أَوۡ يُصۡبِحَ مَآؤُهَا غَوۡرٗا فَلَن تَسۡتَطِيعَ لَهُۥ طَلَبٗا
“Ko kuma ruwanta ya zama ya qafe qarqaf, ba ko za ka sami hanyar samo shi ba.”
وَأُحِيطَ بِثَمَرِهِۦ فَأَصۡبَحَ يُقَلِّبُ كَفَّيۡهِ عَلَىٰ مَآ أَنفَقَ فِيهَا وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُشۡرِكۡ بِرَبِّيٓ أَحَدٗا
Aka kuwa hallaka ‘ya’yan itacen nasa, sannan ya wayi gari yana tafa hannayensa kan irin abin da ya vatar a kanta, ita kuwa ga ta ta zubo a kan dirkokinta, yana kuma cewa: “Kaicona, ina ma ban haxa wani da Ubangijina ba!”
وَلَمۡ تَكُن لَّهُۥ فِئَةٞ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مُنتَصِرًا
Ba shi kuwa da wata qungiya da za ta taimake shi ban da Allah, kuma bai zamo mai taimaka wa (kansa) ba
هُنَالِكَ ٱلۡوَلَٰيَةُ لِلَّهِ ٱلۡحَقِّۚ هُوَ خَيۡرٞ ثَوَابٗا وَخَيۡرٌ عُقۡبٗا
A wannan lokacin ne (ya bayyana) cewa taimako na Allah ne Tabbataccen (Sarki). Shi ne Fiyayyen Mai ba da lada kuma Fiyayyen Mai kyautata qarshe
۞إِنَّ قَٰرُونَ كَانَ مِن قَوۡمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيۡهِمۡۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلۡعُصۡبَةِ أُوْلِي ٱلۡقُوَّةِ إِذۡ قَالَ لَهُۥ قَوۡمُهُۥ لَا تَفۡرَحۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَرِحِينَ
Lalle Qaruna yana daga mutanen Musa, sai ya yi musu girman kai, Muka kuma ba shi taskokin (dukiya) wadda lalle makullansu suna yi wa tarin jama’a qarfafa nauyin (xauka), yayin da mutanensa suka ce da shi: “Kada ka yi fariya, lalle Allah ba Ya son masu fariya
وَٱبۡتَغِ فِيمَآ ءَاتَىٰكَ ٱللَّهُ ٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَۖ وَلَا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ ٱلدُّنۡيَاۖ وَأَحۡسِن كَمَآ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ وَلَا تَبۡغِ ٱلۡفَسَادَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
“Kuma ka nemi gidan lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka; kada kuma ka manta rabonka na duniya; kuma ka kyautata kamar yadda Allah Ya kyautata maka, kada kuma ka nemi yin varna a bayan qasa. Lalle Allah ba Ya son masu varna.”
قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمٍ عِندِيٓۚ أَوَلَمۡ يَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَهۡلَكَ مِن قَبۡلِهِۦ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مَنۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرُ جَمۡعٗاۚ وَلَا يُسۡـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Ya ce: “Ai ni an ba ni ita (wato dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne.” Shin yanzu bai sani ba ne cewa haqiqa Allah Ya hallaka wasu al’ummun da suke a gabaninsa waxanda suka fi shi qarfi da kuma yawan tarin (dukiya)? Ba kuwa za a tambayi masu laifi game da laifinsu ba[1]
1- Watau zai hallaka su kawai ba tare da tsayawa a yi musu tambayoyi a kan laifukansu ba, ballantana a saurari hanzarinsu.
فَخَرَجَ عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ فِي زِينَتِهِۦۖ قَالَ ٱلَّذِينَ يُرِيدُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا يَٰلَيۡتَ لَنَا مِثۡلَ مَآ أُوتِيَ قَٰرُونُ إِنَّهُۥ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٖ
Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa; sai waxanda suke burin rayuwar duniya suka ce: “Ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa Qaruna? Lalle shi mai babban rabo ne.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَيۡلَكُمۡ ثَوَابُ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّمَنۡ ءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗاۚ وَلَا يُلَقَّىٰهَآ إِلَّا ٱلصَّـٰبِرُونَ
Waxanda kuwa aka bai wa ilimi sai suka ce: “Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya yi imani, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu haquri.”
فَخَسَفۡنَا بِهِۦ وَبِدَارِهِ ٱلۡأَرۡضَ فَمَا كَانَ لَهُۥ مِن فِئَةٖ يَنصُرُونَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُنتَصِرِينَ
Sannan muka kifar da shi (Qaruna) tare da gidansa cikin qasa, kuma ba shi da wata jama’a da za su taimake shi ba Allah ba, kuma bai kasance daga masu taimaka wa kawunansu ba
وَأَصۡبَحَ ٱلَّذِينَ تَمَنَّوۡاْ مَكَانَهُۥ بِٱلۡأَمۡسِ يَقُولُونَ وَيۡكَأَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ وَيَقۡدِرُۖ لَوۡلَآ أَن مَّنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا لَخَسَفَ بِنَاۖ وَيۡكَأَنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Kuma waxanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa: “Wai, yau mun ga abin al’ajabi! Allah Yana yalwata arziki ga wanda Ya ga dama daga bayinsa, Yana kuma quntatawa ga wanda Ya ga dama; ba don Allah Ya ba mu sa’a ba da mu ma Ya kifar da mu. Wai, abin mamaki, lalle kafurai ba sa rabauta!”
وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلًا أَصۡحَٰبَ ٱلۡقَرۡيَةِ إِذۡ جَآءَهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Kuma ka ba su misali da mutanen wata alqarya lokacin da manzannin suka zo mata
إِذۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱثۡنَيۡنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزۡنَا بِثَالِثٖ فَقَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَيۡكُم مُّرۡسَلُونَ
A yayin da Muka aika musu (manzanni) biyu sai suka qaryata su, sannan Muka qarfafe su da na uku, sai suka ce: “Lalle mu manzanni ne zuwa gare ku.”
قَالُواْ مَآ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَمَآ أَنزَلَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَكۡذِبُونَ
Suka ce: “Ku ai ba kowa ba ne face mutane kamarmu, kuma (Allah) Mai rahama bai saukar da komai ba, ku dai ba abin da kuke yi sai qarya.”
قَالُواْ رَبُّنَا يَعۡلَمُ إِنَّآ إِلَيۡكُمۡ لَمُرۡسَلُونَ
Suka ce: “Ubangijinmu Yana sane da cewa mu lalle tabbas manzanni ne zuwa gare ku
وَمَا عَلَيۡنَآ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
“Kuma babu wani abu a kanmu sai isar da aike bayyananne.”
قَالُوٓاْ إِنَّا تَطَيَّرۡنَا بِكُمۡۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهُواْ لَنَرۡجُمَنَّكُمۡ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Suka ce: “Mu dai lalle mun camfa ku, tabbas idan ba ku bari ba to za mu jefe ku, kuma tabbas za ku gamu da azaba mai raxaxi daga gare mu.”
قَالُواْ طَـٰٓئِرُكُم مَّعَكُمۡ أَئِن ذُكِّرۡتُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ مُّسۡرِفُونَ
Suka ce: “Camfinku ya qare a kanku. Yanzu don an yi muku gargaxi ne (za ku faxi haka?) A’a, ku dai mutane ne mavarnata.”
وَجَآءَ مِنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ رَجُلٞ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُواْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Wani mutum kuma ya zo daga can qarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waxannan manzannin
ٱتَّبِعُواْ مَن لَّا يَسۡـَٔلُكُمۡ أَجۡرٗا وَهُم مُّهۡتَدُونَ
“Ku bi waxanda ba sa tambayar ku wani lada, ga su kuma shiryayyu
وَمَالِيَ لَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
“Ni kuma me zai hana ni in bauta wa wanda Ya halicce ni, kuma gare Shi ne za a komar da ku?
ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ
“Yanzu na riqi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?
إِنِّيٓ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
“Lalle ni idan na yi haka to tabbas na zama cikin vata mabayyani
إِنِّيٓ ءَامَنتُ بِرَبِّكُمۡ فَٱسۡمَعُونِ
“Lalle ni na yi imani da Ubangijinku, sai ku saurare ni.”
قِيلَ ٱدۡخُلِ ٱلۡجَنَّةَۖ قَالَ يَٰلَيۡتَ قَوۡمِي يَعۡلَمُونَ
Aka ce (da shi): “Shiga Aljanna.” Ya ce: “Kaicon mutanena, ina ma da suna sane?
بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
“Da gafarar da Ubangijina Ya yi min, Ya kuma sanya ni cikin waxanda aka karrama?”
۞وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِن جُندٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ
Ba Mu kuma saukar da wata runduna (ta mala’iku) a kan mutanensa daga sama ba a bayansa, ba Mu kuma saba saukarwa ba
إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ خَٰمِدُونَ
Ba abin da ya kasance sai tsawa guda xaya, sai ga su matattu
يَٰحَسۡرَةً عَلَى ٱلۡعِبَادِۚ مَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Nadama ta tabbata ga bayi (masu qaryatawa), ba wani manzo da zai zo musu sai sun zamanto suna yi masa izgili
أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ أَنَّهُمۡ إِلَيۡهِمۡ لَا يَرۡجِعُونَ
Shin ba sa gani ne, al’ummu nawa ne Muka hallaka kafin su, cewa lalle kuwa ba sa dawowa zuwa gare su?