Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 1

حمٓ

HA MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ

Saukar da Alqur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 3

مَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَمَّآ أُنذِرُواْ مُعۡرِضُونَ

Ba Mu halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu ba sai don gaskiya da kuma (zuwa) wani lokaci qayyadajje. Waxanda kuwa suka kafirta masu bijire wa abin da aka yi musu gargaxi da shi ne



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 4

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ka ce: “Shin kun ga abin da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta na qasa, ko kuwa suna da tarayya ne a (halittar) sammai; ku kawo mini wani littafi da yake gabanin wannan (Alqur’anin), ko kuma wani virvishi na ilimi idan kun kasance masu gaskiya.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 5

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Wane ne ya fi vata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alqiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 6

وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Idan kuma aka tashi mutane (ababen bautar) za su kasance abokan gabarsu, kuma su zamo masu musanta bautar tasu



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 7

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَهُمۡ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٌ

Idan kuma an karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waxanda suka kafirce wa gaskiya lokacin da ta zo musu su ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 8

أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۖ قُلۡ إِنِ ٱفۡتَرَيۡتُهُۥ فَلَا تَمۡلِكُونَ لِي مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـًٔاۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَا تُفِيضُونَ فِيهِۚ كَفَىٰ بِهِۦ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

A’a, cewa dai suka yi: “Qagar sa ya yi.” Ka ce: “Idan har na qage shi ne to ba za ku amfana min komai ba game da Allah; Shi ne Ya fi sanin abin da kuke kutsawa cikinsa[1]; Shi Ya isa Mai shaida tsakanina da ku; kuma Shi ne Mai gafara, Mai rahama.”


1- Watau na saqon Alqur’ani da saqon Manzon Allah ().


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 9

قُلۡ مَا كُنتُ بِدۡعٗا مِّنَ ٱلرُّسُلِ وَمَآ أَدۡرِي مَا يُفۡعَلُ بِي وَلَا بِكُمۡۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ وَمَآ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: “Ba ni ne farau ba daga manzanni[1], kuma ba ni da sanin abin da za a yi min da abin da za a yi muku; ni ba abin da nake bi sai abin da ake yiwo min wahayinsa, kuma ni ba wani ba ne face mai gargaxi mai bayyanawa.”


1- Watau ba shi ne na farko ba da Allah () ya aiko da manzanci ballantana har a riqa mamakin haka.


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 10

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَكَفَرۡتُم بِهِۦ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَلَىٰ مِثۡلِهِۦ فَـَٔامَنَ وَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ka ce: “Ku ba ni labari, idan (Alqur’ani) ya kasance daga wurin Allah yake, kuka kuma kafirce masa, kuma wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya ba da shaida a kan irinsa[1], sai ya yi imani (da shi) ku kuma kuka yi girman kai; to lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.”


1- Watau ya shaida da ingancinsa, duba da abin da ya zo na bayaninsa a cikin littafin Attaura.


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 11

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَوۡ كَانَ خَيۡرٗا مَّا سَبَقُونَآ إِلَيۡهِۚ وَإِذۡ لَمۡ يَهۡتَدُواْ بِهِۦ فَسَيَقُولُونَ هَٰذَآ إِفۡكٞ قَدِيمٞ

Waxanda kuma suka kafirce suka ce wa waxanda suka yi imani: “Da (addinin) ya kasance alheri ne, da su ba su riga mu zuwa gare shi ba.” To tunda kuwa ba su shiriya da shi ba, to za su riqa cewa: “Wannan qarya ce daxaxxiya.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 12

وَمِن قَبۡلِهِۦ كِتَٰبُ مُوسَىٰٓ إِمَامٗا وَرَحۡمَةٗۚ وَهَٰذَا كِتَٰبٞ مُّصَدِّقٞ لِّسَانًا عَرَبِيّٗا لِّيُنذِرَ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُحۡسِنِينَ

A gabaninsa kuwa akwai littafin Musa wanda yake jagora ne da rahama. Wannan littafin kuma mai gaskata (na gabaninsa) ne a harshen Larabci, don ya gargaxi waxanda suka kafirta da kuma yin albishir ga masu kyautatawa



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 13

إِنَّ ٱلَّذِينَ قَالُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُ ثُمَّ ٱسۡتَقَٰمُواْ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tsaya kyam, to babu wani tsoro a gare su, kuma su ba za su yi baqin ciki ba



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 14

أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ خَٰلِدِينَ فِيهَا جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxannan su ne ‘yan Aljanna madawwama a cikinta don sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 15

وَوَصَّيۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ بِوَٰلِدَيۡهِ إِحۡسَٰنًاۖ حَمَلَتۡهُ أُمُّهُۥ كُرۡهٗا وَوَضَعَتۡهُ كُرۡهٗاۖ وَحَمۡلُهُۥ وَفِصَٰلُهُۥ ثَلَٰثُونَ شَهۡرًاۚ حَتَّىٰٓ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَبَلَغَ أَرۡبَعِينَ سَنَةٗ قَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَصۡلِحۡ لِي فِي ذُرِّيَّتِيٓۖ إِنِّي تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَإِنِّي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Kuma Mun yi wa mutum wasiyya da kyautata wa mahaifansa; mahaifiyarsa ta xauki cikinsa a wahalce, ta kuma haife shi a wahalce; xaukan cikinsa da yaye shi kuma wata talatin ne, har lokacin da ya cika qarfinsa ya kai shekara arba’in ya ce: “Ya Ubangijina, Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imarka, wadda Ka ni’imta ni da ita da kuma mahaifana, kuma (Ka ba ni iko) in yi aiki nagari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka kyautata min zurriyata; lalle ni na tuba a gare Ka, kuma lalle ni ina daga cikin Musulmi.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 16

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ نَتَقَبَّلُ عَنۡهُمۡ أَحۡسَنَ مَا عَمِلُواْ وَنَتَجَاوَزُ عَن سَيِّـَٔاتِهِمۡ فِيٓ أَصۡحَٰبِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَعۡدَ ٱلصِّدۡقِ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ

Waxannan su ne waxanda Muke karvar mafi kyan abin da suka aikata, kuma Muke yafe musu munanan ayyukansu, suna cikin ‘yan Aljanna; (wannan) alqawari ne na gaskiya wanda suka kasance ana yi musu alqawarinsa (a duniya)



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 17

وَٱلَّذِي قَالَ لِوَٰلِدَيۡهِ أُفّٖ لَّكُمَآ أَتَعِدَانِنِيٓ أَنۡ أُخۡرَجَ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلۡقُرُونُ مِن قَبۡلِي وَهُمَا يَسۡتَغِيثَانِ ٱللَّهَ وَيۡلَكَ ءَامِنۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ فَيَقُولُ مَا هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Wanda kuma ya ce da mahaifansa: “Tir da ku, yanzu kwa riqa yi min alqawarin za a fito da ni (daga qabarina), alhali kuwa tuni wasu al’ummu sun shuxe gabanina?” Su kuma suna ta roqon Allah da cewa: “Kaiconka, ka yi imani mana, lalle alqawarin Allah tabbatacce ne,” sannan ya ce: “Wannan ba wani abu ba ne face tatsuniyoyin mutanen farko!”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 18

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلُ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ خَٰسِرِينَ

Waxannan su ne waxanda kalmar azaba ta tabbata a kansu cikin al’ummun da suka gabace su na aljannu da mutane; lalle su sun kasance asararru



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 19

وَلِكُلّٖ دَرَجَٰتٞ مِّمَّا عَمِلُواْۖ وَلِيُوَفِّيَهُمۡ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Kuma kowane yana da darajoji (na sakamakon) abin da suka aikata; don kuma tabbas zai cika musu sakamakon ayyukansu, ba kuma za a zalunce su ba



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 20

وَيَوۡمَ يُعۡرَضُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَلَى ٱلنَّارِ أَذۡهَبۡتُمۡ طَيِّبَٰتِكُمۡ فِي حَيَاتِكُمُ ٱلدُّنۡيَا وَٱسۡتَمۡتَعۡتُم بِهَا فَٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَوۡنَ عَذَابَ ٱلۡهُونِ بِمَا كُنتُمۡ تَسۡتَكۡبِرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَبِمَا كُنتُمۡ تَفۡسُقُونَ

(Ka tuna) kuma ranar da za a bijiro da waxanda suka kafirta a gaban wuta, (a ce da su): “Kun tafiyar da jin daxinku a rayuwarku ta duniya, kuma kun more ta, to a yau za a saka muku da azabar wulaqanci saboda kun kasance kuna girman kai a bayan qasa ba da wata hujja ba, saboda kuma kun kasance kuna yin fasiqanci.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 21

۞وَٱذۡكُرۡ أَخَا عَادٍ إِذۡ أَنذَرَ قَوۡمَهُۥ بِٱلۡأَحۡقَافِ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلنُّذُرُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦٓ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Ka kuma tuna xan’uwan Adawa (watau Hudu) lokacin da ya gargaxi mutanensa a al‑Ahqafu, alhali haqiqa masu gargaxi sun shuxe a gabaninsa da kuma a bayansa (suna cewa:) “Kada ku bauta wa (kowa) sai Allah, lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 22

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَأۡفِكَنَا عَنۡ ءَالِهَتِنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Sai suka ce: “Yanzu ka zo ne don ka kawar da mu daga ababen bautarmu? To ka zo mana da abin da kake yi mana alqawarin narko (da shi) idan ka kasance cikin masu gaskiya.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 23

قَالَ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَأُبَلِّغُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦ وَلَٰكِنِّيٓ أَرَىٰكُمۡ قَوۡمٗا تَجۡهَلُونَ

Sai ya ce: “Lalle sani yana wurin Allah kawai, ni kuma ina isar muku abin da aka aiko ni da shi ne, sai dai kuma ni ina ganin ku mutane ne masu wauta.”



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 24

فَلَمَّا رَأَوۡهُ عَارِضٗا مُّسۡتَقۡبِلَ أَوۡدِيَتِهِمۡ قَالُواْ هَٰذَا عَارِضٞ مُّمۡطِرُنَاۚ بَلۡ هُوَ مَا ٱسۡتَعۡجَلۡتُم بِهِۦۖ رِيحٞ فِيهَا عَذَابٌ أَلِيمٞ

To lokacin da suka gan ta (azabar) wani hadari ne mai gindayawa, ya doso wa kwarurukansu sai suka ce: “Wannan hadari ne mai ba mu ruwa!” A’a, (ba ku sani ba) shi ne abin da kuke neman gaggautowarsa, watau iska da take cike da azaba mai raxaxi



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 25

تُدَمِّرُ كُلَّ شَيۡءِۭ بِأَمۡرِ رَبِّهَا فَأَصۡبَحُواْ لَا يُرَىٰٓ إِلَّا مَسَٰكِنُهُمۡۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Tana ruguza kowane irin abu da umarnin Ubangijinta, sai suka wayi gari ba abin da ake gani sai (kufaifan) gidajensu. Kamar haka Muke saka wa mutane masu manyan laifuka



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 26

وَلَقَدۡ مَكَّنَّـٰهُمۡ فِيمَآ إِن مَّكَّنَّـٰكُمۡ فِيهِ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ سَمۡعٗا وَأَبۡصَٰرٗا وَأَفۡـِٔدَةٗ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُمۡ سَمۡعُهُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُهُمۡ وَلَآ أَفۡـِٔدَتُهُم مِّن شَيۡءٍ إِذۡ كَانُواْ يَجۡحَدُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Haqiqa Mun kafa su (a bayan qasa) kafawar da ba Mu yi muku irinta ba, Muka kuma sanya musu ji da gani da tunani, sai jin nasu da ganinsu da tunaninsu ba su amfana musu komai ba, tunda sun kasance suna musanta ayoyin Allah, abin da kuma suka kasance suna yi wa izgili ya auka musu



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 27

وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَا مَا حَوۡلَكُم مِّنَ ٱلۡقُرَىٰ وَصَرَّفۡنَا ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Haqiqa mun hallakar da abin da yake kewaye da ku na (mutanen) alqaryu[1], Mun kuma jujjuya musu ayoyi (ta fuskoki daban-daban) don su dawo (kan hanya)


1- Watau kafirai da suka yi maqotaka da su, kamar Adawa da Samudawa da mutanen Annabi Lux () da mutanen Madyana.


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 28

فَلَوۡلَا نَصَرَهُمُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ قُرۡبَانًا ءَالِهَةَۢۖ بَلۡ ضَلُّواْ عَنۡهُمۡۚ وَذَٰلِكَ إِفۡكُهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

To me ya hana allolin da suka riqe suna bautar su ba Allah ba, su taimake su? A’a, sun dai vace musu ne. Wannan kuma da man qaryarsu ce da kuma abin da suka kasance suna qagawa



Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 29

وَإِذۡ صَرَفۡنَآ إِلَيۡكَ نَفَرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَلَمَّا حَضَرُوهُ قَالُوٓاْ أَنصِتُواْۖ فَلَمَّا قُضِيَ وَلَّوۡاْ إِلَىٰ قَوۡمِهِم مُّنذِرِينَ

(Ka tuna) kuma lokacin da Muka juyo maka da wata jama’a ta aljannu don su saurari Alqur’ani[1]. To lokacin da suka halarto shi, sai suka ce: “Ku yi shiru;” sannan lokacin da aka gama (karatunsa) sai suka juya zuwa mutanensu suna yi musu gargaxi


1- Su ne wasu aljannu da suka saurari karatun Annabi () a wani wuri da ake kira Baxnu Nakhla, lokacin da yake yi wa sahabbansa sallar asuba.


Sure: Suratul Ahqaf 

Vers : 30

قَالُواْ يَٰقَوۡمَنَآ إِنَّا سَمِعۡنَا كِتَٰبًا أُنزِلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ يَهۡدِيٓ إِلَى ٱلۡحَقِّ وَإِلَىٰ طَرِيقٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Suka ce: “Ya ku mutanenmu, haqiqa mu mun jiwo wani littafi da aka saukar bayan Musa, mai gaskata abin da yake gabaninsa, yana shiryarwa zuwa gaskiya da kuma zuwa tafarki madaidaici