Sure: Suratul Baqara

Vers : 241

وَلِلۡمُطَلَّقَٰتِ مَتَٰعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِۖ حَقًّا عَلَى ٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma matan da aka sake su suna da wata kyauta ta kwantar da hankali ta hanyar da aka saba, (wannan) haqqi ne a kan masu taqawa



Sure: Suratul Baqara

Vers : 242

كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ku hankalta



Sure: Suratul Baqara

Vers : 243

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَهُمۡ أُلُوفٌ حَذَرَ ٱلۡمَوۡتِ فَقَالَ لَهُمُ ٱللَّهُ مُوتُواْ ثُمَّ أَحۡيَٰهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

Shin ba ka ga waxanda suka fita daga gidajensu ba su dubbai don tsoron mutuwa, sai Allah Ya ce da su: “Ku mutu”, sannan Ya raya su? Lalle Allah Ma’abocin falala ne ga mutane, sai dai yawancin mutane ba sa godiya



Sure: Suratul Baqara

Vers : 244

وَقَٰتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Kuma ku yi yaqi don xaukaka kalmar Allah, kuma ku sani cewa, lalle Allah Mai ji ne, Masani



Sure: Suratul Baqara

Vers : 245

مَّن ذَا ٱلَّذِي يُقۡرِضُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا فَيُضَٰعِفَهُۥ لَهُۥٓ أَضۡعَافٗا كَثِيرَةٗۚ وَٱللَّهُ يَقۡبِضُ وَيَبۡصُۜطُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Wane ne zai ba wa Allah kyakkyawan rance, sai Ya ninka masa shi ninki mai yawa? Kuma Allah ne Yake kame (dukiya), Yake kuma shimfixa ta, kuma zuwa gare Shi za a mayar da ku



Sure: Suratul Baqara

Vers : 246

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ مِنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنۢ بَعۡدِ مُوسَىٰٓ إِذۡ قَالُواْ لِنَبِيّٖ لَّهُمُ ٱبۡعَثۡ لَنَا مَلِكٗا نُّقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ قَالَ هَلۡ عَسَيۡتُمۡ إِن كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ أَلَّا تُقَٰتِلُواْۖ قَالُواْ وَمَا لَنَآ أَلَّا نُقَٰتِلَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَقَدۡ أُخۡرِجۡنَا مِن دِيَٰرِنَا وَأَبۡنَآئِنَاۖ فَلَمَّا كُتِبَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقِتَالُ تَوَلَّوۡاْ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ

Shin ba ka ga wasu manyan mutane ba daga cikin Banu Isra’ila bayan (mutuwar) Musa yayin da suka faxa wa Annabinsu: “Ka naxa mana wani sarki, wanda za mu yi yaqi (tare da shi) don xaukaka kalmar Allah?” Sai ya ce: “Shin ba kwa tsammanin idan an wajabta muku yaqi, ba za ku yi yaqin ba?” Sai suka ce: “Me zai sa ba za mu yi yaqi don xaukaka kalmar Allah ba, alhali kuwa an fitar da mu daga gidajenmu da ‘ya’yanmu?” To yayin da aka wajabta musu yaqin sai suka juya baya sai ‘yan kaxan daga cikinsu. Kuma Allah Masanin azzalumai ne



Sure: Suratul Baqara

Vers : 247

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ٱللَّهَ قَدۡ بَعَثَ لَكُمۡ طَالُوتَ مَلِكٗاۚ قَالُوٓاْ أَنَّىٰ يَكُونُ لَهُ ٱلۡمُلۡكُ عَلَيۡنَا وَنَحۡنُ أَحَقُّ بِٱلۡمُلۡكِ مِنۡهُ وَلَمۡ يُؤۡتَ سَعَةٗ مِّنَ ٱلۡمَالِۚ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰهُ عَلَيۡكُمۡ وَزَادَهُۥ بَسۡطَةٗ فِي ٱلۡعِلۡمِ وَٱلۡجِسۡمِۖ وَٱللَّهُ يُؤۡتِي مُلۡكَهُۥ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Kuma Annabinsu ya ce da su: “Lalle haqiqa Allah Ya naxa Xalutu ya zama Sarki gare ku.” Sai suka ce: “Ta yaya zai samu sarauta a kanmu, alhalin mun fi shi cancatar sarauta, kuma ba a ba shi yalwar dukiya ba?” Sai ya ce: “Lalle Allah Ya zave shi a kanku, kuma Ya qare shi da yalwar ilimi da ta girman jiki, kuma Allah Yana bayar da mulkinsa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 248

وَقَالَ لَهُمۡ نَبِيُّهُمۡ إِنَّ ءَايَةَ مُلۡكِهِۦٓ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلتَّابُوتُ فِيهِ سَكِينَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَبَقِيَّةٞ مِّمَّا تَرَكَ ءَالُ مُوسَىٰ وَءَالُ هَٰرُونَ تَحۡمِلُهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai Annabinsu ya ce da su: “Lalle alamar (cancantar) mulkinsa ita ce akwatin nan da zai zo muku wanda a cikinsa akwai nutsuwa daga Ubangijinku da kuma sauran abin da iyalin Musa suka bari da iyalin Haruna; mala’iku na xauke da shi. Lalle a cikin wannan tabbas akwai aya a gare ku, in kun kasance muminai.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 249

فَلَمَّا فَصَلَ طَالُوتُ بِٱلۡجُنُودِ قَالَ إِنَّ ٱللَّهَ مُبۡتَلِيكُم بِنَهَرٖ فَمَن شَرِبَ مِنۡهُ فَلَيۡسَ مِنِّي وَمَن لَّمۡ يَطۡعَمۡهُ فَإِنَّهُۥ مِنِّيٓ إِلَّا مَنِ ٱغۡتَرَفَ غُرۡفَةَۢ بِيَدِهِۦۚ فَشَرِبُواْ مِنۡهُ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۚ فَلَمَّا جَاوَزَهُۥ هُوَ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ قَالُواْ لَا طَاقَةَ لَنَا ٱلۡيَوۡمَ بِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦۚ قَالَ ٱلَّذِينَ يَظُنُّونَ أَنَّهُم مُّلَٰقُواْ ٱللَّهِ كَم مِّن فِئَةٖ قَلِيلَةٍ غَلَبَتۡ فِئَةٗ كَثِيرَةَۢ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ

To yayin da Xalutu ya fita (bayan gari) da rundunarsa, sai ya ce: “Lalle Allah zai jarrabe ku da wata qorama, to duk wanda ya sha daga gare ta, to ba ya tare da ni, duk wanda kuwa bai sha ba, to wannan yana tare da ni, sai dai wanda ya kamfata sau xaya da (tafin) hannunsa.” Gaba xayansu sai suka sha daga cikinta sai ‘yan kaxan daga cikinsu (su ne ba su sha ba). To yayin da ya qetare shi, shi da waxanda suka yi imani tare da shi, sai suka ce: “A yau kam ba mu da iko wajen fuskantar Jalutu da rundunarsa.” Sai waxanda suke da yaqinin cewa za su haxu da Allah suka ce: “Sau da yawa wata runduna ‘yan kaxan takan yi rinjaye a kan wata runduna mai yawa da izinin Allah. Kuma Allah Yana tare da masu haquri.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 250

وَلَمَّا بَرَزُواْ لِجَالُوتَ وَجُنُودِهِۦ قَالُواْ رَبَّنَآ أَفۡرِغۡ عَلَيۡنَا صَبۡرٗا وَثَبِّتۡ أَقۡدَامَنَا وَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Kuma yayin da suka yi fito-na-fito da Jalutu da rundunarsa, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka zubo mana haquri na musamman, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutane kafirai.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 251

فَهَزَمُوهُم بِإِذۡنِ ٱللَّهِ وَقَتَلَ دَاوُۥدُ جَالُوتَ وَءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَهُۥ مِمَّا يَشَآءُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai suka murqushe su da izinin Allah, kuma Dawudu ya kashe Jalutu, sai Allah Ya ba shi mulki da hikima, kuma Ya sanar da shi irin abin da Ya ga dama. Ba don yadda Allah Yake kare wani sashin mutane da wani sashi ba, to lalle da qasa ta lalace, sai dai kuma Allah Ma’abocin falala ne ga talikai



Sure: Suratul Baqara

Vers : 252

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Waxannan ayoyin Allah ne, Muna karanta maka su da gaskiya, kuma lalle kai tabbas kana cikin manzanni



Sure: Suratul Baqara

Vers : 253

۞تِلۡكَ ٱلرُّسُلُ فَضَّلۡنَا بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۘ مِّنۡهُم مَّن كَلَّمَ ٱللَّهُۖ وَرَفَعَ بَعۡضَهُمۡ دَرَجَٰتٖۚ وَءَاتَيۡنَا عِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَيَّدۡنَٰهُ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِۗ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلَ ٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡبَيِّنَٰتُ وَلَٰكِنِ ٱخۡتَلَفُواْ فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ وَمِنۡهُم مَّن كَفَرَۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا ٱقۡتَتَلُواْ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

Waxannan manzanni, Mun fifita sashinsu a kan sashi. Cikinsu akwai wanda Allah Ya yi magana da shi, kuma Ya xaukaka wasunsu da darajoji. Kuma Mun bai wa Isa xan Maryam hujjoji bayyanannu, kuma Mun qarfafe shi da Ruhi mai tsarki. Da kuma Allah Ya ga dama da waxanda suka zo bayansu ba su yaqi juna ba bayan hujjoji bayanannu sun zo musu, sai dai kuma sun yi savani; cikinsu akwai wanda ya yi imani, kuma cikinsu akwai wanda ya kafirce, kuma da Allah Ya ga dama da ba su yaqi juna ba, sai dai Allah Yana aikata abin da Yake nufi



Sure: Suratul Baqara

Vers : 254

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا بَيۡعٞ فِيهِ وَلَا خُلَّةٞ وَلَا شَفَٰعَةٞۗ وَٱلۡكَٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku ciyar daga abin da Muka arzurta ku (da shi) tun kafin wani yini ya zo wanda babu ciniki a cikinsa kuma babu abokantaka, kuma babu ceto. Kafirai kuwa su ne azzalumai



Sure: Suratul Baqara

Vers : 255

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaxi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne shi kaxai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maxaukaki Mai girma



Sure: Suratul Baqara

Vers : 256

لَآ إِكۡرَاهَ فِي ٱلدِّينِۖ قَد تَّبَيَّنَ ٱلرُّشۡدُ مِنَ ٱلۡغَيِّۚ فَمَن يَكۡفُرۡ بِٱلطَّـٰغُوتِ وَيُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱسۡتَمۡسَكَ بِٱلۡعُرۡوَةِ ٱلۡوُثۡقَىٰ لَا ٱنفِصَامَ لَهَاۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Babu tilastawa a addini, haqiqa shiriya ta riga ta bayyana daban da vata. Don haka duk wanda ya kafirce wa Xagutu, kuma ya yi imani da Allah, to haqiqa ya yi riqo da igiya mafi qarfi wadda ba ta tsinkewa. Kuma Allah Mai ji ne, Masani



Sure: Suratul Baqara

Vers : 257

ٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّـٰغُوتُ يُخۡرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَٰتِۗ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Allah Shi ne Majivincin lamarin waxanda suka yi imani, Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske; waxanda suka kafirce kuwa, majivinta lamarinsu su ne xagutai, suna fitar da su daga haske zuwa duffai. Waxannan su ne ‘yan wuta; su masu dawwama ne a cikinta



Sure: Suratul Baqara

Vers : 258

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِي حَآجَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ فِي رَبِّهِۦٓ أَنۡ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُ ٱلۡمُلۡكَ إِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّيَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ قَالَ أَنَا۠ أُحۡيِۦ وَأُمِيتُۖ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَأۡتِي بِٱلشَّمۡسِ مِنَ ٱلۡمَشۡرِقِ فَأۡتِ بِهَا مِنَ ٱلۡمَغۡرِبِ فَبُهِتَ ٱلَّذِي كَفَرَۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Shin ba ka ga wanda ya yi jayayya da Ibrahim ba game da lamarin Ubangijinsa, don Allah ya ba shi mulki, yayin da Ibrahimu ya ce: “Ubangijina Shi ne Yake rayawa, kuma Yake kashewa.” Sai ya ce: “Ai ni ma ina rayawa, kuma ina kashewa.” Sai Ibrahim ya ce: “To Allah Yana kawo rana daga gabas, to kai ka kawo ta daga yamma.” Sai wanda ya kafirta ya kixime. Kuma Allah ba Ya shiryar da azzaluman mutane



Sure: Suratul Baqara

Vers : 259

أَوۡ كَٱلَّذِي مَرَّ عَلَىٰ قَرۡيَةٖ وَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا قَالَ أَنَّىٰ يُحۡيِۦ هَٰذِهِ ٱللَّهُ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۖ فَأَمَاتَهُ ٱللَّهُ مِاْئَةَ عَامٖ ثُمَّ بَعَثَهُۥۖ قَالَ كَمۡ لَبِثۡتَۖ قَالَ لَبِثۡتُ يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۖ قَالَ بَل لَّبِثۡتَ مِاْئَةَ عَامٖ فَٱنظُرۡ إِلَىٰ طَعَامِكَ وَشَرَابِكَ لَمۡ يَتَسَنَّهۡۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰ حِمَارِكَ وَلِنَجۡعَلَكَ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِۖ وَٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡعِظَامِ كَيۡفَ نُنشِزُهَا ثُمَّ نَكۡسُوهَا لَحۡمٗاۚ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُۥ قَالَ أَعۡلَمُ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Ko kuma kamar mutumin da ya wuce ta wata alqarya alhalin ta zama kango, sai ya ce: “Ta yaya Allah zai raya wannan bayan mutuwarta?” Sai Allah Ya karvi rayuwarsa tsawon shekara xari, sannan Ya tashe shi, Ya ce: “Mene ne tsawon lokacin da ka zauna?” Sai ya ce: “Ai na zauna yini xaya ne ko ma wani sashi na yinin.” Sai Ya ce: “Ai ka zauna tsawon shekara xari ne, don haka dubi abincinka da abin shanka bai canja ba, kuma ka dubi jakinka mana, don Mu sanya ka ka zamanto aya ga mutane, kuma ka dubi qasusuwan ka gani yadda za Mu haxa su, sannan Mu lulluve su da nama.”To lokacin da komai ya bayyana a gare shi, sai ya ce: “Na sani lalle Allah Mai iko ne a kan komai.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 260

وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ أَرِنِي كَيۡفَ تُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ قَالَ أَوَلَمۡ تُؤۡمِنۖ قَالَ بَلَىٰ وَلَٰكِن لِّيَطۡمَئِنَّ قَلۡبِيۖ قَالَ فَخُذۡ أَرۡبَعَةٗ مِّنَ ٱلطَّيۡرِ فَصُرۡهُنَّ إِلَيۡكَ ثُمَّ ٱجۡعَلۡ عَلَىٰ كُلِّ جَبَلٖ مِّنۡهُنَّ جُزۡءٗا ثُمَّ ٱدۡعُهُنَّ يَأۡتِينَكَ سَعۡيٗاۚ وَٱعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٞ

Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka nuna mini yadda Kake rayar da matattu.” Sai ya ce: “Shin ko ba ka yi imani ba ne?” Ya ce: “A’a, (na yi imani), sai dai ina son zuciyata ta qara samun nutsuwa.” Sai Ya ce: “To ka kama tsuntsaye huxu ka tara su wajenka, sannan ka sanya yanka xaya-xaya nasu a kan kowane saman dutse, sannan ka kira su; za su zo maka da gaggawa. Kuma ka sani cewa lalle Allah Mabuwayi ne, Mai hikima.”



Sure: Suratul Baqara

Vers : 261

مَّثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنۢبَتَتۡ سَبۡعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنۢبُلَةٖ مِّاْئَةُ حَبَّةٖۗ وَٱللَّهُ يُضَٰعِفُ لِمَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ

Misalin waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, kamar misalin qwaya xaya ce da ta fitar da zangarniya bakwai, a cikinta kowace zangarniya kuma (aka sami) qwaya xari. Kuma Allah Yana ninninkawa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani



Sure: Suratul Baqara

Vers : 262

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ لَا يُتۡبِعُونَ مَآ أَنفَقُواْ مَنّٗا وَلَآ أَذٗى لَّهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, sannan ba sa bin abin da suka ciyar da gori ko cuta, (waxannan) suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Sure: Suratul Baqara

Vers : 263

۞قَوۡلٞ مَّعۡرُوفٞ وَمَغۡفِرَةٌ خَيۡرٞ مِّن صَدَقَةٖ يَتۡبَعُهَآ أَذٗىۗ وَٱللَّهُ غَنِيٌّ حَلِيمٞ

Kyakkyawar magana da yafiya sun fi sadakar da cutarwa za ta biyo bayanta alheri. Kuma Allah Shi ne Wadatacce, Mai haquri



Sure: Suratul Baqara

Vers : 264

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُبۡطِلُواْ صَدَقَٰتِكُم بِٱلۡمَنِّ وَٱلۡأَذَىٰ كَٱلَّذِي يُنفِقُ مَالَهُۥ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۖ فَمَثَلُهُۥ كَمَثَلِ صَفۡوَانٍ عَلَيۡهِ تُرَابٞ فَأَصَابَهُۥ وَابِلٞ فَتَرَكَهُۥ صَلۡدٗاۖ لَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّمَّا كَسَبُواْۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku vata sadaqoqinku da gori da cutarwa, kamar wanda yake ciyar da dukiyarsa don mutane su gani, kuma ba ya imani da Allah da ranar lahira; to misalinsa kamar misalin kamfa ne da turvaya take a kansa sai ruwan sama mamako ya same shi, sai ya bar shi tatas. Ba za su amfana da komai daga abin da suka aikata ba. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai



Sure: Suratul Baqara

Vers : 265

وَمَثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمُ ٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِ ٱللَّهِ وَتَثۡبِيتٗا مِّنۡ أَنفُسِهِمۡ كَمَثَلِ جَنَّةِۭ بِرَبۡوَةٍ أَصَابَهَا وَابِلٞ فَـَٔاتَتۡ أُكُلَهَا ضِعۡفَيۡنِ فَإِن لَّمۡ يُصِبۡهَا وَابِلٞ فَطَلّٞۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Kuma misalin waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu don neman yardar Allah da tabbatar da (imani) a zukatansu, kamar misalin gona ce a kan jigawa sai ruwan sama mamako ya same ta, sai ta ba da amfaninta rivi-biyu. To idan mamakon ruwan bai same ta ba, sai yayyafi (ya wadatar da ita). Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Sure: Suratul Baqara

Vers : 266

أَيَوَدُّ أَحَدُكُمۡ أَن تَكُونَ لَهُۥ جَنَّةٞ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَابٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ لَهُۥ فِيهَا مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ وَأَصَابَهُ ٱلۡكِبَرُ وَلَهُۥ ذُرِّيَّةٞ ضُعَفَآءُ فَأَصَابَهَآ إِعۡصَارٞ فِيهِ نَارٞ فَٱحۡتَرَقَتۡۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُمۡ تَتَفَكَّرُونَ

Shin yanzu xayanku zai yi fatan a ce yana da wata gona ta itacen dabino da kuma inabai, wadda qoramu suke gudana a qarqashinta, yana da dukkan wasu nau’uka na ‘ya’yan itace a cikinta, sai kuma girma ya kama shi, kuma ga shi yana da yara raunana, sai kuma wata irin guguwa mai xauke da wuta ta same ta, sai (gonar gaba xaya) ta qone? Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi don ku riqa yin tunani



Sure: Suratul Baqara

Vers : 267

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا كَسَبۡتُمۡ وَمِمَّآ أَخۡرَجۡنَا لَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِۖ وَلَا تَيَمَّمُواْ ٱلۡخَبِيثَ مِنۡهُ تُنفِقُونَ وَلَسۡتُم بِـَٔاخِذِيهِ إِلَّآ أَن تُغۡمِضُواْ فِيهِۚ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ حَمِيدٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku ciyar daga daxaxan abin da kuka tsuwurwuta da kuma abin da muka fitar muku shi daga cikin qasa, kuma kar ku nufaci mummuna daga cikinsa ku ce daga gare shi ne za ku ciyar, alhalin ku ma kanku (idan an ba ku) ba za ku karve shi ba sai kun runtse idanu. Kuma ku sani cewa lalle Allah Mawadaci ne, Sha-yabo



Sure: Suratul Baqara

Vers : 268

ٱلشَّيۡطَٰنُ يَعِدُكُمُ ٱلۡفَقۡرَ وَيَأۡمُرُكُم بِٱلۡفَحۡشَآءِۖ وَٱللَّهُ يَعِدُكُم مَّغۡفِرَةٗ مِّنۡهُ وَفَضۡلٗاۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Shaixan ne yake tsoratar da ku da talauci, kuma yana umartar ku da alfasha; Allah kuwa Yana yi muku alqawarin gafara ta musamman daga gare Shi da kuma falala. Kuma Allah Mai yalwa ne, Masani



Sure: Suratul Baqara

Vers : 269

يُؤۡتِي ٱلۡحِكۡمَةَ مَن يَشَآءُۚ وَمَن يُؤۡتَ ٱلۡحِكۡمَةَ فَقَدۡ أُوتِيَ خَيۡرٗا كَثِيرٗاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Yana bayar da hikima ga wanda Ya ga dama; kuma dukkan wanda aka bai wa hikima, to haqiqa an ba shi alheri mai tarin yawa. Kuma ba wanda yake wa’azantuwa sai ma’abota hankula



Sure: Suratul Baqara

Vers : 270

وَمَآ أَنفَقۡتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوۡ نَذَرۡتُم مِّن نَّذۡرٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُهُۥۗ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٍ

Kuma abin da kuka ciyar na abin ciyarwa ko kuka yi alwashi na bakance, to lalle Allah Yana sane da shi. Kuma azzalumai ba su da waxansu mataimaka