وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ أَن يُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ وَسَعَىٰ فِي خَرَابِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ مَا كَانَ لَهُمۡ أَن يَدۡخُلُوهَآ إِلَّا خَآئِفِينَۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Wane ne mafi zalunci kamar wanda ya hana masallatan Allah a riqa ambaton sunansa a cikinsu, ya yi ta qoqari wajen rushe su? Waxannan bai kamata su shige su ba sai a cikin halin tsoro. Za su gamu da wulaqanci a duniya a lahira kuma suna da wata azaba mai girma
أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Ko kuma kuna cewa ne, “Lalle Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki sun kasance Yahudawa ne ko Nasara?” Ka ce: “Ku ne kuka fi sani ko kuma Allah?” Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya voye shaidar da take wajensa daga Allah, kuma Allah ba rafkananne ne ba game da abin da kuke aikatawa
وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ وَتُدۡلُواْ بِهَآ إِلَى ٱلۡحُكَّامِ لِتَأۡكُلُواْ فَرِيقٗا مِّنۡ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ بِٱلۡإِثۡمِ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, haka kuma kada ku miqa dukiyoyinku zuwa ga masu shari’a, don kawai ku ci wani vangare na dukiyar mutane ta hanyar savo, alhali kuna sane
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَيَقۡتُلُونَ ٱلَّذِينَ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡقِسۡطِ مِنَ ٱلنَّاسِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
Lalle waxanda suke kafirce wa ayoyin Allah, kuma suke kashe annabawa ba tare da wani haqqi ba, kuma suke kashe waxanda suke yin umarni da adalci cikin mutane, to ka yi musu albishir da wata azaba mai raxaxi
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۗ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعَٰلَمِينَ
Waxannan ayoyin Allah ne Muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai
وَلۡيَخۡشَ ٱلَّذِينَ لَوۡ تَرَكُواْ مِنۡ خَلۡفِهِمۡ ذُرِّيَّةٗ ضِعَٰفًا خَافُواْ عَلَيۡهِمۡ فَلۡيَتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡيَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدًا
Waxanda suke jin tsoron za su mutu su bar ‘ya’ya raunana a bayansu, suna kuma jin tsoron a zalunce su, to su kiyaye dokokin Allah, kuma su faxi magana ta daidai
إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا
Lalle waxanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci, wuta ce kawai suke ci a cikkunansu; kuma da sannu za su shiga wuta mai tsananin quna
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne
وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ عُدۡوَٰنٗا وَظُلۡمٗا فَسَوۡفَ نُصۡلِيهِ نَارٗاۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرًا
Kuma duk wanda ya aikata haka don qetare iyaka da zalunci, to za Mu shigar da shi cikin wata wuta; kuma yin haka ya kasance abu ne mai sauqi a wurin Allah
وَأَخۡذِهِمُ ٱلرِّبَوٰاْ وَقَدۡ نُهُواْ عَنۡهُ وَأَكۡلِهِمۡ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِۚ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ مِنۡهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Da kuma cin riba da suke yi, tare da cewa an hana su cin ta, da kuma yadda suke cin dukiyar mutane ta hanyar cuta, Mun kuwa yi tanadin azaba mai raxaxi ga kafirai daga cikinsu
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Kuma ba mafi zalunci fiye da wanda ya qirqiri qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya qaryata ayoyinsa. Haqiqar lamarin dai su azzalumai ba za su tava rabauta ba
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ قَالَ أُوحِيَ إِلَيَّ وَلَمۡ يُوحَ إِلَيۡهِ شَيۡءٞ وَمَن قَالَ سَأُنزِلُ مِثۡلَ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۗ وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلظَّـٰلِمُونَ فِي غَمَرَٰتِ ٱلۡمَوۡتِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ بَاسِطُوٓاْ أَيۡدِيهِمۡ أَخۡرِجُوٓاْ أَنفُسَكُمُۖ ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ غَيۡرَ ٱلۡحَقِّ وَكُنتُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهِۦ تَسۡتَكۡبِرُونَ
Kuma wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qagi qarya ya jingina wa Allah, ko kuma ya ce: “An yiwo mini wahayi,” alhalin kuma ba a yi masa wahayin komai ba, da kuma wanda ya ce: “Zan saukar da irin abin da Allah Ya saukar?” Kuma da za ka ga lokacin da kafirai suke cikin magagin mutuwa, mala’iku kuma suna miqa hannayensu suna cewa: “Ku fito da rayukanku (da kanku), a yau ne za a saka muku da azabar wulaqanci, saboda irin abin da kuke faxa game da Allah wanda ba gaskiya ba, kuma kun kasance kuna girman kai game da ayoyinsa.”
