Sure: Suratu Ghafir

Vers : 1

حمٓ

HA MIM



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

Saukarwar Littafi daga Allah ne Mabuwayi, Masani



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 3

غَافِرِ ٱلذَّنۢبِ وَقَابِلِ ٱلتَّوۡبِ شَدِيدِ ٱلۡعِقَابِ ذِي ٱلطَّوۡلِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ إِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ

Mai gafarta zunubi, Mai kuma karvar tuba, Mai tsananin uquba, Mai ni’imatarwa; babu abin bauta wa da gaskiya sai Shi; makoma zuwa gare Shi ne



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 4

مَا يُجَٰدِلُ فِيٓ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَا يَغۡرُرۡكَ تَقَلُّبُهُمۡ فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Babu mai yin jayayya game da ayoyin Allah sai waxanda suka kafirta, saboda haka kada yawan zirga-zirgarsu a garuruwa ya ruxe ka



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 5

كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۖ وَهَمَّتۡ كُلُّ أُمَّةِۭ بِرَسُولِهِمۡ لِيَأۡخُذُوهُۖ وَجَٰدَلُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّ فَأَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ

Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su, da kuma qungiyoyi (na kafirai) bayansu; kowace al’umma kuma sun yi mummunan nufi da manzonsu don su kama shi (su cutar da shi); suka kuma yi jayayya da (hujja ta) qarya don su rusa gaskiya da ita, sai Na kama su; to yaya uqubata ta kasance?



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 6

وَكَذَٰلِكَ حَقَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

Kamar haka ne kuma kalmar Ubangijinka (ta azaba) ta tabbata a kan waxanda suka kafirta cewa, lalle su ‘yan wuta ne



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 7

ٱلَّذِينَ يَحۡمِلُونَ ٱلۡعَرۡشَ وَمَنۡ حَوۡلَهُۥ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَيُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَيَسۡتَغۡفِرُونَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْۖ رَبَّنَا وَسِعۡتَ كُلَّ شَيۡءٖ رَّحۡمَةٗ وَعِلۡمٗا فَٱغۡفِرۡ لِلَّذِينَ تَابُواْ وَٱتَّبَعُواْ سَبِيلَكَ وَقِهِمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda suke xauke da Al’arshi da waxanda suke kewaye da shi suna yin tasbihi da yabon Ubangijinsu, suna kuma yin imani da Shi, kuma suna nema wa waxanda suka yi imani gafara, (suna cewa): “Ya Ubangiijnmu, ka yalwaci kowane abu da rahama da ilimi, to Ka gafarta wa waxanda suka tuba suka kuma bi hanyarka, Ka kuma kiyaye su daga azabar (wutar) Jahimu



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 8

رَبَّنَا وَأَدۡخِلۡهُمۡ جَنَّـٰتِ عَدۡنٍ ٱلَّتِي وَعَدتَّهُمۡ وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡۚ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

“Ya Ubangijinmu, Ka kuma shigar da su gidajen Aljannar zama waxanda ka alqawarta musu, tare da waxanda suke salihai daga iyayensu da matayensu da kuma zuriyarsu. Lalle Kai Mabuwayi ne, Mai hikima



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 9

وَقِهِمُ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ وَمَن تَقِ ٱلسَّيِّـَٔاتِ يَوۡمَئِذٖ فَقَدۡ رَحِمۡتَهُۥۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

“Ka kuma kiyaye su munanan (ayyuka). Duk kuwa wanda Ka kiyaye shi daga munanan (sakamako) a wannan rana, haqiqa Ka yi masa rahama. Wannan kuwa shi ne babban rabo.”



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُنَادَوۡنَ لَمَقۡتُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُ مِن مَّقۡتِكُمۡ أَنفُسَكُمۡ إِذۡ تُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلۡإِيمَٰنِ فَتَكۡفُرُونَ

Lalle waxanda suka kafirta ana kiran su cewa: “Tabbas fushin Allah da ku ya fi girman fushinku ga kawunanku, lokacin da ake kiran ku zuwa imani (a duniya) sai kuke kafircewa.”



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 11

قَالُواْ رَبَّنَآ أَمَتَّنَا ٱثۡنَتَيۡنِ وَأَحۡيَيۡتَنَا ٱثۡنَتَيۡنِ فَٱعۡتَرَفۡنَا بِذُنُوبِنَا فَهَلۡ إِلَىٰ خُرُوجٖ مِّن سَبِيلٖ

Suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka kashe mu sau biyu Ka kuma raya mu sau biyu[1], to mun amsa laifukanmu, shin ko akwai wata hanya ta fita (daga wuta)?”


