Sure: Suratus Sajda

Vers : 1

الٓمٓ

ALIF LAM MIM[1]


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Sure: Suratus Sajda

Vers : 2

تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Saukar da Littafin da babu kokwanto a cikinsa daga Ubangijin talikai ne



Sure: Suratus Sajda

Vers : 3

أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰهُۚ بَلۡ هُوَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أَتَىٰهُم مِّن نَّذِيرٖ مِّن قَبۡلِكَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ

Ko kuwa suna cewa (Annabi Muhammadu) qirqirar sa ya yi?” Ba haka ne ba, shi dai (Alqur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, don ka gargaxi mutanen da wani mai gargaxi bai zo musu gabaninka ba, don su shiriya



Sure: Suratus Sajda

Vers : 4

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ مَا لَكُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا شَفِيعٍۚ أَفَلَا تَتَذَكَّرُونَ

Allah ne Wanda Ya halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida sannan Ya daidaita bisa Al’arshi; ba ku da wani majivincin al’amari ko mai ceto bayansa. Yanzu me ya sa ba kwa wa’azantuwa?



Sure: Suratus Sajda

Vers : 5

يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ثُمَّ يَعۡرُجُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥٓ أَلۡفَ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Yana shirya al’amari daga sama zuwa qasa sannan (al’amarin) ya hau zuwa gare Shi a cikin wani yini da gwargwadon (tsawonsa) yake shekara dubu ne daga abin da kuke qirgawa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 6

ذَٰلِكَ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Wannan (Shi ne) Masanin voye da sarari, Mabuwayi, Mai rahama



Sure: Suratus Sajda

Vers : 7

ٱلَّذِيٓ أَحۡسَنَ كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥۖ وَبَدَأَ خَلۡقَ ٱلۡإِنسَٰنِ مِن طِينٖ

Wanda Ya kyautata kowane abu da ya halicce shi; kuma Ya fari halittar mutum daga tavo



Sure: Suratus Sajda

Vers : 8

ثُمَّ جَعَلَ نَسۡلَهُۥ مِن سُلَٰلَةٖ مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ

Sannan Ya sanya zuriyarsa daga tataccen ruwa wulaqantacce



Sure: Suratus Sajda

Vers : 9

ثُمَّ سَوَّىٰهُ وَنَفَخَ فِيهِ مِن رُّوحِهِۦۖ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

Sannan Ya daidaita shi, Ya kuma busa masa daga ruhinsa; kuma Ya sanya muku ji da gani da zukata. Kaxan ne qwarai kuke godewa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 10

وَقَالُوٓاْ أَءِذَا ضَلَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ أَءِنَّا لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدِۭۚ بَلۡ هُم بِلِقَآءِ رَبِّهِمۡ كَٰفِرُونَ

Suka kuma ce: “Yanzu idan muka zagwanye a cikin qasa, ashe za a sake sabunta halittarmu?” A’a, su dai suna kafircewa ne da saduwa da Ubangijinsu



Sure: Suratus Sajda

Vers : 11

۞قُلۡ يَتَوَفَّىٰكُم مَّلَكُ ٱلۡمَوۡتِ ٱلَّذِي وُكِّلَ بِكُمۡ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ

Ka ce (da su): “Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karvi ranku sannan kuma ga Ubangijinku za a komar da ku



Sure: Suratus Sajda

Vers : 12

وَلَوۡ تَرَىٰٓ إِذِ ٱلۡمُجۡرِمُونَ نَاكِسُواْ رُءُوسِهِمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ رَبَّنَآ أَبۡصَرۡنَا وَسَمِعۡنَا فَٱرۡجِعۡنَا نَعۡمَلۡ صَٰلِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ

Da kuwa za ka ga lokacin da masu manyan laifuka suke sunkuye da kawunansu a wurin Ubangiijnsu (suna cewa): “Ya Ubangijinmu, mun gani, mun kuma ji, to Ka mayar da mu (duniya), za mu yi aiki nagari, haqiqa mu masu sakankancewa ne.”



Sure: Suratus Sajda

Vers : 13

وَلَوۡ شِئۡنَا لَأٓتَيۡنَا كُلَّ نَفۡسٍ هُدَىٰهَا وَلَٰكِنۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ مِنِّي لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Idan kuwa da Mun ga dama, tabbas da Mun bai wa kowane rai shiriyarsa, sai dai kuma maganata ta tabbata cewa, tabbas zan cike Jahannama da aljannu da mutane gaba xaya



Sure: Suratus Sajda

Vers : 14

فَذُوقُواْ بِمَا نَسِيتُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَآ إِنَّا نَسِينَٰكُمۡۖ وَذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡخُلۡدِ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Sai (a ce da su): “Ku xanxani (azaba) saboda mancewa da kuka yi da saduwa da wannan ranar taku, lalle Mu ma Mun yi watsi da ku; kuma ku xanxani azaba mai xorewa saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 15

إِنَّمَا يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِهَا خَرُّواْۤ سُجَّدٗاۤ وَسَبَّحُواْ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ۩

Lalle kawai masu imani da ayoyinmu su ne waxanda idan aka yi musu wa’azi da su za su faxi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi tare da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai



Sure: Suratus Sajda

Vers : 16

تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمۡ عَنِ ٱلۡمَضَاجِعِ يَدۡعُونَ رَبَّهُمۡ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

Kuyavunsu suna nesantar wuraren kwanciya[1], suna bauta wa Ubangijinsu cikin halin tsoro da kuma kwaxayi, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka arzuta su


1- Watau suna qaurace wa wuraren barci, suna tsayawa cikin dare suna sallolin nafilfilu suna roqon Allah ().