وَمِنَ ٱلۡإِبِلِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ وَصَّىٰكُمُ ٱللَّهُ بِهَٰذَاۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا لِّيُضِلَّ ٱلنَّاسَ بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Haka kuma raquma akwai jinsi biyu, daga cikin shanu ma akwai jinsi biyu. Ka ce: “Shin mazan guda biyu Ya haramta ko matan biyu ko kuma abin da yake cikin mahaifar matan biyu ya haramta ko kuma kun zama shaidu yayin da Allah Ya yi muku wasicci da wannan abin?” To ba wanda ya fi zaluntar kansa fiye da wanda ya qirqiri qarya, ya jingina wa Allah don ya vatar da mutane ba tare da ilimi ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
أَوۡ تَقُولُواْ لَوۡ أَنَّآ أُنزِلَ عَلَيۡنَا ٱلۡكِتَٰبُ لَكُنَّآ أَهۡدَىٰ مِنۡهُمۡۚ فَقَدۡ جَآءَكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَصَدَفَ عَنۡهَاۗ سَنَجۡزِي ٱلَّذِينَ يَصۡدِفُونَ عَنۡ ءَايَٰتِنَا سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يَصۡدِفُونَ
Ko kuma ku ce: “In da mu aka saukar wa da littafin, to da lalle mun fi su shiryuwa.” To ai haqiqa hujja ta riga ta zo muku daga Ubangijinku, da kuma shiriya da rahama; don haka babu wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya qaryata ayoyin Allah, kuma ya yi watsi da su. Da sannu za Mu saka wa waxanda suke bijire wa ayoyinmu da mummunar azaba, saboda bijirewar da suke yi
۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلۡأَحۡبَارِ وَٱلرُّهۡبَانِ لَيَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلنَّاسِ بِٱلۡبَٰطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۗ وَٱلَّذِينَ يَكۡنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلۡفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٖ
Ya ku waxanda suka yi imani, lalle da yawa daga malaman (Yahudawa) da masu ibada (Nasara) tabbas suna cin dukiyoyin mutane ta hanyar cuta, suna kuma toshe hanyar Allah. Waxanda kuma suke voye zinariya da azurfa ba sa ciyar da ita saboda Allah[1], to ka yi musu albishir da wata azaba mai raxaxi
1- Watau ba sa fitar da zakka daga dukiyarsu.
إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ ٱلنَّاسَ شَيۡـٔٗا وَلَٰكِنَّ ٱلنَّاسَ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ
Lalle Allah ba Ya zaluntar mutane da komai, sai dai mutane kawunansu kawai suke zalunta
۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا
Kuma dukkanin fuskoki suka qasqanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haqiqa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya tave
وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا
Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma qwauro
وَجَحَدُواْ بِهَا وَٱسۡتَيۡقَنَتۡهَآ أَنفُسُهُمۡ ظُلۡمٗا وَعُلُوّٗاۚ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ
Suka kuma musanta su don zalunci da girman kai, alhali kuwa zukatansu sun sakankance da su[1]. To sai ka duba ka ga yadda qarshen mavarnata ya kasance
1- Watau a zukatansu sun san gaskiya ce, su kuma a kan qarya suke, amma son zuciya ya hana su su sallama.
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِٱلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُۥٓۚ أَلَيۡسَ فِي جَهَنَّمَ مَثۡوٗى لِّلۡكَٰفِرِينَ
Wane ne ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya ko kuma ya qaryata gaskiya lokacin da ta zo masa? Yanzu ashe babu mazaunar kafirai a cikin Jahannama?
وَإِذۡ قَالَ لُقۡمَٰنُ لِٱبۡنِهِۦ وَهُوَ يَعِظُهُۥ يَٰبُنَيَّ لَا تُشۡرِكۡ بِٱللَّهِۖ إِنَّ ٱلشِّرۡكَ لَظُلۡمٌ عَظِيمٞ
Kuma (ka tuna) lokacin da Luqumanu ya ce da xansa a yayin da yake yi masa wa’azi: “Ya kai xanxana, kada ka yi shirka da Allah; lalle ita shirka zalunci ne mai girma
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ ثُمَّ أَعۡرَضَ عَنۡهَآۚ إِنَّا مِنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُنتَقِمُونَ
Wane ne kuma mafi zalunci fiye da wanda aka yi wa wa’azi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu? Lalle Mu Masu saka wa masu manyan laifuka ne
ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
A wannan ranar za a saka wa kowane rai da irin abin da ya aikata. Babu zalunci a wannan ranar. Lalle Allah Mai gaggawar yin hisabi ne
إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَظۡلِمُونَ ٱلنَّاسَ وَيَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Laifi kam yana kan waxanda suke zaluntar mutane ne suke kuma yin ta’adda a bayan qasa ba da wata hujja ba. Waxannan suna da azaba mai raxaxi
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُوَ يُدۡعَىٰٓ إِلَى ٱلۡإِسۡلَٰمِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Ba wanda kuma ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya, alhali kuwa shi ana kiran sa zuwa Musulunci. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai