Sure: Suratu Yunus

Vers : 1

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡحَكِيمِ

ALIF LAM RA[1]. Waxannan ayoyin littafi ne (wato Alqur’ani) mai hikima


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Sure: Suratu Yunus

Vers : 2

أَكَانَ لِلنَّاسِ عَجَبًا أَنۡ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ رَجُلٖ مِّنۡهُمۡ أَنۡ أَنذِرِ ٱلنَّاسَ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنَّ لَهُمۡ قَدَمَ صِدۡقٍ عِندَ رَبِّهِمۡۗ قَالَ ٱلۡكَٰفِرُونَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٞ مُّبِينٌ

Shin ya zama abin mamaki ga mutane cewar Mun yi wahayi zuwa ga wani mutum daga cikinsu, cewa: “Ka gargaxi mutane, kuma ka yi wa waxanda suka yi imani albishir cewa suna da babban matsayi wurin Ubangijinsu? Sai kafirai suka ce: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne mai bayyana (sihirinsa).”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 3

إِنَّ رَبَّكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَۖ مَا مِن شَفِيعٍ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ إِذۡنِهِۦۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Lalle Ubangijinku Shi ne Allah wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi[1]; Yana tsara al’amari (yadda Ya ga dama). Babu wani mai ceto sai da izininsa. Wannan Shi ne Allah Ubangijinku. To sai ku bauta masa. Ashe ba za ku wa’azantu ba?


1- Duba Suratul A’araf aya ta 54. hashiya ta 126.


Sure: Suratu Yunus

Vers : 4

إِلَيۡهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗاۖ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقًّاۚ إِنَّهُۥ يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّ يُعِيدُهُۥ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ بِٱلۡقِسۡطِۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ

Zuwa gare Shi ne makomarku take gaba xaya; alqawarin Allah ne da gaske. Lalle Shi ne Yake farar da halitta sannan Ya maido da ita (bayan mutuwa) don Ya saka wa waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari da adalci. Waxanda suka kafirce kuwa suna da abin sha mai tsananin quna da kuma azaba mai raxaxi saboda kafircewa da suke yi



Sure: Suratu Yunus

Vers : 5

هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلشَّمۡسَ ضِيَآءٗ وَٱلۡقَمَرَ نُورٗا وَقَدَّرَهُۥ مَنَازِلَ لِتَعۡلَمُواْ عَدَدَ ٱلسِّنِينَ وَٱلۡحِسَابَۚ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Shi ne Wanda Ya sanya muku rana ta zamo mai haske da kuma wata ya zamo mai haskakawa, Ya kuma sanya shi mai masaukai don ku san adadin shekaru da kuma (sanin) lissafi (na lokuta). Allah bai halicci wannan ba sai da gaskiya. Yana bayyana ayoyi ne ga mutanen da suke da sani



Sure: Suratu Yunus

Vers : 6

إِنَّ فِي ٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَّقُونَ

Lalle game da sassavawar dare da rana da kuma abubuwan da Allah Ya halitta cikin sammai da qasa akwai ayoyi ga mutanen da suke kiyaye dokokin Allah



Sure: Suratu Yunus

Vers : 7

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا وَرَضُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَٱطۡمَأَنُّواْ بِهَا وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِنَا غَٰفِلُونَ

Lalle waxanda ba sa tsammanin gamuwa da Mu, suka kuma yarda da rayuwar duniya, kuma suka nutsu da ita, da kuma waxanda suke gafala daga ayoyinmu



Sure: Suratu Yunus

Vers : 8

أُوْلَـٰٓئِكَ مَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُ بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Waxanan makomarsu wuta ce saboda abin da suka kasance suna aikatawa



Sure: Suratu Yunus

Vers : 9

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ يَهۡدِيهِمۡ رَبُّهُم بِإِيمَٰنِهِمۡۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهِمُ ٱلۡأَنۡهَٰرُ فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, Ubangijinsu zai shirye su saboda imaninsu: qoramu suna gudana ta qarqashinsu cikin aljannatai na ni’ima



Sure: Suratu Yunus

Vers : 10

دَعۡوَىٰهُمۡ فِيهَا سُبۡحَٰنَكَ ٱللَّهُمَّ وَتَحِيَّتُهُمۡ فِيهَا سَلَٰمٞۚ وَءَاخِرُ دَعۡوَىٰهُمۡ أَنِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Addu’arsu a cikinta: “Muna tsarkake Ka ya Allah”, gaisuwarsu kuma a cikinta “Salamun” (watau aminci). Qarshen addu’arsu kuma ita ce: “Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 11

۞وَلَوۡ يُعَجِّلُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ ٱلشَّرَّ ٱسۡتِعۡجَالَهُم بِٱلۡخَيۡرِ لَقُضِيَ إِلَيۡهِمۡ أَجَلُهُمۡۖ فَنَذَرُ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Da dai Allah zai gaggauta (karvar addu’ar) mutane ta sharri kamar yadda yake gaggauta ta alheri to da qarshen rayuwarsu ya zo. Sai dai Mukan bar waxanda ba sa tsammanin haxuwa da Mu cikin shisshiginsu su yi ta ximuwa



Sure: Suratu Yunus

Vers : 12

وَإِذَا مَسَّ ٱلۡإِنسَٰنَ ٱلضُّرُّ دَعَانَا لِجَنۢبِهِۦٓ أَوۡ قَاعِدًا أَوۡ قَآئِمٗا فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُ ضُرَّهُۥ مَرَّ كَأَن لَّمۡ يَدۡعُنَآ إِلَىٰ ضُرّٖ مَّسَّهُۥۚ كَذَٰلِكَ زُيِّنَ لِلۡمُسۡرِفِينَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Idan kuma wata cuta ta sami mutum, sai ya roqe Mu, a kishingixe ne ko a zaune ko kuwa a tsaye. To lokacin da Muka yaye masa cutarsa sai ya ci gaba (da halinsa) kamar bai tava roqon Mu game da wata cuta da ta shafe shi ba. Kamar haka ne aka qawata wa mavarnata abin da suka kasance suna aikatawa



Sure: Suratu Yunus

Vers : 13

وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَا ٱلۡقُرُونَ مِن قَبۡلِكُمۡ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Haqiqa kuma Mun hallaka al’ummun da suka gabace ku, lokacin da suka yi zalunci, kuma manzanninsu suka zo musu da (hujjoji) mabayyana, sai ba su zamana sun yi imani ba. Kamar haka ne Muke saka wa mutane masu laifi



Sure: Suratu Yunus

Vers : 14

ثُمَّ جَعَلۡنَٰكُمۡ خَلَـٰٓئِفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لِنَنظُرَ كَيۡفَ تَعۡمَلُونَ

Sannan bayansu Muka mayar da ku madadinsu a bayan qasa don Mu ga me za ku aikata



Sure: Suratu Yunus

Vers : 15

وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَاتُنَا بَيِّنَٰتٖ قَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ لِقَآءَنَا ٱئۡتِ بِقُرۡءَانٍ غَيۡرِ هَٰذَآ أَوۡ بَدِّلۡهُۚ قُلۡ مَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أُبَدِّلَهُۥ مِن تِلۡقَآيِٕ نَفۡسِيٓۖ إِنۡ أَتَّبِعُ إِلَّا مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّۖ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu bayyanannu sai waxanda ba sa tsammanin haxuwa da mu su ce: “Ka zo da wani alqur’anin ba wannan ba, ko kuma ka canja shi.” Ka ce (da su): “Bai dace da ni ba in canja shi da raxin kaina. Ni ba abin da nake bi sai abin da kawai aka yo mini wahayi. Lalle ni dai ina tsoron azabar rana mai girma idan na sava wa Ubangijina.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 16

قُل لَّوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا تَلَوۡتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ وَلَآ أَدۡرَىٰكُم بِهِۦۖ فَقَدۡ لَبِثۡتُ فِيكُمۡ عُمُرٗا مِّن قَبۡلِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ka ce: “Da Allah Ya ga dama da ban karanta muku shi ba, kuma da (Allah) bai sanar da ku shi ba, domin haqiqa na zauna cikinku shekaru masu yawa[1] tun gabaninsa. Me ya sa ba za ku hankalta ba?”


1- Annabi () ya zauna a cikin mutanensa shekara arba’in kafin a fara yi masa wahayi.


