إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡخَلَّـٰقُ ٱلۡعَلِيمُ
Lalle Ubangijinka Shi ne Mai halitta, Masani
يُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ أَنۡ أَنذِرُوٓاْ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
Yana saukar da mala’iku da wahayi na umarninsa ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa da cewa,: “Ku yi gargaxi cewa,, lalle ba wani abin bauta sai Ni, to sai ku kiyaye dokokina.”
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ تَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Ya halicci sammai da qasa da gaskiya. Ya xaukaka daga abin da suke tara (Shi da shi)
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٖ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٞ مُّبِينٞ
Ya halicci mutum daga maniyyi, sai ga shi mai jayayya a fili
وَٱلۡأَنۡعَٰمَ خَلَقَهَاۖ لَكُمۡ فِيهَا دِفۡءٞ وَمَنَٰفِعُ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Ya kuma halicci dabbobin ni’ima. Kuna da (abin) xumama jiki tattare da su, da kuma sauran abubuwan amfani; daga gare su ne kuma kuke ci
وَعَلَى ٱللَّهِ قَصۡدُ ٱلسَّبِيلِ وَمِنۡهَا جَآئِرٞۚ وَلَوۡ شَآءَ لَهَدَىٰكُمۡ أَجۡمَعِينَ
Kuma bayanin hanya madaidaiciya haqqi ne a kan Allah, daga kuma (hanyar) akwai karkatacciya. Da kuma Ya ga dama lalle da Ya shirye ku gaba xaya
وَإِن تَعُدُّواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ لَا تُحۡصُوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Idan kuma da za ku qirga ni’imar Allah to ba za ku iya qididdige ta ba. Lalle Allah tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai
وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ
Allah kuma Ya san abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa
إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٞ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Abin bautarku Abin bauta ne Xaya, sai dai waxanda ba sa yin imani da ranar lahira zukatansu masu musun hakan ne, kuma su masu girman kai ne
لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡتَكۡبِرِينَ
Ba shakka, lalle Allah Yana sane da abin da suke voyewa da abin da suke bayyanawa. Lalle Shi ba Ya son masu girman kai
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡۖ فَأَلۡقَوُاْ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعۡمَلُ مِن سُوٓءِۭۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Waxanda mala’iku suke karvar ransu suna masu zaluntar kawunansu; sai suka ba da kai (suna cewa,): “Ba mu kasance muna yin wani mummunan aiki ba.” A’a, ba haka ba ne, lalle Allah Masanin abin da kuka zamanto kuna aikatawa ne
إِنَّمَا قَوۡلُنَا لِشَيۡءٍ إِذَآ أَرَدۡنَٰهُ أَن نَّقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Abin da kawai Muke cewa da abu idan Mun nufe shi, sai Mu ce da shi: “Kasance”, sai kawai ya kasance
ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Waxanda suka yi haquri kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogaro
۞وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓاْ إِلَٰهَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱرۡهَبُونِ
Allah kuma Ya ce: “Kada ku riqi abubuwan bauta guda biyu[1]. Abin bauta Xaya Yake Tilo; to sai ku ji tsoro na Ni kaxai.”
1- Watau kamar Majusawa masu cewa, wai akwai ubangijin alheri shi ne haske, akwai kuma na sharri shi ne duhu.
وَمَا بِكُم مِّن نِّعۡمَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيۡهِ تَجۡـَٔرُونَ
Kuma duk abin da kuke da shi na ni’ima to daga Allah ne; sannan kuma idan cuta ta same ku to wurinsa kuke kai kuka
وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلۡمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيۡهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ
Da kuwa Allah Yana kama mutane da laifukansu ne to da bai bar wata dabba (mai tafiya) a bayanta ba (wato qasa), sai dai kuma Yana saurara musu ne har zuwa wani lokaci qayyadajje. To idan ajalinsu ya zo ba za su jinkirta daidai da sa’a guda ba, kuma ba za su gabata ba
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ
Allah kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke ji
وَٱللَّهُ فَضَّلَ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلرِّزۡقِۚ فَمَا ٱلَّذِينَ فُضِّلُواْ بِرَآدِّي رِزۡقِهِمۡ عَلَىٰ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَهُمۡ فِيهِ سَوَآءٌۚ أَفَبِنِعۡمَةِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ
Allah kuma Ya fifita sashenku a kan wani sashi a arziki. Waxanda aka fifita xin ba za su ba da arzikin nasu ga bayinsu ba don su zama daidai a cikinsa[1]. Shin da ni’imar Allah ne suke jayayya?
