Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 228

وَٱلۡمُطَلَّقَٰتُ يَتَرَبَّصۡنَ بِأَنفُسِهِنَّ ثَلَٰثَةَ قُرُوٓءٖۚ وَلَا يَحِلُّ لَهُنَّ أَن يَكۡتُمۡنَ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِيٓ أَرۡحَامِهِنَّ إِن كُنَّ يُؤۡمِنَّ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِي ذَٰلِكَ إِنۡ أَرَادُوٓاْ إِصۡلَٰحٗاۚ وَلَهُنَّ مِثۡلُ ٱلَّذِي عَلَيۡهِنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ وَلِلرِّجَالِ عَلَيۡهِنَّ دَرَجَةٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ

Kuma mata waxanda aka saki za su dakatar da kawunansu (tsawon) qur’i[1] uku, kuma ba ya halatta a gare su su voye abin da Allah Ya halitta a cikin mahaifarsu, in sun kasance suna yin imani da Allah da ranar qarshe; kuma mazajensu su suka fi cancantar dawo da su a cikin wancan lokaci in sun yi nufin sulhu[2]; kuma su (mata) suna da haqqi kwatankwacin irin wanda yake kansu ta hanyar da aka sani, kuma mazaje suna da fifiko a kansu. Allah Kuma Mabuwayi ne, Mai hikima


1- Qur’i a Larabci yana nufin ‘haila’ ko ‘tsarki’, A ra’ayin manyan sahabbai, har da Halifofi huxu da wasu tabi’ai, sun ce, ana nufin ‘jinin haila’. Watau iddar wadda aka saki tana qare wa da xaukewar jinin al’adar ta ta uku bayan sakin.


2- Mijin da ya saki matarsa saki na farko, ko na biyu, zai iya dawo da ita matuqar suna son su ci gaba da zama da juna cikin mutuntawa da kyautatawa.


Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 231

وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ سَرِّحُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖۚ وَلَا تُمۡسِكُوهُنَّ ضِرَارٗا لِّتَعۡتَدُواْۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗاۚ وَٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَمَآ أَنزَلَ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَٱلۡحِكۡمَةِ يَعِظُكُم بِهِۦۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Kuma idan kuka saki mata, sai wa’adin iddarsu ya kusa, (idan kuna son su) sai ku riqe su ta hanyar da ta dace (a shari’ance) ko kuma ku qyale su ta hanyar da ta dace (a shari’ance); kuma kada ku riqe su da nufin cutarwa don ku qetare iyakar (Ubangiji). Duk wanda ya aikata haka kuwa, to haqiqa ya zalunci kansa. Kuma kada ku mayar da ayoyin Allah abin izgili, kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku da abin da Ya saukar muku na Littafi da Hikima Yana yi muku wa’azi da shi. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku sani lalle Allah Masanin komai ne



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 232

وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحۡنَ أَزۡوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوۡاْ بَيۡنَهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ ذَٰلِكُمۡ أَزۡكَىٰ لَكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Kuma idan kun saki mata sai suka cika wa’adin iddarsu, to (ku waliyyai) kada ku hana su su auri mazajensu (na da) idan sun yi yarjejeniya a tsakaninsu ta hanyar da ta dace (a shari’a). Wannan (abin da aka ambata) shi ne wanda ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance daga cikinku, yana imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne abin da ya fi alheri a gare ku kuma ya fi tsarki; kuma Allah Shi ne Yake da sani, ku ba ku sani ba