Sure: Suratu Yunus

Vers : 17

فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَوۡ كَذَّبَ بِـَٔايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

To ba wanda ya fi zalunci irin wanda ya qirqira wa Allah qarya ko kuma ya qaryata ayoyinsa. Lalle masu babban laifi ba za su rabauta ba



Sure: Suratu Yunus

Vers : 18

وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡ وَيَقُولُونَ هَـٰٓؤُلَآءِ شُفَعَـٰٓؤُنَا عِندَ ٱللَّهِۚ قُلۡ أَتُنَبِّـُٔونَ ٱللَّهَ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Suna kuma bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai cutar da su ba ba kuma zai amfane su ba, suna kuma cewa: “Waxannan su ne masu ceton mu a wurin Allah.” Ka ce: “Shin yanzu za ku ba Allah labarin abin da bai sani ba ne a cikin sammai ko kuma a bayan qasa? Tsarki ya tabbata a gare Shi Ya kuma xaukaka daga abin da suke shirka da Shi.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 19

وَمَا كَانَ ٱلنَّاسُ إِلَّآ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ فَٱخۡتَلَفُواْۚ وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَقُضِيَ بَيۡنَهُمۡ فِيمَا فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

A da can mutane sun zamanto al’umma xaya ce (a kan tauhidi), to sai suka sassava. Da ba don wata kalma da ta gabata daga Ubangijinka[1] ba, to da an yi hukunci a tsakaninsu game da abin da suke sassavawa a kai


1- Watau hukuncinsa na cewa zai saurara wa mushirikai har zuwa ranar alqiyama.


Sure: Suratu Yunus

Vers : 20

وَيَقُولُونَ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۖ فَقُلۡ إِنَّمَا ٱلۡغَيۡبُ لِلَّهِ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ

Suna kuma cewa: “Don me ba a saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa ba?” To ka ce: “Sanin gaibu na Allah ne kawai, sai ku saurara, lalle ni ma ina tare da ku cikin masu sauraro.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 21

وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ مِّنۢ بَعۡدِ ضَرَّآءَ مَسَّتۡهُمۡ إِذَا لَهُم مَّكۡرٞ فِيٓ ءَايَاتِنَاۚ قُلِ ٱللَّهُ أَسۡرَعُ مَكۡرًاۚ إِنَّ رُسُلَنَا يَكۡتُبُونَ مَا تَمۡكُرُونَ

Idan kuma Muka xanxana wa mutane daxi bayan wahala ta same su, sai ga su suna qulla makirci ga ayoyinmu. Ka ce: “Allah Ya fi gaggawar (sakayya a kan) makirci.” Lalle manzanninmu suna rubuta abin da kuke qullawa na makirci



Sure: Suratu Yunus

Vers : 22

هُوَ ٱلَّذِي يُسَيِّرُكُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَرَيۡنَ بِهِم بِرِيحٖ طَيِّبَةٖ وَفَرِحُواْ بِهَا جَآءَتۡهَا رِيحٌ عَاصِفٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡمَوۡجُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ أُحِيطَ بِهِمۡ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنۡ أَنجَيۡتَنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Shi ne Wanda Yake tafiyar da ku a tudu da cikin ruwa, har lokacin da kuka shiga cikin jiragen ruwa, (jiragen) kuwa suka yi gudu da su tare da iska mai daxi, suka kuma yi farin ciki da su (jiragen) sai kuma wata iska mai qarfi ta zo musu; raqumin ruwa kuma ya zo musu ta kowane wuri, suka kuma tabbatar cewa dai su kam an rutsa da su, sai kuma suka roqi Allah suna masu tsarkake addini gare Shi (suna cewa): “Tabbas idan Ka tserar da mu daga wannan, lalle haqiqa za mu zamo cikin masu godiya.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 23

فَلَمَّآ أَنجَىٰهُمۡ إِذَا هُمۡ يَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۗ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَا بَغۡيُكُمۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۖ مَّتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ إِلَيۡنَا مَرۡجِعُكُمۡ فَنُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

To lokacin da Ya tserar da su sai ga su suna varna a bayan qasa ba da gaskiya ba. Ya ku mutane, haqiqa (sakamakon) varnarku a kanku kawai yake; ku xan ji daxin rayuwar duniya; sannan (daga qarshe) zuwa gare Mu ne makomarku take, sannan mu ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Sure: Suratu Yunus