1- Watau ya samar da su bayan babu su, sannan ya kashe su, sannan ya sake raya su domin yi musu hisabi.


Sure: Suratu Ghafir

Vers : 12

ذَٰلِكُم بِأَنَّهُۥٓ إِذَا دُعِيَ ٱللَّهُ وَحۡدَهُۥ كَفَرۡتُمۡ وَإِن يُشۡرَكۡ بِهِۦ تُؤۡمِنُواْۚ فَٱلۡحُكۡمُ لِلَّهِ ٱلۡعَلِيِّ ٱلۡكَبِيرِ

Wannan (sakamakon) saboda cewa, idan aka kira Allah Shi kaxai sai ku kafirce, idan kuwa aka yi shirka da Shi, sai ku yi imani. To hukuncin na Allah ne Maxaukaki, Mai girma



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 13

هُوَ ٱلَّذِي يُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُنَزِّلُ لَكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ رِزۡقٗاۚ وَمَا يَتَذَكَّرُ إِلَّا مَن يُنِيبُ

Shi ne wanda Yake nuna muku ayoyinsa, Yake kuma saukar muku da arziki daga sama (watau ruwan sama). Ba kuma kowa ne yake wa’azantuwa ba sai mai komawa (ga Allah)



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 14

فَٱدۡعُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Sai ku bauta wa Allah kuna masu tsantsanta addini gare Shi, ko da kuwa kafirai ba sa so



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 15

رَفِيعُ ٱلدَّرَجَٰتِ ذُو ٱلۡعَرۡشِ يُلۡقِي ٱلرُّوحَ مِنۡ أَمۡرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦ لِيُنذِرَ يَوۡمَ ٱلتَّلَاقِ

(Shi ne) Mai maxaukakan darajoji, Ma’abocin Al’arshi, Yana sauko da wahayi daga umarninsa ga wanda Ya ga dama daga bayinsa don Ya yi gargaxin ranar haxuwa



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 16

يَوۡمَ هُم بَٰرِزُونَۖ لَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِنۡهُمۡ شَيۡءٞۚ لِّمَنِ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَۖ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ

Ranar da za su bayyana; babu wani abu nasu da zai vuya ga Allah. (Zai ce): “Mulki na wane ne a yau?” (Sai Ya ce): “Na Allah Makaxaici, Mai rinjaye ne.”



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 17

ٱلۡيَوۡمَ تُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۚ لَا ظُلۡمَ ٱلۡيَوۡمَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

A wannan ranar za a saka wa kowane rai da irin abin da ya aikata. Babu zalunci a wannan ranar. Lalle Allah Mai gaggawar yin hisabi ne



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 18

وَأَنذِرۡهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡأٓزِفَةِ إِذِ ٱلۡقُلُوبُ لَدَى ٱلۡحَنَاجِرِ كَٰظِمِينَۚ مَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ حَمِيمٖ وَلَا شَفِيعٖ يُطَاعُ

Ka kuma tsoratar da su ranar (alqiyama) mai kusantowa, a yayin da zukata suke maqare a wuyoyinsu (saboda tsananin tsoro). Azzalumai ba su da wani masoyi ko kuma wani mai ceto da za a yi wa biyayya



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 19

يَعۡلَمُ خَآئِنَةَ ٱلۡأَعۡيُنِ وَمَا تُخۡفِي ٱلصُّدُورُ

(Allah) Yana sane da ha’incin idanuwa da kuma abin da zukata suke voyewa



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 20

وَٱللَّهُ يَقۡضِي بِٱلۡحَقِّۖ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقۡضُونَ بِشَيۡءٍۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Allah Yana hukunci da gaskiya; waxanda kuwa suke bauta wa wanda ba Shi ba, ba sa hukunta komai. Haqiqa Allah Shi ne Mai ji, Mai gani



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 21

۞أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُواْ هُمۡ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Shin ba sa tafiya a bayan qasa sannan su ga yaya qarshen waxanda suka kasance gabaninsu ya zama? Su sun kasance sun fi su tsananin qarfi da barin gurabe na tarihi a bayan qasa, sai Allah Ya kama su da laifukansu, ba su kuma da wani mai kare su daga Allah



