أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا
Ya fitar da ruwanta da makiyayarta daga gare ta
وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا
Duwatsu kuma Ya kafa su
مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Don jin daxinku da na dabbobinku
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Sannan idan mafi girman busar qaho ta zo (watau busa ta biyu)
يَوۡمَ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ
A ranar da mutum zai tuna abin da ya aikata
وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ
Aka kuma bayyana (wutar) Jahimu ga kowane mai gani
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ
To (a wannan ranar) duk wanda ya yi xagawa
وَءَاثَرَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Ya kuma fifita rayuwar duniya
فَإِنَّ ٱلۡجَحِيمَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ
To lalle (wutar) Jahimu ita ce makoma
وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ
Duk wanda kuma ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijinsa, ya kuma hana zuciya bin abin da take so
فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ
To lalle Aljanna ita ce makoma
يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَا
Suna tambayar ka game da alqiyama, yaushe ne lokacinta?
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَآ
Me ya gama ka da ambaton lokacinta?
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ
Zuwa ga Ubangijinka ne iyakacin saninta yake[1]
1- Watau Allah ne kaxai ya san lokacin aukuwarta.
إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخۡشَىٰهَا
Kai dai kawai mai gargaxin wanda yake tsoron ta ne
كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَهَا لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا عَشِيَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا
Kai ka ce su ranar da za su gan ta ba su zauna ba (a duniya) face wani yammaci ko kuma hantsinta