1- To me ya sa kafirai suka yarda su sanya wa Allah kishiyoyi daga cikin bayinsa, amma su ba su amince bayinsu su yi tarayya da su a cikin dukiyoyinsu ba?
فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Kada kuma ku sanya wa Allah abokan tarayya. Lalle Allah Yana sane, ku ne ba ku sani ba
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَٰلٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡجِبَالِ أَكۡنَٰنٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ سَرَٰبِيلَ تَقِيكُمُ ٱلۡحَرَّ وَسَرَٰبِيلَ تَقِيكُم بَأۡسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡلِمُونَ
Kuma Allah ne Ya sanya muku inuwoyi daga abin da Ya halitta, Ya kuma sanya muku xakuna daga duwatsu, Ya kuma sanya muku riguna da suke kare ku daga zafi, da kuma riguna (na sulke) da suke kare ku (daga makamai) a fagen daga. Kamar haka ne Yake cika muku ni’imarsa don ku miqa wuya
يَعۡرِفُونَ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Suna sane da ni’imar Allah sannan sai su musanta ta, yawancinsu kuwa kafirai ne
وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ إِذَا عَٰهَدتُّمۡ وَلَا تَنقُضُواْ ٱلۡأَيۡمَٰنَ بَعۡدَ تَوۡكِيدِهَا وَقَدۡ جَعَلۡتُمُ ٱللَّهَ عَلَيۡكُمۡ كَفِيلًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ
Ku kuma cika alqawarin Allah idan kuka xauki alqawari, kada kuma ku warware rantsuwa bayan kun qarfafa ta, alhali kuwa kun sanya Allah shaida a kanku. Lalle Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa
وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَلَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya sanya ku al’umma xaya (masu addini xaya), sai dai kuma Yana vatar da wanda Ya ga dama Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Kuma tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna aikatawa
إِنَّهُۥ لَيۡسَ لَهُۥ سُلۡطَٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Lalle shi (Shaixan) ba shi da iko a kan waxanda suka yi imani kuma suke dogara da Ubangijinsu
مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنۡ أُكۡرِهَ وَقَلۡبُهُۥ مُطۡمَئِنُّۢ بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلۡكُفۡرِ صَدۡرٗا فَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Wanda ya kafirce wa Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta wa alhali kuwa zuciyarsa ta cika da imani, amma kuma wanda ya buxe wa kafirci qirjinsa, to (waxannan) fushin Allah ya tabbata a kansu kuma suna da azaba mai girma
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا فُتِنُواْ ثُمَّ جَٰهَدُواْ وَصَبَرُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ
Sannan lalle Ubangjinka (Mai gafara ne da jin qai) ga waxanda suka yi hijira bayan an fitine su, sannan suka yi jihadi suka kuma yi haquri, lalle Ubangijinka, bayansu (waxannan ayyuka) Mai gafara ne, Mai jin qai
فَكُلُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَٱشۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ
To ku ci halal mai daxi daga abin da Allah Ya arzuta ku da shi, kuma ku gode ni’imomin Allah in kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحۡمَ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۖ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Abin da kawai Ya haramta muku (shi ne) mushe da jini (mai kwarara) da naman alade da kuma abin da aka yanka da (sunan) wanin Allah; amma wanda ya matsu (ya ci) ba yana mai zalunci ko qetare iyaka ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
وَلَا تَقُولُواْ لِمَا تَصِفُ أَلۡسِنَتُكُمُ ٱلۡكَذِبَ هَٰذَا حَلَٰلٞ وَهَٰذَا حَرَامٞ لِّتَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ لَا يُفۡلِحُونَ
Kuma saboda abin da harsunanku suke bayyanawa na qarya kada ku riqa cewa, wannan halal ne, wannan kuma haram ne, don ku yi wa Allah qarya. Lalle waxanda suke qirqira wa Allah qarya ba sa rabauta
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَٰلَةٖ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ وَأَصۡلَحُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٌ
Sannan lalle Ubangijinka (Mai gafara ne) ga waxanda suka aikata mummuna a cikin jahilci sannan suka tuba bayan haka suka kuma gyara, lalle Ubagijinka Mai gafara ne, Mai jin qai