suka koma to fa ba shakka al’adar mutanen farko ta gabata[1]


1- Watau yadda Allah () ya hallaka al’ummun da suka gabata waxanda suka qaryata annabawansu.


Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 39

وَقَٰتِلُوهُمۡ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتۡنَةٞ وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُۥ لِلَّهِۚ فَإِنِ ٱنتَهَوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Kuma ku yaqe su har sai ya zamanto ba wata fitina[1], addini kuma ya zamanto dukkaninsa na Allah. Sannan idan suka daina, to lalle Allah Mai ganin abin da suke aikatawa ne


1- Watau watsuwar shirka a cikin al’umma da yunqurin hana mutane karvar gaskiya.


Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 40

وَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ مَوۡلَىٰكُمۡۚ نِعۡمَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَنِعۡمَ ٱلنَّصِيرُ

Idan kuma suka ba da baya, to ku sani cewa, Allah (Shi ne) Majivincin al’amarinku. Madalla da wannan Majivinci, kuma madalla da wannan Mai taimako



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 41

۞وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَا غَنِمۡتُم مِّن شَيۡءٖ فَأَنَّ لِلَّهِ خُمُسَهُۥ وَلِلرَّسُولِ وَلِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ عَبۡدِنَا يَوۡمَ ٱلۡفُرۡقَانِ يَوۡمَ ٱلۡتَقَى ٱلۡجَمۡعَانِۗ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Kuma ku sani cewa duk abin da kuka samu na ganima to lalle xaya bisa biyar na Allah ne da Manzo da kuma makusantan (Annabi)[1], da marayu da kuma miskinai da kuma matafiya[2], idan kun kasance kun yi imani da Allah da kuma abin da Muka saukar wa bawanmu ranar rabewa (ranar yaqin Badar) ranar da qungiyoyin nan biyu suka haxu. Allah kuwa Mai iko ne a kan komai


1- Su ne Banu Hashim da Banu Muxxalib waxanda aka haramta musu cin zakka.


2- Suran kashi huxun kuwa na mayaqa ne.


Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 42

إِذۡ أَنتُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلۡقُصۡوَىٰ وَٱلرَّكۡبُ أَسۡفَلَ مِنكُمۡۚ وَلَوۡ تَوَاعَدتُّمۡ لَٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡمِيعَٰدِ وَلَٰكِن لِّيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗا لِّيَهۡلِكَ مَنۡ هَلَكَ عَنۢ بَيِّنَةٖ وَيَحۡيَىٰ مَنۡ حَيَّ عَنۢ بَيِّنَةٖۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَسَمِيعٌ عَلِيمٌ

Ku tuna lokacin da kuke a gacin da ya fi kusa (da Madina) su kuma suna gacin da ya fi nisa, ayarin (Abu Sufyan) kuwa yana qasa da ku. Da kuwa kun yi alqawarin (haxuwa a Badar) to babu shakka da kun sava wajen cika alqawarin, sai dai kuma wannan ya faru ne saboda Allah Ya zartar da al’amarin da ya zamanto mai faruwa ne, don wanda ya hallaka ya hallaka da dalili, kuma wanda kuma ya rayu ya rayu da dalili. Lalle Allah Mai ji ne Masani



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 43

إِذۡ يُرِيكَهُمُ ٱللَّهُ فِي مَنَامِكَ قَلِيلٗاۖ وَلَوۡ أَرَىٰكَهُمۡ كَثِيرٗا لَّفَشِلۡتُمۡ وَلَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ سَلَّمَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

Ka tuna lokacin da Allah Yake nuna maka su cikin baccinka suna ‘yan kaxan; da kuwa Ya nuna maka su da yawa fal, to ba shakka da kun tsorata kuma lalle da kun yi jayayya a cikin al’amarin, sai dai kuma Allah Ya kiyaye. Lalle Shi Masanin abin da ke zukata ne



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 44

وَإِذۡ يُرِيكُمُوهُمۡ إِذِ ٱلۡتَقَيۡتُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِكُمۡ قَلِيلٗا وَيُقَلِّلُكُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِهِمۡ لِيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗاۗ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ

Ku kuma tuna lokacin da Yake nuna muku su a yayin da kuka gamu suna ‘yan kaxan a idanuwanku, Yake kuma qarantar da ku a idonsu, saboda Allah Ya hukunta al’amarin da yake mai afkuwa ne. Kuma wurin Allah ne ake mayar da duka al’amura



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 45

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمۡ فِئَةٗ فَٱثۡبُتُواْ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka haxu da wata qungiya (ta mayaqa), to sai ku dage, ku kuma ambaci Allah da yawa, don ku rabauta



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 46

وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَنَٰزَعُواْ فَتَفۡشَلُواْ وَتَذۡهَبَ رِيحُكُمۡۖ وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Kuma ku bi Allah da Manzonsa, kada ku rarrabu sai ku zama matsorata kuma qarfinku ya tafi; ku kuma yi haquri. Lalle Allah Yana tare da masu haquri



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 47

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بَطَرٗا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ

Kada kuma ku zama kamar waxanda suka fito daga gidajensu don fariya da kuma nuna wa mutane (watau riya), suna kuma hana (mutane) bin hanyar Allah. Allah kuwa Mai kewaye abin da suke aikatawa ne



