Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 31

نَحۡنُ أَوۡلِيَآؤُكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِۖ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَشۡتَهِيٓ أَنفُسُكُمۡ وَلَكُمۡ فِيهَا مَا تَدَّعُونَ

“Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta (Aljanna) za ku sami duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku sami duk abin da kuke nema a cikinta



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 32

نُزُلٗا مِّنۡ غَفُورٖ رَّحِيمٖ

“Liyafa ce daga (Allah) Mai gafara, Mai jin qai.”



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 33

وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 34

وَلَا تَسۡتَوِي ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِي بَيۡنَكَ وَبَيۡنَهُۥ عَدَٰوَةٞ كَأَنَّهُۥ وَلِيٌّ حَمِيمٞ

Kyakkyawan (abu) da mummuna ba za su zama xaya ba. To ka ture mummuna da abin da ya fi kyau, to sai ka ga wanda yake tsakaninsa da kai gaba ce, ya zamanto kamar wani masoyi ne na qut da qut



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 35

وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَمَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٖ

Ba kowa ake bai wa wannan kyakkyawar xabi’ar ba sai waxanda suka yi haquri, ba kowa ake bai wa ita ba sai mai babban rabo



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 36

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Idan kuma wani tunzuri daga Shaixan ya tunzura ka, to sai ka nemi tsari daga Allah; lalle Shi Mai ji ne, Masani



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 38

فَإِنِ ٱسۡتَكۡبَرُواْ فَٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ يُسَبِّحُونَ لَهُۥ بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَهُمۡ لَا يَسۡـَٔمُونَ۩

Idan kuwa sun yi girman kai, to waxanda suke wurin Ubangijinka (mala’iku) suna yi masa tasbihi dare da rana, kuma su ba sa qosawa



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 39

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa lalle za ka ga qasa a qeqashe, to idan Mun saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura (ta fitar da tsirrai). Lalle wanda Ya raya ta Shi ne Mai raya matattu. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 40

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا لَا يَخۡفَوۡنَ عَلَيۡنَآۗ أَفَمَن يُلۡقَىٰ فِي ٱلنَّارِ خَيۡرٌ أَم مَّن يَأۡتِيٓ ءَامِنٗا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ٱعۡمَلُواْ مَا شِئۡتُمۡ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Lalle waxanda suke fanxara game da ayoyinmu[1], ba za su voyu gare Mu ba. Yanzu wanda za a jefa shi a cikin wuta, shi ya fi ko kuma wanda zai zo yana amintacce a ranar alqiyama? Ku aikata abin da kuka ga dama, lalle Shi Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau suke fanxare wa ayoyinsa, suna qaryata su, suna musunta su da jirkita ma’anoninsa ko canza lafuzansu.


Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 41

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِٱلذِّكۡرِ لَمَّا جَآءَهُمۡۖ وَإِنَّهُۥ لَكِتَٰبٌ عَزِيزٞ

Lalle waxanda suka kafirce wa Alqur’ani lokacin da ya zo musu (tabbas Allah zai saka musu). Lalle kuma shi littafi ne mabuwayi



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 42

لَّا يَأۡتِيهِ ٱلۡبَٰطِلُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَلَا مِنۡ خَلۡفِهِۦۖ تَنزِيلٞ مِّنۡ حَكِيمٍ حَمِيدٖ

Varna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa; saukakke ne daga Mai hikima, Sha-yabo



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 43

مَّا يُقَالُ لَكَ إِلَّا مَا قَدۡ قِيلَ لِلرُّسُلِ مِن قَبۡلِكَۚ إِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغۡفِرَةٖ وَذُو عِقَابٍ أَلِيمٖ

Ba abin da ake faxa maka sai irin abin da aka faxa wa manzanni a gabaninka[1]. Lalle Ubangijinka Mai gafara ne, kuma Mai uquba mai raxaxi ne


1- Watau na qaryata su da yi musu izgili.


Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 44

وَلَوۡ جَعَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا أَعۡجَمِيّٗا لَّقَالُواْ لَوۡلَا فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥٓۖ ءَا۬عۡجَمِيّٞ وَعَرَبِيّٞۗ قُلۡ هُوَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ هُدٗى وَشِفَآءٞۚ وَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ فِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٞ وَهُوَ عَلَيۡهِمۡ عَمًىۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يُنَادَوۡنَ مِن مَّكَانِۭ بَعِيدٖ

Da Mun sanya shi Alqur’ani Ba’ajame da tabbas za su ce: “Me ya hana a bayyana ayoyinsa? Yanzu (a ce Alqur’ani) Ba’ajame (Annabi kuma) Balarabe?” Ka ce: “Shi ga waxanda suka yi imani shiriya ne da waraka. Waxanda kuwa ba sa yin imani akwai nauyi cikin kunnuwansu, shi kuma makanta ne a gare su.” Waxannan (sun yi kama da waxanda) ake kira daga wuri mai nisa



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 45

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَٱخۡتُلِفَ فِيهِۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡۚ وَإِنَّهُمۡ لَفِي شَكّٖ مِّنۡهُ مُرِيبٖ

