Sure: Suratul A’araf

Vers : 181

وَمِمَّنۡ خَلَقۡنَآ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ

Kuma akwai wata al’umma daga cikin waxanda Muka halitta suna shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke adalci



Sure: Suratul A’araf

Vers : 182

وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ

Kuma waxanda suka qaryata ayoyinmu, za Mu yi musu talala ta inda ba su sani ba



Sure: Suratul A’araf

Vers : 183

وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ

Kuma Ina yi musu jinkiri ne; lalle kaidina mai qarfi ne



Sure: Suratul A’araf

Vers : 184

أَوَلَمۡ يَتَفَكَّرُواْۗ مَا بِصَاحِبِهِم مِّن جِنَّةٍۚ إِنۡ هُوَ إِلَّا نَذِيرٞ مُّبِينٌ

Shin ba za su yi tunani ba. Lalle abokin nasu fa babu hauka a tattare da shi. Ba kowa ne shi ba, face mai gargaxi, mai bayyanarwa?



Sure: Suratul A’araf

Vers : 185

أَوَلَمۡ يَنظُرُواْ فِي مَلَكُوتِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ وَأَنۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَدِ ٱقۡتَرَبَ أَجَلُهُمۡۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ

Shin ba za su yi duba cikin mulkin sammai da qasa da kuma abin da Allah Ya halitta ba, kuma lalle ya kusata a ce ajalinsu yana gab da zuwa, to da wane zance ne za su yi imani bayansa (wato Alqur’ani)?



Sure: Suratul A’araf

Vers : 186

مَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَلَا هَادِيَ لَهُۥۚ وَيَذَرُهُمۡ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ

Wanda duk Allah Ya vatar, to ba shi da mai shiryar da shi. Kuma zai qyale su a cikin qetare iyakar da suke yi suna ximuwa



Sure: Suratul A’araf

Vers : 187

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّيۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقۡتِهَآ إِلَّا هُوَۚ ثَقُلَتۡ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا تَأۡتِيكُمۡ إِلَّا بَغۡتَةٗۗ يَسۡـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِيٌّ عَنۡهَاۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Suna tambayar ka game da tashin alqiyama yaushe ne matabbatarta take? Ka ce: “Sanin lokacinta yana wajen Ubangijina; ba mai bayyanar da lokacinta sai Shi. Ta yi nauyi a cikin sammai da qasa. Ba za ta zo muku ba sai katsahan.” Suna tambayar ka kamar ka nace a kanta, ka ce: “Iliminta yana wajen Allah kaxai”, sai dai da yawa daga cikin mutane ba su sani ba



Sure: Suratul A’araf

Vers : 188

قُل لَّآ أَمۡلِكُ لِنَفۡسِي نَفۡعٗا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ وَلَوۡ كُنتُ أَعۡلَمُ ٱلۡغَيۡبَ لَٱسۡتَكۡثَرۡتُ مِنَ ٱلۡخَيۡرِ وَمَا مَسَّنِيَ ٱلسُّوٓءُۚ إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٞ وَبَشِيرٞ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Ka ce, “Ba na iya mallakar wa kaina wani amfani, ko wata cuta sai abin da Allah Ya ga dama. Kuma in da na kasance na san gaibu, lalle da na yawaita alheri, da kuma wani mummunan abu bai shafe ni ba. Ni ba wani ne ba face mai gargaxi mai bushara ga mutanen da suke yin imani.”



Sure: Suratul A’araf

Vers : 189

۞هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ وَجَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا لِيَسۡكُنَ إِلَيۡهَاۖ فَلَمَّا تَغَشَّىٰهَا حَمَلَتۡ حَمۡلًا خَفِيفٗا فَمَرَّتۡ بِهِۦۖ فَلَمَّآ أَثۡقَلَت دَّعَوَا ٱللَّهَ رَبَّهُمَا لَئِنۡ ءَاتَيۡتَنَا صَٰلِحٗا لَّنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Shi ne Wanda Ya halicce ku daga rai guda xaya, kuma Ya halicci matarsa daga gare shi, don ya sami nutsuwa tare da ita; to yayin da ya kusance ta, sai ta xauki yaron ciki, sai ta ci gaba (da harkokinta) da shi, to yayin da (cikin) ya yi nauyi, sai suka roqi Allah Ubangijinsu cewa: “Lalle idan Ka ba mu xa lafiyayye[1], lalle za mu kasance masu godiya.”


1- Watau lafiyayye kuma nagari.


Sure: Suratul A’araf

Vers : 190

فَلَمَّآ ءَاتَىٰهُمَا صَٰلِحٗا جَعَلَا لَهُۥ شُرَكَآءَ فِيمَآ ءَاتَىٰهُمَاۚ فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

To yayin da Ya ba su[1] xa lafiyayye, sai suka sanya masa abubuwan tarayya cikin abin da ya ba su. Allah kuwa ya xaukaka ga barin abin da suke shirka da Shi


1- Watau ana nufin cikin zuriyyar Adamu da Hauwa’u waxanda suka riqa yi wa Allah kishiyoyi bayan ni’imar da ya yi musu.


Sure: Suratul A’araf

Vers : 191

أَيُشۡرِكُونَ مَا لَا يَخۡلُقُ شَيۡـٔٗا وَهُمۡ يُخۡلَقُونَ

Shin sa riqa haxa (Allah) da abin da ba ya halittar komai, hasali ma su ne ake halitta?



Sure: Suratul A’araf

Vers : 192

وَلَا يَسۡتَطِيعُونَ لَهُمۡ نَصۡرٗا وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ

Kuma ba za su iya taimaka musu ba, ba kuma za su iya taimaka wa kawunansu ba?



Sure: Suratul A’araf

Vers : 193

وَإِن تَدۡعُوهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ لَا يَتَّبِعُوكُمۡۚ سَوَآءٌ عَلَيۡكُمۡ أَدَعَوۡتُمُوهُمۡ أَمۡ أَنتُمۡ صَٰمِتُونَ

Kuma in da za ku kirawo su zuwa shiriya, to lalle ba za su bi ku ba. Duk xaya ne a gare ku kun kirawo su, ko kuma kun yi shiru?



Sure: Suratul A’araf

Vers : 194

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمۡثَالُكُمۡۖ فَٱدۡعُوهُمۡ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Lalle waxanda kuke kira ba Allah ba bayi ne kamarku, to ku kirawo su mana, sai su kuma su amsa muku idan kun kasance masu gaskiya ne



Sure: Suratul A’araf

Vers : 195

أَلَهُمۡ أَرۡجُلٞ يَمۡشُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ أَيۡدٖ يَبۡطِشُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ أَعۡيُنٞ يُبۡصِرُونَ بِهَآۖ أَمۡ لَهُمۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۗ قُلِ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ كِيدُونِ فَلَا تُنظِرُونِ

Shin wai suna da qafafun da suke tafiya da su ne; ko suna da hannayen da suke damqa da su, ko kuma suna da wasu idanuwa da suke gani da su; ko suna da wasu kunnuwa da suke saurare da su? Ka ce: “Ku kirawo abokan tarayyarku, sannan ku shirya mini makirci kuma kada ku saurara mini.”



Sure: Suratul A’araf

Vers : 196

إِنَّ وَلِـِّۧيَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡكِتَٰبَۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى ٱلصَّـٰلِحِينَ

“Lalle Majivincin lamarina Shi ne Allah Wanda Ya saukar da Littafi; kuma Shi Yake jivintar lamarin salihan bayi.”



Sure: Suratul A’araf

Vers : 197

وَٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَكُمۡ وَلَآ أَنفُسَهُمۡ يَنصُرُونَ

Waxanda kuke kira ba Shi ba kuwa, ba za su iya taimakon ku ba, kuma ba za su iya taimaka wa kawunansu ba



Sure: Suratul A’araf

Vers : 198

وَإِن تَدۡعُوهُمۡ إِلَى ٱلۡهُدَىٰ لَا يَسۡمَعُواْۖ وَتَرَىٰهُمۡ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ وَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ

Kuma idan da za ku yi kiran su zuwa ga shiriya, to fa ba za su ji ba; kuma za ka gan su suna kallon ka, alhali kuwa ba sa gani



Sure: Suratul A’araf

Vers : 199

خُذِ ٱلۡعَفۡوَ وَأۡمُرۡ بِٱلۡعُرۡفِ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡجَٰهِلِينَ

Ka yi riqo da afuwa, kuma ka yi umarni da kyakkyawan abu, ka kuma kawar da kai daga wawaye



Sure: Suratul A’araf

Vers : 200

وَإِمَّا يَنزَغَنَّكَ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ نَزۡغٞ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Idan wani tunzuri daga Shaixan ya tunzura ka, to ka nemi tsarin Allah. Lalle Shi Mai ji ne, Masani



Sure: Suratul A’araf

Vers : 201

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ إِذَا مَسَّهُمۡ طَـٰٓئِفٞ مِّنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ تَذَكَّرُواْ فَإِذَا هُم مُّبۡصِرُونَ

Lalle waxanda suka kiyaye dokokin Allah, idan wani Shaixan mai sa waswasi ya shafe su, sai su tuna (da Allah), sai ga su suna gani tar



Sure: Suratul A’araf

Vers : 202

وَإِخۡوَٰنُهُمۡ يَمُدُّونَهُمۡ فِي ٱلۡغَيِّ ثُمَّ لَا يُقۡصِرُونَ

‘Yan’uwansu kuwa[1] suna qara kawo musu xauki na vata, sannan su ba sa taqaitawa


1- Su ne shaixanu na mutane da aljanu, suna qara ingiza kafirai cikin vata ba tare da suna gajiya ko qosawa a kan haka ba.


Sure: Suratul A’araf

Vers : 203

وَإِذَا لَمۡ تَأۡتِهِم بِـَٔايَةٖ قَالُواْ لَوۡلَا ٱجۡتَبَيۡتَهَاۚ قُلۡ إِنَّمَآ أَتَّبِعُ مَا يُوحَىٰٓ إِلَيَّ مِن رَّبِّيۚ هَٰذَا بَصَآئِرُ مِن رَّبِّكُمۡ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Kuma idan ba ka kawo musu wata aya ba, sai su ce: “Don me ba ka qirqiro ta ba?” Ka ce: “Ba abin da nake bi sai kawai abin da aka yi min wahayinsa daga Ubangijina. Waxannan hujjoji ne daga Ubangijinku da kuma shiriya da kuma rahama ga mutanen da suke yin imani.”



Sure: Suratul A’araf

Vers : 204

وَإِذَا قُرِئَ ٱلۡقُرۡءَانُ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥ وَأَنصِتُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Kuma idan an karanta Alqur’ani, to ku saurare shi, ku kuma yi tsit, don a ji qan ku



Sure: Suratul A’araf

Vers : 205

وَٱذۡكُر رَّبَّكَ فِي نَفۡسِكَ تَضَرُّعٗا وَخِيفَةٗ وَدُونَ ٱلۡجَهۡرِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ

Kuma ka ambaci (sunan) Ubangijinka a ranka, kana mai qasqantar da kai, kuma kana mai jin tsoro, ba kuma tare da xaga murya ba, safe da yamma, kada kuma ka zamo cikin gafalallu



Sure: Suratul A’araf

Vers : 206

إِنَّ ٱلَّذِينَ عِندَ رَبِّكَ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَيُسَبِّحُونَهُۥ وَلَهُۥ يَسۡجُدُونَۤ۩

Lalle waxanda suke wajen Ubangijinka, ba sa girman kai wajen bautar Sa, kuma suna tsarkake Shi, kuma gare Shi kawai suke yin sujjada