Vers : 24

إِنَّمَا مَثَلُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ مِمَّا يَأۡكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلۡأَنۡعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلۡأَرۡضُ زُخۡرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتۡ وَظَنَّ أَهۡلُهَآ أَنَّهُمۡ قَٰدِرُونَ عَلَيۡهَآ أَتَىٰهَآ أَمۡرُنَا لَيۡلًا أَوۡ نَهَارٗا فَجَعَلۡنَٰهَا حَصِيدٗا كَأَن لَّمۡ تَغۡنَ بِٱلۡأَمۡسِۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Misalin rayuwar duniya kawai kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, to sai shukokin da suke kan qasa suka cuxanya da shi daga abin da mutane da dabbobi suke ci; har lokacin da qasa ta qawata (da shi) ta kuma yi ado; masu ita kuma suka sakankance cewa su masu ikon cin amfaninta ne, sai qaddararmu ta zo mata cikin dare ko rana, sai Muka mayar da ita girbabbiya kamar daxai ba ta rayu ba a jiya. Kamar haka Muke bayyana ayoyi ga mutanen da suke tunani



Sure: Suratu Yunus

Vers : 25

وَٱللَّهُ يَدۡعُوٓاْ إِلَىٰ دَارِ ٱلسَّلَٰمِ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Allah kuwa Yana kira ne zuwa gidan aminci (wato Aljanna), Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama zuwa tafarki madaidaici



Sure: Suratu Yunus

Vers : 26

۞لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ ٱلۡحُسۡنَىٰ وَزِيَادَةٞۖ وَلَا يَرۡهَقُ وُجُوهَهُمۡ قَتَرٞ وَلَا ذِلَّةٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma qari[1]. Wani qunci da qasqanci kuma ba za su same su ba. Waxannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta


1- Watau shi ne ganin Fuskar Allah () bayan shigarsu Aljanna. Duba Muslim #181.


Sure: Suratu Yunus

Vers : 27

وَٱلَّذِينَ كَسَبُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةِۭ بِمِثۡلِهَا وَتَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۖ كَأَنَّمَآ أُغۡشِيَتۡ وُجُوهُهُمۡ قِطَعٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مُظۡلِمًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuma suka yi mummunan aiki, to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma qasqanci zai lulluve su; ba su da wani mai kare su daga (azabar) Allah; kamar dai an lulluve fuskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu qirin. Waxannan su ne ‘yan wuta; su kuma masu dawwama ne a cikinta



Sure: Suratu Yunus

Vers : 28

وَيَوۡمَ نَحۡشُرُهُمۡ جَمِيعٗا ثُمَّ نَقُولُ لِلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ مَكَانَكُمۡ أَنتُمۡ وَشُرَكَآؤُكُمۡۚ فَزَيَّلۡنَا بَيۡنَهُمۡۖ وَقَالَ شُرَكَآؤُهُم مَّا كُنتُمۡ إِيَّانَا تَعۡبُدُونَ

(Ka tuna) ranar da za mu tara su ga baki xaya, sannan mu ce da waxanda suka yi shirka: “Ku tsaya cak a wurarenku ku da abokan tarayyarku”. Sai kuma mu raba tsakaninsu; sai abokan tarayyarsu kuma su ce: “Ba mu ne kuka kasance kuna bauta wa ba



Sure: Suratu Yunus

Vers : 29

فَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمۡ إِن كُنَّا عَنۡ عِبَادَتِكُمۡ لَغَٰفِلِينَ

“To kuma Allah Ya isa shaida tsakaninmu da ku: mu kam lalle mun kasance ba mu ma san kuna bautar mu ba.”



Sure: Suratu Yunus

Vers : 30

هُنَالِكَ تَبۡلُواْ كُلُّ نَفۡسٖ مَّآ أَسۡلَفَتۡۚ وَرُدُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ مَوۡلَىٰهُمُ ٱلۡحَقِّۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

A can ne kowane rai zai samu sakamakon abin da ya gabatar (a duniya). An kuma mayar da su zuwa ga Allah Majivincinsu na gaskiya; abin da kuma suka kasance suna qirqira ya vace musu