Haqiqa Mun bai wa Musa Littafin (Attaura), sai aka yi savani a cikinsa, kuma ba don Kalma ta gabata daga Ubangijinka ba, tabbas da an yi hukunci a tsakaninsu. Lalle kuma su, tabbas suna cikin shakka mai sa kokwanto a game da shi



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 46

مَّنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَسَآءَ فَعَلَيۡهَاۗ وَمَا رَبُّكَ بِظَلَّـٰمٖ لِّلۡعَبِيدِ

Wanda ya yi aiki nagari, to kansa ya yi wa, wanda kuma ya munana, to a kan kansa ya yi wa. Ubangijnka ba Mai zaluntar bayi ba ne



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 47

۞إِلَيۡهِ يُرَدُّ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِۚ وَمَا تَخۡرُجُ مِن ثَمَرَٰتٖ مِّنۡ أَكۡمَامِهَا وَمَا تَحۡمِلُ مِنۡ أُنثَىٰ وَلَا تَضَعُ إِلَّا بِعِلۡمِهِۦۚ وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ أَيۡنَ شُرَكَآءِي قَالُوٓاْ ءَاذَنَّـٰكَ مَامِنَّا مِن شَهِيدٖ

Gare shi ne ake mayar da sanin lokacin alqiyama. Kuma babu wasu ‘ya’yan itatuwa da suke fitowa daga kwansonsu, babu kuma wata mace da take xaukan ciki ko take haifewa sai da saninsa. Kuma a ranar da zai yi kiran su cewa: “Ina abokan tarayyar tawa?” Za su ce: “Mun sanar da Kai (a yau) babu wani mai yin shaida daga cikinmu[1].”


1- Watau babu wani da zai ba da shaidar cewa, Allah yana da abokan tarayya.


Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 48

وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَدۡعُونَ مِن قَبۡلُۖ وَظَنُّواْ مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٖ

Kuma abin da suka kasance suna bauta wa a da ya vace musu, suka kuma tabbatar ba su da wata matsera



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 49

لَّا يَسۡـَٔمُ ٱلۡإِنسَٰنُ مِن دُعَآءِ ٱلۡخَيۡرِ وَإِن مَّسَّهُ ٱلشَّرُّ فَيَـُٔوسٞ قَنُوطٞ

Mutum ba ya qosawa wajen roqon alheri, idan kuwa wani sharri ya same shi, to sai ya zama mai tsananin xebe qauna



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 50

وَلَئِنۡ أَذَقۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنَّا مِنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُ لَيَقُولَنَّ هَٰذَا لِي وَمَآ أَظُنُّ ٱلسَّاعَةَ قَآئِمَةٗ وَلَئِن رُّجِعۡتُ إِلَىٰ رَبِّيٓ إِنَّ لِي عِندَهُۥ لَلۡحُسۡنَىٰۚ فَلَنُنَبِّئَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِمَا عَمِلُواْ وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ

Tabbas kuma idan Muka xanxana masa wata rahama tamu bayan wata cuta da ta same shi, tabbas zai riqa cewa: “Wannan nawa ne, kuma ba na tsammanin alqiyama za ta tashi, kuma tabbas idan ma da za a mayar da ni zuwa ga Ubangijina, lalle zan zama mai samun mafi kyan sakamako a wurinsa.” To tabbas za Mu saka wa waxanda suka kafirta da abin da suka aikata, kuma tabbas za Mu xanxana musu azaba mai gwavi



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 51

وَإِذَآ أَنۡعَمۡنَا عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ أَعۡرَضَ وَنَـَٔا بِجَانِبِهِۦ وَإِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ فَذُو دُعَآءٍ عَرِيضٖ

Idan kuma Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya ja jikinsa nesa (daga tuna Allah), kuma idan sharri ya same shi, sai ya zama mai faffaxar addu’a



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 52

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ ثُمَّ كَفَرۡتُم بِهِۦ مَنۡ أَضَلُّ مِمَّنۡ هُوَ فِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

Ka ce: “Ku ba ni labari, idan (Alqur’ani) ya kasance daga wajen Allah, sannan kuka kafirce masa, to wane ne ya fi vata fiye da wanda yake cikin savani mai nisa?”



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 53

سَنُرِيهِمۡ ءَايَٰتِنَا فِي ٱلۡأٓفَاقِ وَفِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمۡ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّۗ أَوَلَمۡ يَكۡفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

Ba da daxewa ba za Mu nuna musu ayoyinmu a cikin nahiyoyi da kuma a kan kawunansu har sai sun gane cewa lalle shi (Alqur’ani) gaskiya ne. Yanzu bai ishe ka ba game da Ubangijinka cewa Shi lalle Mai shaida ne a kan komai?



Capítulo: Suratu Fussilat

Verso : 54

أَلَآ إِنَّهُمۡ فِي مِرۡيَةٖ مِّن لِّقَآءِ رَبِّهِمۡۗ أَلَآ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءٖ مُّحِيطُۢ

Ku saurara, lalle su suna cikin kokwanto ne game da haxuwa da Ubangijnsu. Ku saurara, lalle Shi Mai kewaye komai ne da saninsa