الٓرۚ كِتَٰبٌ أُحۡكِمَتۡ ءَايَٰتُهُۥ ثُمَّ فُصِّلَتۡ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ خَبِيرٍ
ALIF LAM RA[1]. (Wannan) Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa sannan aka bayyana su filla-filla, daga wurin Mai hikima, Masani
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۚ إِنَّنِي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ
Da cewa kada ku bauta wa kowa sai Allah. (Ka ce): “Lalle ni mai yi muku gargaxi ne mai albishir daga gare Shi (Allah)
وَأَنِ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِ يُمَتِّعۡكُم مَّتَٰعًا حَسَنًا إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى وَيُؤۡتِ كُلَّ ذِي فَضۡلٖ فَضۡلَهُۥۖ وَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٖ كَبِيرٍ
“Kuma da cewa, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare Shi, zai jiyar da ku daxi, kyakkyawar jiyarwa zuwa wani lokaci qayyadadde, Ya kuma bai wa duk wani wanda Ya yi abin kirki (sakamakon) kirkinsa. Idan kuwa kuka ba da baya, to lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma
إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
“Zuwa ga Allah ne makomarku; Shi kuwa Mai iko ne a kan komai.”
أَلَآ إِنَّهُمۡ يَثۡنُونَ صُدُورَهُمۡ لِيَسۡتَخۡفُواْ مِنۡهُۚ أَلَا حِينَ يَسۡتَغۡشُونَ ثِيَابَهُمۡ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Ku saurara! Lalle su suna karkatar da qirazansu don su voye masa (Allah). Ku saurara! Ai lokacin da suke lulluva da tufafinsu Yana sane da abin da suke voyewa da kuma abin da suke bayyanawa. Lalle Shi (Allah) Masanin abin da yake cikin zukata ne
۞وَمَا مِن دَآبَّةٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ رِزۡقُهَا وَيَعۡلَمُ مُسۡتَقَرَّهَا وَمُسۡتَوۡدَعَهَاۚ كُلّٞ فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ
Kuma babu wata dabba a ban qasa face arzikinta yana hannun Allah, kuma Yana sane da matabbatarta da ma’ajiyarta[1]. Dukkanin wannan yana nan a cikin littafi mabayyani (shi ne Lauhul Mahafuzu)
1- Watau ya san wurin zamansu da wurin tafiye-tafiyensu, ya san inda za su mutu a binne su.
وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَكَانَ عَرۡشُهُۥ عَلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۗ وَلَئِن قُلۡتَ إِنَّكُم مَّبۡعُوثُونَ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡمَوۡتِ لَيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Shi ne kuma wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, Al’arshinsa kuwa ya kasance a kan ruwa, don Ya jarraba ku a cikinku wa ya fi kyakkyawan aiki. Kuma tabbas idan ka ce (da su): “Lalle za a tashe ku bayan mutuwa,” tabbas kafirai za su ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne sai tsafi mabayyani.”
وَلَئِنۡ أَخَّرۡنَا عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابَ إِلَىٰٓ أُمَّةٖ مَّعۡدُودَةٖ لَّيَقُولُنَّ مَا يَحۡبِسُهُۥٓۗ أَلَا يَوۡمَ يَأۡتِيهِمۡ لَيۡسَ مَصۡرُوفًا عَنۡهُمۡ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Kuma tabbas da Mun jinkirta musu azaba zuwa wani lokaci qayyadadde, lalle za su ce: “Me ya tsare ta?” Ku saurara! Ranar da za ta zo musu ba za a kawar da ita daga kansu ba, kuma abin da suke yi wa izgili zai tabbata a kansu
وَلَئِنۡ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ ثُمَّ نَزَعۡنَٰهَا مِنۡهُ إِنَّهُۥ لَيَـُٔوسٞ كَفُورٞ
Kuma tabbas idan Muka xanxana wa mutum wata rahama daga gare Mu sannan Muka karve ta daga gare shi, lalle shi mai yawan yanke qauna ne, mai kuma yawan kafirci
وَلَئِنۡ أَذَقۡنَٰهُ نَعۡمَآءَ بَعۡدَ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُ لَيَقُولَنَّ ذَهَبَ ٱلسَّيِّـَٔاتُ عَنِّيٓۚ إِنَّهُۥ لَفَرِحٞ فَخُورٌ
Lalle kuma idan Muka xanxana masa daxi bayan ya sha wahala da ta same shi, tabbas zai riqa cewa: “Ai munanan (abubuwa) sun bar ni.” Lalle shi mai farin ciki ne mai yawan alfahari