Capítulo: Suratul Baqara

Verso : 235

وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِيمَا عَرَّضۡتُم بِهِۦ مِنۡ خِطۡبَةِ ٱلنِّسَآءِ أَوۡ أَكۡنَنتُمۡ فِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ سَتَذۡكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِن لَّا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّآ أَن تَقُولُواْ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗاۚ وَلَا تَعۡزِمُواْ عُقۡدَةَ ٱلنِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡكِتَٰبُ أَجَلَهُۥۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِيٓ أَنفُسِكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Kuma babu laifi a kanku game da abin da kuka yi wa mata jirwaye da shi na neman aurensu ko kuma kuka voye a cikin zukatanku, Allah Ya san cewa ku za ku riqa maganarsu, sai dai kar ku yi alqawari da su (na aure) a asirce, sai dai in za ku faxi zance wanda yake sananne a (shari’a). Kuma kada ku qulla igiyar aure (da mata masu takaba) har sai faralin idda ya cika wa’adinsa. Kuma ku sani lalle Allah Ya san abin da yake cikin zukatanku, don haka ku kiyaye Shi. Kuma ku sani lalle Allah Mai yawan gafara ne, Mai haquri



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 49

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَيۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةٖ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka auri mata muminai, sannan kuka sake su tun kafin ku sadu da su, to babu wata idda taku a kansu da za ku nemi cikar adadin (kwanakinta); sai ku jiyar da su daxi[1], kuma ku sake su kyakkyawan saki


1- Watau su ba su abin da zai daxaxa musu rai, don ya rage musu raxaxin sakin da aka yi musu.


Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا

Ya kai wannan Annabi, (ka ce da jama’arka): “Idan za ku saki mata sai ku sake su a farkon iddarsu[1], kuma ku kula da kiyaye qidaya idda[2]; kuma ku kiyaye dokokin Ubangijinku; kada ku fitar da su daga xakunansu, su ma kada su fita sai dai idan sun aikata alfasha bayayyananna. Waxannan kuwa su ne iyakokin Allah. Wanda kuwa duk ya qetare iyakokin Allah, to haqiqa ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ko Allah zai farar da wani al’amari bayan wannan[3]


1- Watau lokacin da suka yi tsarkin haila wanda kuma ba su sadu da su ba a cikinsa, ko kuma idan ciki ya bayyana.


2- Domin su iya dawo da matansu kafin qarewarta idan suna buqatar yin haka.


3- Watau Allah ya sake kawo jituwa a tsakanin mijin da matar su fahimci juna su mayar da aurensu.


Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 2

فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا

Idan kuma sun kusa isa qarshen iddarsu, to ku riqe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita



Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 3

وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا

Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu



Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 4

وَٱلَّـٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّـٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا

Waxanda kuma suka xebe qauna ta yin al’ada daga matanku, idan kun yi kokwanto, to iddarsu wata uku ne, da kuma waxanda ba su tava yin al’ada ba. Mata masu ciki kuma qarewar iddarsu ita ce haife cikinsu[1]. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai sanya masa sauqi game da al’amarinsa


1- Hakanan iddar matar da mijinta ya rasu.


Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 5

ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا

Wannan shi ne hukuncin Allah da Ya saukar da shi a gare ku. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai kankare masa zunubbansa Ya kuma girmama masa lada



Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 6

أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ

Ku zaunar da su (matayen) a inda kuka zauna daidai da samunku, kada kuma ku cuce su don ku quntata musu. Idan kuwa sun kasance masu ciki to sai ku ciyar da su har sai sun haife cikinsu. Sannan idan sun shayar muku da (‘ya’yanku) sai ku ba su ladansu; ku kuma daidaita a tsakaninku ta hanya tagari; idan kuma kuka kasa daidaitawa, to wata mai shayarwar sai ta shayar masa



Capítulo: Suratux Xalaq

Verso : 7

لِيُنفِقۡ ذُو سَعَةٖ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡيُنفِقۡ مِمَّآ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَآ ءَاتَىٰهَاۚ سَيَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرٖ يُسۡرٗا

Mawadaci ya ciyar daidai da wadatarsa; wanda kuwa aka quntata masa arzikinsa, to ya ciyar daidai da abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya xora wa rai sai gwargwadon abin da Ya ba shi. Kuma da sannu Allah zai sanya sauqi bayan tsanani