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 48

وَإِذۡ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّي جَارٞ لَّكُمۡۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلۡفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكُمۡ إِنِّيٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوۡنَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku tuna lokacin da Shaixan ya qawata musu ayyukansu, ya kuma ce: “Babu wasu mutane a yau da za su yi galaba a kanku, lalle kuma ni maqocinku ne.” Saboda haka lokacin da qungiyoyin biyu suka haxu sai ya tsere a guje, ya kuma ce: “Lalle ni ba ruwana da ku, lalle ni ina ganin abin da ku ba kwa gani, lalle ni ina tsoron Allah. Allah kuwa Mai tsananin azaba ne.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 49

إِذۡ يَقُولُ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ غَرَّ هَـٰٓؤُلَآءِ دِينُهُمۡۗ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Ka tuna lokacin da munafuqai da kuma waxanda suke da rauni a zukatansu suke cewa: “Waxannan addininsu ne ya ruxe su.” Duk wanda ya dogara ga Allah kuwa to lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 50

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذۡ يَتَوَفَّى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَضۡرِبُونَ وُجُوهَهُمۡ وَأَدۡبَٰرَهُمۡ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Kuma da za ka ga lokacin da mala’iku suke xaukan ran waxanda suka kafirta, suna dukan fuskokinsu da kuma bayansu, suna kuma (cewa da su): “Ku xanxani azabar quna.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 51

ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيۡسَ بِظَلَّـٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ

“Wannan (ya faru gare ku ne) saboda abin da hannayenku suka aikata, kuma lalle Allah ba Mai zaluntar bayi ne ba.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 52

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

(Al’adar kafiran Makka) kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun kafirce wa ayoyin Allah, saboda haka Allah Ya kama su da zunubansu. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mai tsananin uquba



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 53

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ لَمۡ يَكُ مُغَيِّرٗا نِّعۡمَةً أَنۡعَمَهَا عَلَىٰ قَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Wannan (kuwa) saboda Allah bai kasance Mai canza wata ni’ima da Ya yi wa wasu mutane ba har sai sun canja halayensu, lalle Allah kuma Mai ji ne Masani



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 54

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَۚ وَكُلّٞ كَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun qaryata ayoyin Ubangijinsu, sai Muka hallaka su saboda zunubansu, Muka kuma nutsar da mutanen Fir’auna (a cikin kogi). Dukkaninsu kuwa sun kasance azzalumai



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 55

إِنَّ شَرَّ ٱلدَّوَآبِّ عِندَ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ

Lalle mafi sharrin masu tafiya a bayan qasa a wurin Allah (su ne) waxanda suka kafirta, don haka kuma su ba sa yin imani



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 56

ٱلَّذِينَ عَٰهَدتَّ مِنۡهُمۡ ثُمَّ يَنقُضُونَ عَهۡدَهُمۡ فِي كُلِّ مَرَّةٖ وَهُمۡ لَا يَتَّقُونَ

Waxanda idan ka yi alqawari da su sai su warware alqawarinsu ko da yaushe, ba sa kuma kiyaye dokokin Allah (dangane da alqawari)



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 57

فَإِمَّا تَثۡقَفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡحَرۡبِ فَشَرِّدۡ بِهِم مَّنۡ خَلۡفَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ

Sannan idan ka haxu da su a wurin yaqi, to sai ka fatattaki na bayansu da su, don su (na bayan) sa wa’azantu



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 58

وَإِمَّا تَخَافَنَّ مِن قَوۡمٍ خِيَانَةٗ فَٱنۢبِذۡ إِلَيۡهِمۡ عَلَىٰ سَوَآءٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡخَآئِنِينَ

Kuma idan kana jin tsoron wani ha’inci daga wasu mutane (da ka yi sulhu da su), to sai ka jefar musu shi (sulhun) a bayyane (ba da ha’inci ba). Lalle Allah ba Ya son masu ha’inci



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 59

وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ سَبَقُوٓاْۚ إِنَّهُمۡ لَا يُعۡجِزُونَ

Kuma kada waxanda suka kafirta su yi tsammanin sun tsere, lalle su ba za su gagari (Allah) ba



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 60

وَأَعِدُّواْ لَهُم مَّا ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن قُوَّةٖ وَمِن رِّبَاطِ ٱلۡخَيۡلِ تُرۡهِبُونَ بِهِۦ عَدُوَّ ٱللَّهِ وَعَدُوَّكُمۡ وَءَاخَرِينَ مِن دُونِهِمۡ لَا تَعۡلَمُونَهُمُ ٱللَّهُ يَعۡلَمُهُمۡۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يُوَفَّ إِلَيۡكُمۡ وَأَنتُمۡ لَا تُظۡلَمُونَ

Ku yi musu tanadin abin da kuke iyawa na qarfi da kuma tanadin xaurarrun dawakai, kuna tsorata maqiya Allah kuma maqiyanku da shi (tanadin), har kuma da wasu ban da su da ba ku san su ba, Allah ne kawai Ya san su. Kuma duk irin abin da kuka ciyar cikin hanyar Allah za a cika muku (ladanku) ba kuwa za a zalunce ku ba