إِلَّا ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٞ
Sai dai waxanda suka yi haquri suka kuma yi aiki nagari, waxannan suna da gafara da kuma lada mai girma
فَلَعَلَّكَ تَارِكُۢ بَعۡضَ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيۡكَ وَضَآئِقُۢ بِهِۦ صَدۡرُكَ أَن يَقُولُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ كَنزٌ أَوۡ جَآءَ مَعَهُۥ مَلَكٌۚ إِنَّمَآ أَنتَ نَذِيرٞۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٌ
To yanzu za ka bar wani abu daga abin da ake yi maka wahayi da shi, kuma zuciyarka za ta quntata da shi don kawai za su ce: “Me ya hana a saukar masa da wata taska, ko kuma wani mala’ika ya zo tare da shi?” Kai dai mai gargaxi ne kawai. Allah kuma Wakili ne a kan komai
أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ فَأۡتُواْ بِعَشۡرِ سُوَرٖ مِّثۡلِهِۦ مُفۡتَرَيَٰتٖ وَٱدۡعُواْ مَنِ ٱسۡتَطَعۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
A’a, ko cewa suka yi: “Ya qirqire shi ne?” Ka ce: “Ku kawo sura goma kamarsa qagaggu, kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba (ya taimake ku) in kun kasance masu gaskiya.”
فَإِلَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلۡمِ ٱللَّهِ وَأَن لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَهَلۡ أَنتُم مُّسۡلِمُونَ
To idan ba su amsa muku ba, to ku tabbatar cewa lalle an saukar da shi ne (Alqur’ani) da sanin Allah, kuma babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, To shin yanzu za ku miqa wuya?
مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيۡهِمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ فِيهَا وَهُمۡ فِيهَا لَا يُبۡخَسُونَ
Waxanda suke nufin rayuwar duniya da qawace-qawacenta, to za Mu ba su cikakken sakamakon ayyukansu a cikinta, kuma ba za a tauye musu (komai ba)
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَيۡسَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا ٱلنَّارُۖ وَحَبِطَ مَا صَنَعُواْ فِيهَا وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Waxannan su ne waxanda ba su da komai a lahira sai wuta; kuma abin da suka aikata a cikinta (duniyar) ya rushe, kuma abin da suke aikatawa ya lalace
أَفَمَن كَانَ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّهِۦ وَيَتۡلُوهُ شَاهِدٞ مِّنۡهُ وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةًۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ مِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ فَٱلنَّارُ مَوۡعِدُهُۥۚ فَلَا تَكُ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُۚ إِنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ
Shin yanzu wanda yake a kan hujja daga Ubangijinsa, kuma wani mai ba da shaida yana biye da shi (Alqur’ani); a gabaninsa kuma akwai Littafin (Annabi) Musa (wanda yake) abin koyi ne, kuma rahama ne, (zai yi daidai da wanda ba haka ba)? Waxannan suna yin imani da shi. Daga sauran qungiyoyi kuma duk wanda ya kafirce da shi, to fa wuta ce makomarsa. Don haka kada ka kasance cikin kokwanto game da shi (Alqur’ani). Lalle shi gaskiya ne daga Ubangijika yake, sai dai kuma yawancin mutane ba sa yin imani
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ يُعۡرَضُونَ عَلَىٰ رَبِّهِمۡ وَيَقُولُ ٱلۡأَشۡهَٰدُ هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ كَذَبُواْ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ أَلَا لَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya qirqira wa Allah qarya. Waxannan za a kawo su a gaban Ubangijinsu, shaidu kuma (wato mala’iku) su ce: “Waxannan su ne suka yi wa Ubangijinsu qarya. Ku saurara, la’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai
ٱلَّذِينَ يَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجٗا وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ
“Waxanda suke hana bin hanyar Allah, suna kuma son ta a karkace; kuma su ne masu kafircewa da ranar lahira.”
أُوْلَـٰٓئِكَ لَمۡ يَكُونُواْ مُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كَانَ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِنۡ أَوۡلِيَآءَۘ يُضَٰعَفُ لَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ مَا كَانُواْ يَسۡتَطِيعُونَ ٱلسَّمۡعَ وَمَا كَانُواْ يُبۡصِرُونَ
Waxannan ba su zamo masu gagara ba a bayan qasa, kuma ba su da masu jivintar lamarinsu waxanda ba Allah ba, (kuma) za a ninka musu azaba. Ba su kasance sun iya jin (gaskiya) ba, ba su kuma zamanto masu iya ganin (ta) ba
أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ
Waxannan su ne waxanda suka yi asarar kawunansu. Abin da suke qirqira kuma ya vace musu
لَا جَرَمَ أَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡأَخۡسَرُونَ
Ba shakka lalle su ne suka fi asara a lahira
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَأَخۡبَتُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, suka kuma qasqantar da kansu ga Ubangijinsu to waxannan su ne ‘yan Aljanna, su masu dawwama ne a cikinta
۞مَثَلُ ٱلۡفَرِيقَيۡنِ كَٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡأَصَمِّ وَٱلۡبَصِيرِ وَٱلسَّمِيعِۚ هَلۡ يَسۡتَوِيَانِ مَثَلًاۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Misalin jama’ar nan guda biyu (mumini da kafiri) kamar makaho ne da kurma da kuma mai gani da mai ji. Shin ga misali za su zama daidai kuwa? To me ya sa ba za ku wa’azantu ba?
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦٓ إِنِّي لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٌ
Haqiqa kuma Mun aiko Nuhu zuwa ga mutanensa (ya ce da su): “Lalle ni mai gargaxi bayyananne ne a gare ku
أَن لَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۖ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ أَلِيمٖ
“Cewa kada ku bauta wa (kowa) sai Allah. Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wata rana mai raxaxi.”
فَقَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ مَا نَرَىٰكَ إِلَّا بَشَرٗا مِّثۡلَنَا وَمَا نَرَىٰكَ ٱتَّبَعَكَ إِلَّا ٱلَّذِينَ هُمۡ أَرَاذِلُنَا بَادِيَ ٱلرَّأۡيِ وَمَا نَرَىٰ لَكُمۡ عَلَيۡنَا مِن فَضۡلِۭ بَلۡ نَظُنُّكُمۡ كَٰذِبِينَ
Sai manya-manya daga cikin mutanensa, waxanda suka kafirta suka ce (da shi): “Mu fa mun xauke ka kawai mutum ne kamarmu, kuma ba ma ganin wani ya bi ka in ban da wulakantattun cikinmu gidadawa. Kuma ba ma ganin ku da wani fifiko a kanmu; kai muna ma tsammanin ku maqaryata ne.”
قَالَ يَٰقَوۡمِ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كُنتُ عَلَىٰ بَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّي وَءَاتَىٰنِي رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِهِۦ فَعُمِّيَتۡ عَلَيۡكُمۡ أَنُلۡزِمُكُمُوهَا وَأَنتُمۡ لَهَا كَٰرِهُونَ
(Annabi Nuhu) ya ce: “Ya ku mutanena, ku ba ni labari, yanzu idan na zamanto ina riqe da hujja daga Ubangijina, Ya kuma ba ni wata rahama daga gare Shi, sai aka voye muku ita, yanzu ma tilasta muku ita, alhali kuwa kuna qin ta?
وَيَٰقَوۡمِ لَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مَالًاۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِۚ وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْۚ إِنَّهُم مُّلَٰقُواْ رَبِّهِمۡ وَلَٰكِنِّيٓ أَرَىٰكُمۡ قَوۡمٗا تَجۡهَلُونَ
“Kuma ya ku mutanena, ba na tambayar ku wata dukiya a kansa (kiran); ladana a wurin Allah kawai yake. Ni kuwa ba zan kori waxanda suka yi imani ba. Lalle su masu saduwa ne da Ubangijinsu, sai dai ni ina ganin ku mutane ne da kuke jahiltar (gaskiya).”
وَيَٰقَوۡمِ مَن يَنصُرُنِي مِنَ ٱللَّهِ إِن طَرَدتُّهُمۡۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
“Ya ku mutanena, wa zai kare ni daga Allah idan na kore su? Me ya sa ne ba kwa wa’azantuwa?