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 22

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَانَت تَّأۡتِيهِمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَكَفَرُواْ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Wannan (ya same su ne) saboda manzanninsu sun kasance suna zuwa musu da hujjoji bayyanannu, sai suka kafirce, sai Allah Ya kama su. Lalle Shi Mai (tsananin) qarfi ne, Mai tsananin azaba



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 23

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu da kuma hujja mabayyaniya



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 24

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَقَٰرُونَ فَقَالُواْ سَٰحِرٞ كَذَّابٞ

Zuwa ga Fir’auna da Hamana da Qaruna, sai suka ce shi mai sihiri ne, babban maqaryaci



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 25

فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ مِنۡ عِندِنَا قَالُواْ ٱقۡتُلُوٓاْ أَبۡنَآءَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ وَٱسۡتَحۡيُواْ نِسَآءَهُمۡۚ وَمَا كَيۡدُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

To lokacin da ya zo musu da gaskiya daga wajenmu sai suka ce: “Ku kashe `ya`yan waxanda suka yi imani tare da shi, ku kuma qyale matansu da rai.” Makircin kafirai bai zama ba sai a lalace



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 26

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ذَرُونِيٓ أَقۡتُلۡ مُوسَىٰ وَلۡيَدۡعُ رَبَّهُۥٓۖ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُمۡ أَوۡ أَن يُظۡهِرَ فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡفَسَادَ

Fir’auna kuma ya ce: “Ku bar ni in kashe Musa, kuma (ya je) ya kirawo Ubangijin nasa; lalle ni ina jin tsoron kada ya sauya addininku ko kuma ya bayyanar da varna a bayan qasa[1].”


1- Watau zai kawo rikici da savani tsakanin mutane wanda zai haifar musu da yamutsi da kashe-kashe.


Sure: Suratu Ghafir

Vers : 27

وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُم مِّن كُلِّ مُتَكَبِّرٖ لَّا يُؤۡمِنُ بِيَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ

Musa ya ce: “Lalle ni ina neman tsari da Ubangijina, da kuma Ubangijinku daga duk wani mai girman kai da ba ya yin imani da ranar hisabi.”



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 28

وَقَالَ رَجُلٞ مُّؤۡمِنٞ مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَكۡتُمُ إِيمَٰنَهُۥٓ أَتَقۡتُلُونَ رَجُلًا أَن يَقُولَ رَبِّيَ ٱللَّهُ وَقَدۡ جَآءَكُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ مِن رَّبِّكُمۡۖ وَإِن يَكُ كَٰذِبٗا فَعَلَيۡهِ كَذِبُهُۥۖ وَإِن يَكُ صَادِقٗا يُصِبۡكُم بَعۡضُ ٱلَّذِي يَعِدُكُمۡۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَنۡ هُوَ مُسۡرِفٞ كَذَّابٞ

Kuma wani mutum mumini daga dangin Fir’auna wanda yake voye imaninsa ya ce: “Yanzu kwa kashe mutum don ya ce ‘Allah ne Ubangijina’, kuma alhalin ya zo muku da hujjoji bayyanannu daga Ubangijinku? Idan ya zama maqaryaci ne to laifin qaryarsa yana kansa; idan kuwa ya zama mai gaskiya, to wani abu daga abin da yake yi muku gargaxinsa zai same ku. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake shi mai yawan varna ne, maqaryaci



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 29

يَٰقَوۡمِ لَكُمُ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡيَوۡمَ ظَٰهِرِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَن يَنصُرُنَا مِنۢ بَأۡسِ ٱللَّهِ إِن جَآءَنَاۚ قَالَ فِرۡعَوۡنُ مَآ أُرِيكُمۡ إِلَّا مَآ أَرَىٰ وَمَآ أَهۡدِيكُمۡ إِلَّا سَبِيلَ ٱلرَّشَادِ

“Ya ku mutanena, a yau ku ne masu mulki masu qarfi a bayan qasa, to wane ne zai kare mu daga azabar Allah idan ta zo mana?” Fir’auna ya ce: “Ba abin da nake nuna muku sai abin da na gani (shi ne daidai), kuma hanyar shiriya kaxai nake nuna muku.”



Sure: Suratu Ghafir

Vers : 30

وَقَالَ ٱلَّذِيٓ ءَامَنَ يَٰقَوۡمِ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُم مِّثۡلَ يَوۡمِ ٱلۡأَحۡزَابِ

Sai kuma wannan da ya yi imani ya ce: “Ya ku mutanena, lalle ni ina jiye muku tsoron irin ranar gangamin qungiyoyin (kafirai)