إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا
Lalle masu taqawa suna da babban rabo
حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبٗا
(Su ne) gonaki da inabai
وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابٗا
Da ‘yan mata tsaraiku
وَكَأۡسٗا دِهَاقٗا
Da kofin (giya) cikakke
لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا كِذَّـٰبٗا
Ba sa jin maganar banza a cikinta ko kuma qarya
جَزَآءٗ مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابٗا
Sakamako ne daga Ubangijinka, kyauta ce a lissafe (gwargwadon aikin kowa)
رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابٗا
Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu (watau Allah) Mai rahama; (halittu) ba sa samun ikon yi masa magana daga gare Shi
يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ صَفّٗاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابٗا
Ranar da Jibrilu da mala’iku za su tsaya sahu-sahu; (halittu) ba sa iya magana sai fa wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, ya kuma faxi abin da ya dace[1]
1- Watau kalmar tauhidi.
ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا
Wannan rana ce tabbatacciya; saboda haka wanda ya ga dama sai ya riqi kyakkyawar makoma zuwa ga Ubangijinsa
إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابٗا قَرِيبٗا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا
Lalle Mun yi muku gargaxin azaba ta kurkusa, a ranar da mutum zai ga abin da hannayensa suka gabatar (na alheri ko na sharri), kafiri kuma ya riqa cewa: “Ina ma da na zama turvaya[1]!”
1- Watau kamar sauran dabbobi da za a ce musu su zama turvaya.