Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 155

وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَيۡءٖ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٰلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٰتِۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّـٰبِرِينَ

Kuma lalle za Mu jarrabe ku da wani abin tsoro da yunwa da tawayar dukiya da ta rayuka da ta ‘ya’yan itatuwa. Don haka ka yi albishir ga masu haquri



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 156

ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٞ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٰجِعُونَ

(Su ne) waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: “Lalle mu na Allah ne, kuma lalle mu gare Shi muke komawa.”



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 214

أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تَدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ وَلَمَّا يَأۡتِكُم مَّثَلُ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۖ مَّسَّتۡهُمُ ٱلۡبَأۡسَآءُ وَٱلضَّرَّآءُ وَزُلۡزِلُواْ حَتَّىٰ يَقُولَ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ مَتَىٰ نَصۡرُ ٱللَّهِۗ أَلَآ إِنَّ نَصۡرَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ

Shin kun yi tsammanin za ku shiga Aljanna ne, alhalin misalin irin abin da ya shafi waxanda suka shuxe gabaninku bai zo muku ba? Tsananin talauci da cuta sun shafe su; kuma an girgiza su sosai, har Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi suka riqa cewa: “Yaushe ne nasarar Allah za ta zo?” Ku saurara, lalle nasarar Allah a kusa take



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 249

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

To yayin da Xalutu ya fita (bayan gari) da rundunarsa, sai ya ce: “Lalle Allah zai jarrabe ku da wata qorama, to duk wanda ya sha daga gare ta, to ba ya tare da ni, duk wanda kuwa bai sha ba, to wannan yana tare da ni, sai dai wanda ya kamfata sau xaya da (tafin) hannunsa.” Gaba xayansu sai suka sha daga cikinta sai ‘yan kaxan daga cikinsu (su ne ba su sha ba). To yayin da ya qetare shi, shi da waxanda suka yi imani tare da shi, sai suka ce: “A yau kam ba mu da iko wajen fuskantar Jalutu da rundunarsa.” Sai waxanda suke da yaqinin cewa za su haxu da Allah suka ce: “Sau da yawa wata runduna ‘yan kaxan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da izinin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haquri.”



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 152

وَلَقَدۡ صَدَقَكُمُ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥٓ إِذۡ تَحُسُّونَهُم بِإِذۡنِهِۦۖ حَتَّىٰٓ إِذَا فَشِلۡتُمۡ وَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَعَصَيۡتُم مِّنۢ بَعۡدِ مَآ أَرَىٰكُم مَّا تُحِبُّونَۚ مِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلدُّنۡيَا وَمِنكُم مَّن يُرِيدُ ٱلۡأٓخِرَةَۚ ثُمَّ صَرَفَكُمۡ عَنۡهُمۡ لِيَبۡتَلِيَكُمۡۖ وَلَقَدۡ عَفَا عَنكُمۡۗ وَٱللَّهُ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma tabbas haqiqa Allah Ya cika muku alqawarinsa yayin da kuka riqa kisan su da yawa da izininsa; har zuwa lokacin da kuka yi rauni, kuma kuka yi jayayya a cikin umarnin (Manzo), kuma daga qarshe kuka sava bayan (Allah) Ya nuna muku irin abin da kuke so. Cikinku akwai waxanda suke nufin duniya, kuma cikinku akwai waxanda suke nufin lahira. Sannan sai Ya kautar da ku kuka bar su don ya jarrabe ku; kuma tabbas haqiqa Allah Ya yi muku afuwa. Kuma Allah Ma’abocin falala ne ga muminai



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 179

مَّا كَانَ ٱللَّهُ لِيَذَرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ عَلَىٰ مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ حَتَّىٰ يَمِيزَ ٱلۡخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُطۡلِعَكُمۡ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَجۡتَبِي مِن رُّسُلِهِۦ مَن يَشَآءُۖ فَـَٔامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۚ وَإِن تُؤۡمِنُواْ وَتَتَّقُواْ فَلَكُمۡ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Da xai Allah ba zai qyale muminai a yadda kuke xin nan ba har sai Ya rarrabe tsakanin lalatacce da kyakkyawa. Kuma Allah ba zai sanar da ku gaibu ba, sai dai Allah Yana zavar wanda Ya so cikin manzanninsa ne; don haka ku yi imani da Allah da manzanninsa. Idan kun yi imani, kun yi taqawa kuwa, to kuna da lada mai girma



