Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 91

قَالُواْ لَن نَّبۡرَحَ عَلَيۡهِ عَٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرۡجِعَ إِلَيۡنَا مُوسَىٰ

Suka ce: “Ba za mu gushe muna duqufa wajen bauta masa ba har sai Musa ya dawo mana.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 92

قَالَ يَٰهَٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذۡ رَأَيۡتَهُمۡ ضَلُّوٓاْ

(Musa) ya ce: “Ya Haruna, me ya hana ka lokacin da ka gan su sun vace?



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 93

أَلَّا تَتَّبِعَنِۖ أَفَعَصَيۡتَ أَمۡرِي

“Ka bi ni (don ka sanar da ni)? Ko kuwa ka sava umarnina ne?”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 94

قَالَ يَبۡنَؤُمَّ لَا تَأۡخُذۡ بِلِحۡيَتِي وَلَا بِرَأۡسِيٓۖ إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقۡتَ بَيۡنَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَلَمۡ تَرۡقُبۡ قَوۡلِي

(Haruna) ya ce: “Ya xan’ummata, kada ka kama mini gemuna, da kuma (gashin) kaina; lalle ni na ji tsoron ka ce (da ni): ‘Ka rarraba kan Banu-Isra’ila, ba ka kuma kiyaye maganata ba.’”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 95

قَالَ فَمَا خَطۡبُكَ يَٰسَٰمِرِيُّ

(Musa) ya ce: “Mene ne lamarinka, ya Samiri?”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 96

قَالَ بَصُرۡتُ بِمَا لَمۡ يَبۡصُرُواْ بِهِۦ فَقَبَضۡتُ قَبۡضَةٗ مِّنۡ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذۡتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتۡ لِي نَفۡسِي

Ya ce: “Na ga abin da ba su gani ba ne[1], sai na xebi danqi daga gurbin (qasar) sawun (goxiyar) Manzon (wato Jibrilu) sannan na watsa ta (a kan xan maraqin). Kamar haka kuwa raina ya qawata mini.”


1- Watau ya ga Mala’ika Jibrilu a kan dokinsa lokacin da ya zo hallaka Fir’auna da jama’arsa.


Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 97

قَالَ فَٱذۡهَبۡ فَإِنَّ لَكَ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَۖ وَإِنَّ لَكَ مَوۡعِدٗا لَّن تُخۡلَفَهُۥۖ وَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ إِلَٰهِكَ ٱلَّذِي ظَلۡتَ عَلَيۡهِ عَاكِفٗاۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِي ٱلۡيَمِّ نَسۡفًا

(Annabi Musa) ya ce: “To sai ka tafi, amma ka tabbatar cewa (sakamakonka) a rayuwar (da za ka yi) shi ne ka riqa cewa ‘la misasa’, (watau ba za ka tavu ba kuma ba za ka tava kowa ba)[1]; kuma lalle kana da qayyadajjen lokaci wanda ba za a sava maka ba; kuma ka dubi ubangijin naka wanda ka duqufa a kansa kana bauta; lalle za mu qona shi sannan tabbas za mu sheqar da shi cikin kogi.”


1- Watau ba zai iya gauraya da mutane ba; don ba zai iya tava kowa ba, ba kuma wanda zai iya tava jikinsa.


Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 98

إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا

Abin bautarku kawai shi ne Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Ya yalwaci komai da iliminsa



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 99

كَذَٰلِكَ نَقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ مَا قَدۡ سَبَقَۚ وَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ مِن لَّدُنَّا ذِكۡرٗا

Kamar haka ne Muke ba ka labari daga labaran abubuwan da suka riga suka wuce. Haqiqa kuwa Mun ba ka Alqur’ani daga wajenmu



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 100

مَّنۡ أَعۡرَضَ عَنۡهُ فَإِنَّهُۥ يَحۡمِلُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وِزۡرًا

Duk wanda ya bijire masa to lalle zai xauki nauyin zunubi a ranar alqiyama



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 101

خَٰلِدِينَ فِيهِۖ وَسَآءَ لَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ حِمۡلٗا

(Suna) madawwama a cikinsa (zunubin); kayan (zunubi) kuwa ya munana a gare su ranar alqiyama



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 102

يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِۚ وَنَحۡشُرُ ٱلۡمُجۡرِمِينَ يَوۡمَئِذٖ زُرۡقٗا

(Ita ce) ranar da za a busa qaho. Kuma Mu tayar da kafirai a wannan ranar idanuwansu jawur[1]


1- Watau saboda tsananin tsoro da fargaba.


Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 103

يَتَخَٰفَتُونَ بَيۡنَهُمۡ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا عَشۡرٗا

Suna raxa a tsakaninsu (suna cewa): “Ba ku zauna (a qaburburanku) ba face (kwana) goma.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 104

نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذۡ يَقُولُ أَمۡثَلُهُمۡ طَرِيقَةً إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا يَوۡمٗا

Mu Muka fi sanin abin da suke faxi lokacin da wanda ya fi tunani daga cikinsu yake cewa: “Ba ku zauna ba face rana guda.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 105

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسۡفٗا

Suna kuma tambayar ka game da duwatsu, to ka ce (da su): “Ubangijina zai niqe su tilis



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 106

فَيَذَرُهَا قَاعٗا صَفۡصَفٗا

“Sannan Ya bar ta (wato qasar) fili fetal



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 107

لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا

“Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 108

يَوۡمَئِذٖ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُۥۖ وَخَشَعَتِ ٱلۡأَصۡوَاتُ لِلرَّحۡمَٰنِ فَلَا تَسۡمَعُ إِلَّا هَمۡسٗا

A wannan rana ne za su bi mai kira (zuwa matattara), ba mai bauxe masa; kuma (duk) muryoyi su yi qasa-qasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raxa



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 109

يَوۡمَئِذٖ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَرَضِيَ لَهُۥ قَوۡلٗا

A wannan ranar ceto ba ya amfani sai ga wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, kuma Ya yarda da maganarsa



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 110

يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلۡمٗا

(Allah) Yana sane da abin da yake gaba gare su (na ranar alqiyama) da kuma abin da yake bayansu (na ayyukan da suka yi a duniya), su kuwa ba za su kewaye da saninsa ba



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 111

۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا

Kuma dukkanin fuskoki suka qasqanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haqiqa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya tave



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 112

وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا

Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma qwauro



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 113

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا وَصَرَّفۡنَا فِيهِ مِنَ ٱلۡوَعِيدِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ أَوۡ يُحۡدِثُ لَهُمۡ ذِكۡرٗا

Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alqur’ani) Balarabe (watau da harshen Larabci), Muka kuma sarrafa ayoyin gargaxi a cikinsa don su kiyaye dokokin (Allah) ko kuma ya sa su su wa’azantu



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 114

فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا

Kuma fa Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka (daga maganganun kafirai). Kada kuma ka yi garaje da (karatun) Alqur’ani tun kafin a gama yi maka wahayinsa, kuma ka ce: “Ubangiji Ka qara min ilimi.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 115

وَلَقَدۡ عَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ ءَادَمَ مِن قَبۡلُ فَنَسِيَ وَلَمۡ نَجِدۡ لَهُۥ عَزۡمٗا

Kuma haqiqa Mun yi alqawari da Adamu tun da farko (cewa kada ya ci itaciyar da aka hana shi), sai ya manta, sai ba Mu same shi da qarfin quduri ba



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 116

وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ

Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu” sai suka yi sujjadar sai Iblis ne kawai ya qi



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 117

فَقُلۡنَا يَـٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوّٞ لَّكَ وَلِزَوۡجِكَ فَلَا يُخۡرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلۡجَنَّةِ فَتَشۡقَىٰٓ

Sannan Muka ce: “Ya Adamu, lalle wannan maqiyinka ne kai da matarka, to kada (ku yarda) ya fitar da ku daga Aljanna, sai ka wahala



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 118

إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعۡرَىٰ

“Lalle (Allah) Ya yi maka alqawarin ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 119

وَأَنَّكَ لَا تَظۡمَؤُاْ فِيهَا وَلَا تَضۡحَىٰ

“Kuma lalle kai ba za ka ji qishi ba a cikinta, kuma ba za ka ji zafin rana ba.”



Sure: Suratu Xa Ha

Vers : 120

فَوَسۡوَسَ إِلَيۡهِ ٱلشَّيۡطَٰنُ قَالَ يَـٰٓـَٔادَمُ هَلۡ أَدُلُّكَ عَلَىٰ شَجَرَةِ ٱلۡخُلۡدِ وَمُلۡكٖ لَّا يَبۡلَىٰ

Sai Shaixan ya yi masa waswasi ya ce: “Ya Adamu, yanzu ba na nuna maka wata bishiya ta dawwama da kuma mulki wanda ba zai qare ba?”