Sure: Suratus Sajda

Vers : 17

فَلَا تَعۡلَمُ نَفۡسٞ مَّآ أُخۡفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعۡيُنٖ جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Kuma ba wani rai da zai san abin da aka voye musu na faranta rai, don sakamako game da abin da suka kasance suna aikatawa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 18

أَفَمَن كَانَ مُؤۡمِنٗا كَمَن كَانَ فَاسِقٗاۚ لَّا يَسۡتَوُۥنَ

Yanzu wanda ya zamanto mumini ya zama kamar wanda ya kasance fasiqi? Ai ba za su zama daidai ba



Sure: Suratus Sajda

Vers : 19

أَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلۡمَأۡوَىٰ نُزُلَۢا بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Amma waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, to suna da gidajen Aljanna na makoma, (wannan) liyafa ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 20

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ فَسَقُواْ فَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ كُلَّمَآ أَرَادُوٓاْ أَن يَخۡرُجُواْ مِنۡهَآ أُعِيدُواْ فِيهَا وَقِيلَ لَهُمۡ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلنَّارِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Amma kuma waxanda suka fice daga biyayyar Allah, to makomarsu wuta ce; ko da yaushe suka yi niyyar fitowa daga gare ta sai a mayar da su a cikinta a kuma ce da su: “Ku xanxani azabar wuta wadda kuka kasance kuna qaryatawa.”



Sure: Suratus Sajda

Vers : 21

وَلَنُذِيقَنَّهُم مِّنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَدۡنَىٰ دُونَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَكۡبَرِ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Kuma tabbas lalle za Mu xanxana musu (wani abu) daga azabar da ta fi qanqanta (ta duniya) kafin azabar da ta fi girma (ta lahira) don su dawo (daga vata)



Sure: Suratus Sajda

Vers : 22

وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦ ثُمَّ أَعۡرَضَ عَنۡهَآۚ إِنَّا مِنَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ مُنتَقِمُونَ

Wane ne kuma mafi zalunci fiye da wanda aka yi wa wa’azi da ayoyin Ubangijinsa sannan ya bijire musu? Lalle Mu Masu saka wa masu manyan laifuka ne



Sure: Suratus Sajda

Vers : 23

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ فَلَا تَكُن فِي مِرۡيَةٖ مِّن لِّقَآئِهِۦۖ وَجَعَلۡنَٰهُ هُدٗى لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Haqiqa kuma Mu Mun bai wa Musa Littafi, to kada ka kasance (kai Manzo) cikin kokwanto na saduwa da shi (Musan)[1]. Kuma Mun sanya shi ya zamanto shiriya ga Banu-Isra’ila


1- Watau haxuwar Annabi Muhammad () da Annabi Musa () a daren mi’iraji.


Sure: Suratus Sajda

Vers : 24

وَجَعَلۡنَا مِنۡهُمۡ أَئِمَّةٗ يَهۡدُونَ بِأَمۡرِنَا لَمَّا صَبَرُواْۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يُوقِنُونَ

Muka kuma sanya shugabanni daga cikinsu waxanda suke shiryuwa da umarninmu yayin da suka yi haquri, suka kuma kasance suna sakankancewa da ayoyinmu



Sure: Suratus Sajda

Vers : 25

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَفۡصِلُ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Lalle Ubangijinka Shi ne zai yi hukunci a tsakaninsu ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna sassavawa a kansa



Sure: Suratus Sajda

Vers : 26

أَوَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَبۡلِهِم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٍۚ أَفَلَا يَسۡمَعُونَ

Yanzu ba su gane wa idanunsu ba al’ummu nawa Muka hallakar a gabaninsu waxanda suke ta zirga-zirga tsakankanin gidajensu? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi; to me ya sa ba sa sauraro ne?



Sure: Suratus Sajda

Vers : 27

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَسُوقُ ٱلۡمَآءَ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡجُرُزِ فَنُخۡرِجُ بِهِۦ زَرۡعٗا تَأۡكُلُ مِنۡهُ أَنۡعَٰمُهُمۡ وَأَنفُسُهُمۡۚ أَفَلَا يُبۡصِرُونَ

Ko kuwa ba sa gani cewa Mu Muke koro ruwa zuwa ga qeqasasshiyar qasa, sai Mu fitar da tsirrai da shi, waxanda dabbobinsu da su kansu suke ci daga gare shi? To me ya sa ba sa lura ne?



Sure: Suratus Sajda

Vers : 28

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡفَتۡحُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Yaushe ne (ranar) wannan hukuncin idan kun kasance masu gaskiya?



Sure: Suratus Sajda

Vers : 29

قُلۡ يَوۡمَ ٱلۡفَتۡحِ لَا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِيمَٰنُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Ka ce: “Ranar hukuncin, waxanda suka kafirce, imaninsu ba zai amfane su ba, kuma ba ma za a saurara musu ba.”



Sure: Suratus Sajda

Vers : 30

فَأَعۡرِضۡ عَنۡهُمۡ وَٱنتَظِرۡ إِنَّهُم مُّنتَظِرُونَ

To ka rabu da su, ka kuma saurara, lalle su ma masu sauraro ne