Capítulo: Suratu Ali-Imran

Verso : 186

۞لَتُبۡلَوُنَّ فِيٓ أَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡ وَلَتَسۡمَعُنَّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُوٓاْ أَذٗى كَثِيرٗاۚ وَإِن تَصۡبِرُواْ وَتَتَّقُواْ فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

Lalle za a jarrabe ku a cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma lalle za ku riqa jin cutarwa mai yawa daga waxanda aka bai wa Littafi kafinku, haka kuma daga waxanda suke mushirikai. Amma idan har kuka yi haquri, kuma kuka tsare dokar Allah, to lalle wannan yana daga cikin manyan al’amura



Capítulo: Suratul An’am

Verso : 165

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ ٱلۡأَرۡضِ وَرَفَعَ بَعۡضَكُمۡ فَوۡقَ بَعۡضٖ دَرَجَٰتٖ لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۗ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ ٱلۡعِقَابِ وَإِنَّهُۥ لَغَفُورٞ رَّحِيمُۢ

“Kuma Shi ne Ya sanya ku halifofi a bayan qasa, kuma Ya xaukaka darajar wasunku a kan wasu, don Ya jarrabe ku game da abin da Ya ba ku. Lalle Ubangijinka Mai gaggawar uquba ne, kuma lalle Shi tabbas Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai.”



Capítulo: Suratul Anfal

Verso : 17

فَلَمۡ تَقۡتُلُوهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ قَتَلَهُمۡۚ وَمَا رَمَيۡتَ إِذۡ رَمَيۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ وَلِيُبۡلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡهُ بَلَآءً حَسَنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Saboda haka ba ku kuka kashe su ba, Allah ne Ya kashe su[1]. Kuma ba ka jefa ba lokacin da ka jefa, sai dai Allah ne Ya jefa[2]. Don kuma Ya jarrabi muminai da kyakkyawar jarrabawa[3]. Lalle Allah Mai ji ne Masani


1- Domin komai ya faru ne da taimakonsa da agajinsa.


2- Watau shi ma Annabi () da ya xauki qasa da tafin hannunsa ya watsa ta a fuskokin kafirai ta kuma cika musu ido, to a haqiqa ba shi ne ya yi wannan jifan ba, Allah ne ya yi.


3- Domin su yi masa godiya a kan ni’imominsa.


Capítulo: Suratu Hud

Verso : 7

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ وَكَانَ عَرۡشُهُۥ عَلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۗ وَلَئِن قُلۡتَ إِنَّكُم مَّبۡعُوثُونَ مِنۢ بَعۡدِ ٱلۡمَوۡتِ لَيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Shi ne kuma wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, Al’arshinsa kuwa ya kasance a kan ruwa, don Ya jarraba ku a cikinku wa ya fi kyakkyawan aiki. Kuma tabbas idan ka ce (da su): “Lalle za a tashe ku bayan mutuwa,” tabbas kafirai za su ce: “Ai wannan ba wani abu ba ne sai tsafi mabayyani.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 2

أَحَسِبَ ٱلنَّاسُ أَن يُتۡرَكُوٓاْ أَن يَقُولُوٓاْ ءَامَنَّا وَهُمۡ لَا يُفۡتَنُونَ

Yanzu mutane suna tsammanin za a qyale su ne saboda suna cewa: “Mun yi imani,” kuma ba za a fitine su ba?



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 3

وَلَقَدۡ فَتَنَّا ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۖ فَلَيَعۡلَمَنَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ وَلَيَعۡلَمَنَّ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Haqiqa kuwa Mun fitini waxanda suke gabaninsu; to tabbas kuwa Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, lalle kuma zai bayyana maqaryata



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 11

هُنَالِكَ ٱبۡتُلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَزُلۡزِلُواْ زِلۡزَالٗا شَدِيدٗا

A nan ne fa aka jarrabi muminai, aka kuma girgiza su girgizawa mai tsanani



Capítulo: Suratu Muhammad

Verso : 31

وَلَنَبۡلُوَنَّكُمۡ حَتَّىٰ نَعۡلَمَ ٱلۡمُجَٰهِدِينَ مِنكُمۡ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَنَبۡلُوَاْ أَخۡبَارَكُمۡ

Kuma tabbas za Mu jarraba ku har sai Mun bayyana masu jihadi daga cikinku, da masu haquri, kuma za Mu bayyana halayenku



Capítulo: Suratut Taghabun

Verso : 15

إِنَّمَآ أَمۡوَٰلُكُمۡ وَأَوۡلَٰدُكُمۡ فِتۡنَةٞۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne kawai (a gare ku). Kuma a wurin Allah lada mai girma yake



Capítulo: Suratul Mulk

Verso : 2

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ

Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara