Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 81

وَقُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَزَهَقَ ٱلۡبَٰطِلُۚ إِنَّ ٱلۡبَٰطِلَ كَانَ زَهُوقٗا

Kuma ka ce: “Gaskiya ta zo, varna kuma ta watse. Lalle da ma can ita varna ai watsattsiya ce.”



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 42

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ يَـٰٓأَبَتِ لِمَ تَعۡبُدُ مَا لَا يَسۡمَعُ وَلَا يُبۡصِرُ وَلَا يُغۡنِي عَنكَ شَيۡـٔٗا

Lokacin da ya ce da Babansa: “Ya Babana, me ya sa kake bauta wa abin da ba ya ji ba kuma ya gani, kuma ba ya yi maka maganin komai?



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 81

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لِّيَكُونُواْ لَهُمۡ عِزّٗا

(Kafirai) kuma suka riqi wasu abubuwan bauta ba Allah ba don su zama mataimaka a gare su



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 82

كَلَّاۚ سَيَكۡفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمۡ وَيَكُونُونَ عَلَيۡهِمۡ ضِدًّا

A’a, ba haka ba ne. Ba da daxewa ba za su kafirce wa bautar da suke yi musu, su kuma zama abokan gaba a gare su



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 61

قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ وَيۡلَكُمۡ لَا تَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا فَيُسۡحِتَكُم بِعَذَابٖۖ وَقَدۡ خَابَ مَنِ ٱفۡتَرَىٰ

Musa ya ce da su: “Kaiconku! Kada fa ku qirqira wa Allah qarya, sai Ya hallaka ku da azaba; haqiqa kuwa wanda ya qirqira (masa qarya) to ya tave.”



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 88

فَأَخۡرَجَ لَهُمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٞ فَقَالُواْ هَٰذَآ إِلَٰهُكُمۡ وَإِلَٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِيَ

To sai ya fitar musu da xan maraqi jika-jika mai kuka, sai suka ce[1]: “Wannan ubangijinku ne kuma ubangijin Musa, amma sai ya manta (da yana nan).”


1- Watau wasu fitinannu daga cikin Banu Isra’ila suka faxi wannan magana.


Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 89

أَفَلَا يَرَوۡنَ أَلَّا يَرۡجِعُ إِلَيۡهِمۡ قَوۡلٗا وَلَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا

Yanzu ba sa gani cewa (maraqin) ba ya mayar musu da magana, kuma ba ya mallakar wata cuta ko amfani gare su?



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 18

بَلۡ نَقۡذِفُ بِٱلۡحَقِّ عَلَى ٱلۡبَٰطِلِ فَيَدۡمَغُهُۥ فَإِذَا هُوَ زَاهِقٞۚ وَلَكُمُ ٱلۡوَيۡلُ مِمَّا تَصِفُونَ

A’a, ba haka ba ne, Muna jefa gaskiya a kan qarya, sai ta yi rugu-rugu da ita, sai (ka gan ta) ta vace vat. Kuma tsananin azaba ya tabbata a gare ku saboda abin da kuke siffanta (Shi da shi)[1]


1- Watau na cewa yana da mata ko xa ko abokin tarayya.


Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 21

أَمِ ٱتَّخَذُوٓاْ ءَالِهَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ هُمۡ يُنشِرُونَ

Shin ko sun riqi wasu ababen bauta a nan qasa ne waxanda suke raya matattu?



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 22

لَوۡ كَانَ فِيهِمَآ ءَالِهَةٌ إِلَّا ٱللَّهُ لَفَسَدَتَاۚ فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ رَبِّ ٱلۡعَرۡشِ عَمَّا يَصِفُونَ

Da ya zamana akwai wasu ababen bauta ba Allah ba a cikinsu (wato sammai da qasa), to da sun lalace. Sai dai tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi game da abin da suke siffata (Shi da shi)



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 24

أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ قُلۡ هَاتُواْ بُرۡهَٰنَكُمۡۖ هَٰذَا ذِكۡرُ مَن مَّعِيَ وَذِكۡرُ مَن قَبۡلِيۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ٱلۡحَقَّۖ فَهُم مُّعۡرِضُونَ

Ko kuma sun riqi wasu ababen bauta ne ba Shi ba? Ka ce (da su): “To ku kawo dalilinku (a kan haka). Ga wa’azin waxanda suke tare dani (watau Alqur’ani), ga kuma wa’azin waxanda suka gabace ni (watau littattafan annabawa sai ku duba).” A’a, yawancinsu dai ba sa sanin gaskiya sannan kuma masu bijire (mata) ne



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 25

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٍ إِلَّا نُوحِيٓ إِلَيۡهِ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدُونِ

Kuma ba wani manzo da Muka aiko gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa, babu wani abin bauta da gaskiya sai Ni; to sai ku bauta min[1]


1- Duk manzannin da Allah ya aiko sun zo ne da saqon a bauta wa Allah shi kaxai ba tare da shirka ba.


Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 26

وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۚ بَلۡ عِبَادٞ مُّكۡرَمُونَ

Suka kuma ce wai Allah Ya riqi xa (daga cikin mala’iku)! Tsarki ya tabbata a gare Shi. A’a, su bayi dai ne ababen girmamawa



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 29

۞وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ

Daga cikinsu kuwa duk wanda ya ce: “Ni abin bauta ne ba shi (Allah) ba,” to wannan za Mu saka masa da (wutar) Jahannama. Kamar haka kuwa Muke saka wa azzalumai



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 43

أَمۡ لَهُمۡ ءَالِهَةٞ تَمۡنَعُهُم مِّن دُونِنَاۚ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَ أَنفُسِهِمۡ وَلَا هُم مِّنَّا يُصۡحَبُونَ

Ko kuwa suna da ababen bauta ne da za su kare su (daga azaba) ba Mu ba? Ba za su iya taimakon kansu ba, kuma ba za a kiyaye su (daga azabarmu) ba



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 52

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا هَٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِيٓ أَنتُمۡ لَهَا عَٰكِفُونَ

(Ka tuna) lokacin da ya ce da babansa da kuma jama’arsa: “Mene ne (amfanin) waxannan gumakan da kuka duqufa a bautar su?”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 53

قَالُواْ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَٰبِدِينَ

Suka ce: “Mun sami iyayenmu suna bauta musu ne.”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 54

قَالَ لَقَدۡ كُنتُمۡ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمۡ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

(Ibrahimu) ya ce: “Haqiqa ku da iyayen naku kun tabbata a kan vata bayyananne.”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 65

ثُمَّ نُكِسُواْ عَلَىٰ رُءُوسِهِمۡ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَا هَـٰٓؤُلَآءِ يَنطِقُونَ

Sannan aka juyo da kawunansu (zuwa kafirci) suka ce (da Ibrahimu): “Mun rantse haqiqa ka san cewa su waxannan ba sa magana.”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 66

قَالَ أَفَتَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يَضُرُّكُمۡ

Ya ce: “To yanzu kwa riqa bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amfana muku komai ba kuma ba zai cuce ku ba?



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 98

إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

(Sai a ce da su): “Lallai ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.”



Capítulo: Suratul Anbiya

Verso : 99

لَوۡ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Da waxancan (gumakan) sun kasance alloli (na gaske) da ba su shiga cikinta ba, dukkaninsu kuwa madawwama ne a cikinta



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 12

يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne vata mai nisa



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 13

يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ

Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana



Capítulo: Suratul Hajji

Verso : 62

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

Wannan kuwa saboda lalle Allah Shi ne (abin bauta) na gaskiya, kuma lalle abin da suke bauta wa wanda ba Shi ba shi na qarya ne, kuma lalle Allah Shi ne Maxaukaki, Mai girma



Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 3

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗ لَّا يَخۡلُقُونَ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ وَلَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ ضَرّٗا وَلَا نَفۡعٗا وَلَا يَمۡلِكُونَ مَوۡتٗا وَلَا حَيَوٰةٗ وَلَا نُشُورٗا

Kuma suka riqi ababen bauta ba Shi ba, ba sa halittar komai, alhali kuwa su ake halittawa, kuma ba sa mallakar cuta ko amfani ga kawunansu, ba sa kuma mallakar kashewa ko rayawa ko tashi (bayan mutuwa)



Capítulo: Suratul Furqan

Verso : 43

أَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ أَفَأَنتَ تَكُونُ عَلَيۡهِ وَكِيلًا

Shin ka ga wanda ya mayar da son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, to yanzu kai za ka zama mai kiyaye shi (daga bin son zuciyarsa)?



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 38

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ مَا عَلِمۡتُ لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرِي فَأَوۡقِدۡ لِي يَٰهَٰمَٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجۡعَل لِّي صَرۡحٗا لَّعَلِّيٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّي لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Fir’auna kuma ya ce: “Ya ku manyan gari, ban san kuna da wani abin bauta ba in ba ni ba, kai ko Hamana, shirya min qonannen tavo sannan ka yi min dogon gini don in hango abin bautar Musa, lalle ni ina tsammanin cewa shi yana cikin maqaryata.”



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 62

وَيَوۡمَ يُنَادِيهِمۡ فَيَقُولُ أَيۡنَ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ كُنتُمۡ تَزۡعُمُونَ

Kuma ka tuna ranar da (Allah) zai kirawo su sai Ya ce: “Ina abokan tarayyar nawa waxanda kuka kasance kuna riyawa?”



Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 63

قَالَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ ٱلَّذِينَ أَغۡوَيۡنَآ أَغۡوَيۡنَٰهُمۡ كَمَا غَوَيۡنَاۖ تَبَرَّأۡنَآ إِلَيۡكَۖ مَا كَانُوٓاْ إِيَّانَا يَعۡبُدُونَ

Sai waxanda alqawarin Allah (na azaba) ya tabbata a kansu su ce: “Ya Ubangijinmu, waxannan da muka vatar, mun vatar da su ne kamar yadda mu ma muka vata; ba ruwanmu da kowa sai kai; don kuwa ba su kasance mu suke bauta wa ba.”