Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 31

إِن تَجۡتَنِبُواْ كَبَآئِرَ مَا تُنۡهَوۡنَ عَنۡهُ نُكَفِّرۡ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَنُدۡخِلۡكُم مُّدۡخَلٗا كَرِيمٗا

Idan har kun nisanci manya-manyan laifuffukan da aka hana ku, to za Mu kankare muku qananan kurakuranku, kuma za Mu shigar da ku wata mashiga ta karamci



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 32

وَلَا تَتَمَنَّوۡاْ مَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بِهِۦ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبُواْۖ وَلِلنِّسَآءِ نَصِيبٞ مِّمَّا ٱكۡتَسَبۡنَۚ وَسۡـَٔلُواْ ٱللَّهَ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

Kuma kada ku yi burin abin da Allah Ya fifita wasunku a kan wasu da shi, maza suna da kaso na abin da suka tsuwurwurta, haka mata ma suna da kaso na abin da suka tsuwurwurta. Kuma ku roqi Allah daga falalarsa. Lalle Allah Ya kasance Masanin komai ne



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 33

وَلِكُلّٖ جَعَلۡنَا مَوَٰلِيَ مِمَّا تَرَكَ ٱلۡوَٰلِدَانِ وَٱلۡأَقۡرَبُونَۚ وَٱلَّذِينَ عَقَدَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَـَٔاتُوهُمۡ نَصِيبَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا

Kuma kowa Mun sanya masa magadansa daga abin da mahaifa suka bari ko dangi mafiya kusanci[1]. Su kuma waxanda rantsuwar qulla (zumunci) ta haxa tsakaninku, to ku ba su rabonsu[2]. Lalle Allah Ya kasance Mai tsinkaye ne a kan komai


1- Ana nufin masu cin gado ta hanyar asibci.


2- An shafe wannan hukuncin da aya ta 75 ta Suratul Anfal.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 34

ٱلرِّجَالُ قَوَّـٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعۡضَهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ وَبِمَآ أَنفَقُواْ مِنۡ أَمۡوَٰلِهِمۡۚ فَٱلصَّـٰلِحَٰتُ قَٰنِتَٰتٌ حَٰفِظَٰتٞ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُۚ وَٱلَّـٰتِي تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهۡجُرُوهُنَّ فِي ٱلۡمَضَاجِعِ وَٱضۡرِبُوهُنَّۖ فَإِنۡ أَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُواْ عَلَيۡهِنَّ سَبِيلًاۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيّٗا كَبِيرٗا

Maza su ne tsayayyu a kan mata saboda abin da Allah Ya fifita sashinsu da shi a kan sashi, kuma saboda abin da suka ciyar na dukiyarsu. To salihan mata masu xa’a ne, masu tsare (haqqoqin mazajensu) ne a bayan idon mazajensu da tsarewar Allah. Waxanda kuwa kuke jin tsoron kangarewarsu, to ku yi musu wa’azi, kuma ku qaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke su[1]; amma idan sun yi muku xa’a, to kada ku nemi wata hanyar cutar da su. Lalle Allah Ya kasance Maxaukaki ne, Mai girma


1- Watau duka wanda ba zai raunana jiki ba. Wannan mataki zai zo ne bayan duk wasu matakai na ladabtarwa sun ci tura, sannan kuma ana da qwaqqwaran zaton cewa hakan zai wanzar da zaman lafiya tsakanin ma'aurata. Annabi () bai tava dukan matarsa ko bawansa ba tunda yake.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 35

وَإِنۡ خِفۡتُمۡ شِقَاقَ بَيۡنِهِمَا فَٱبۡعَثُواْ حَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهِۦ وَحَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصۡلَٰحٗا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيۡنَهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرٗا

Kuma idan kun ji tsoron ci gaba da samun savani a tsakaninsu, to sai ku aika da wani mai hukunci daga danginsa (mijin), da wani mai hukunci daga danginta (matar), in (su mahukuntan) suna nufin samar da gyara, to Allah zai daidaita tsakaninsu (ma’auratan). Lalle Allah Ya kasance Mai yawan sani ne Masanin abin da yake voye



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 36

۞وَٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗا وَبِذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡجَارِ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡجَارِ ٱلۡجُنُبِ وَٱلصَّاحِبِ بِٱلۡجَنۢبِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخۡتَالٗا فَخُورًا

Kuma ku bauta wa Allah (Shi kaxai), kada ku haxa Shi da komai; kuma ku kyautata wa iyaye da dangi makusanta da marayu da talakawa da maqwabci makusanci da maqwabci na nesa, da abokin da ake tare[1] da kuma matafiyi da bayinku. Lalle Allah ba Ya son duk wanda ya kasance mai taqama, mai yawan fariya


1- Watau wanda tafiya ta haxa mutun da shi ko kuma matarsa.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 37

ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ وَيَأۡمُرُونَ ٱلنَّاسَ بِٱلۡبُخۡلِ وَيَكۡتُمُونَ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَأَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابٗا مُّهِينٗا

Su ne waxanda suke rowa kuma suke umartar mutane da rowa kuma suke voye abin da Allah Ya ba su na falalarsa. Mun kuwa yi tanadin azaba mai wulaqantarwa ga kafirai



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 38

وَٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ رِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَلَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ وَمَن يَكُنِ ٱلشَّيۡطَٰنُ لَهُۥ قَرِينٗا فَسَآءَ قَرِينٗا

Waxanda kuma suke ciyar da dukiyoyinsu don mutane su gani, kuma ba sa yin imani da Allah, ba sa kuma yin imani da ranar qarshe. Duk wanda Shaixan ya kasance shi ne abokinsa, to tir da aboki irin wannan



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 39

وَمَاذَا عَلَيۡهِمۡ لَوۡ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقَهُمُ ٱللَّهُۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِهِمۡ عَلِيمًا

Kuma me zai cutar da su da a ce sun yi imani da Allah da ranar qarshe, kuma suka ciyar daga abin da Allah Ya arzurta su da shi? Kuma Allah Ya kasance Mai yawan sani ne gare su



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 40

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةٗ يُضَٰعِفۡهَا وَيُؤۡتِ مِن لَّدُنۡهُ أَجۡرًا عَظِيمٗا

Lalle Allah ba Ya zalunci ko da daidai da nauyin jaririyar tururuwa; kuma idan ya kasance aiki ne mai kyau to zai ninka shi, kuma Ya ba da lada mai girma daga wurinsa



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 41

فَكَيۡفَ إِذَا جِئۡنَا مِن كُلِّ أُمَّةِۭ بِشَهِيدٖ وَجِئۡنَا بِكَ عَلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِ شَهِيدٗا

To yaya al’amarin zai kasance idan Muka zo da kowace al’umma tare da mai yi mata shaida, kai kuma Muka zo da kai a matsayin mai shaida kan waxannan al’ummar?



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 42

يَوۡمَئِذٖ يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَعَصَوُاْ ٱلرَّسُولَ لَوۡ تُسَوَّىٰ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضُ وَلَا يَكۡتُمُونَ ٱللَّهَ حَدِيثٗا

A wannan yini ne waxanda suka kafirta kuma suka sava wa Manzo, za su yi burin ina ma a mayar da su qasa, kuma ba za su voye wa Allah wani zance ba



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 43

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَقۡرَبُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمۡ سُكَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعۡلَمُواْ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِي سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغۡتَسِلُواْۚ وَإِن كُنتُم مَّرۡضَىٰٓ أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوۡ جَآءَ أَحَدٞ مِّنكُم مِّنَ ٱلۡغَآئِطِ أَوۡ لَٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمۡ تَجِدُواْ مَآءٗ فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدٗا طَيِّبٗا فَٱمۡسَحُواْ بِوُجُوهِكُمۡ وَأَيۡدِيكُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kusanci salla alhalin kuna cikin maye har sai kun san abin da kuke faxa[1], haka mai janaba, sai dai in masu qetara hanya ne, har sai kun yi wanka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya ko a halin tafiya, ko xaya daga cikinku ya dawo daga bahaya ko kuma kuka sadu da mata kuma ba ku sami ruwa ba, to sai ku nufi doron qasa mai tsarki ku yi taimama, sai ku shafi fuskokinku da hannayenku. Lalle Allah Ya kasance Mai afuwa ne, Mai gafara


1- Wannan ayar an shafe ta da ayar haramta shan giya baki xaya da ke cikin Suratun Ma’idah, aya ta 90.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 44

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يَشۡتَرُونَ ٱلضَّلَٰلَةَ وَيُرِيدُونَ أَن تَضِلُّواْ ٱلسَّبِيلَ

Shin ba ka ga waxannan da aka ba su wani rabo na ilimin Littafi ba, suna sayen vata, kuma suna nufin su ga kun vace daga kan hanya?



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 45

وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِأَعۡدَآئِكُمۡۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَلِيّٗا وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ نَصِيرٗا

Allah kuma Shi ne mafi sanin maqiyanku. Kuma Allah Ya isa Ya zama majivinci (gare ku), kuma Ya isa Ya zama Mai taimako (gare ku)



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 46

مِّنَ ٱلَّذِينَ هَادُواْ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَيَقُولُونَ سَمِعۡنَا وَعَصَيۡنَا وَٱسۡمَعۡ غَيۡرَ مُسۡمَعٖ وَرَٰعِنَا لَيَّۢا بِأَلۡسِنَتِهِمۡ وَطَعۡنٗا فِي ٱلدِّينِۚ وَلَوۡ أَنَّهُمۡ قَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَا وَٱسۡمَعۡ وَٱنظُرۡنَا لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۡ وَأَقۡوَمَ وَلَٰكِن لَّعَنَهُمُ ٱللَّهُ بِكُفۡرِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُونَ إِلَّا قَلِيلٗا

Cikin waxanda suka zama Yahudawa akwai waxanda suke juyar da kalmomi daga bigirensu, kuma suna cewa: “Mun ji, kuma mun sava, kuma ka saurara, kai ba abin a saurare ka ba ne, kuma ‘ra’ina’.”[1] Suna masu karkatar da harashensu kuma don su soki addini. Da za su ce: “Mun ji, mun yi xa’a, kuma ka saurare mu, kuma ka jira mu.” da ya kasance mafi alheri gare su, kuma ya fi zama miqaqqiyar (hanya), sai dai Allah Ya riga Ya tsine musu saboda kafircinsu, ba za su yi imani ba sai kaxan


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 104.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 47

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ ءَامِنُواْ بِمَا نَزَّلۡنَا مُصَدِّقٗا لِّمَا مَعَكُم مِّن قَبۡلِ أَن نَّطۡمِسَ وُجُوهٗا فَنَرُدَّهَا عَلَىٰٓ أَدۡبَارِهَآ أَوۡ نَلۡعَنَهُمۡ كَمَا لَعَنَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلسَّبۡتِۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولًا

Ya ku waxanda aka ba su littafi, ku yi imani da abin da Muka saukar mai gaskata abin da yake tare da ku, tun kafin Mu shafe wasu fuskoki, Mu mayar da su bayansu, ko kuma Mu la’ance su irin yadda Muka la’anci ma’abota ranar Asabar[1]. Kuma al’amarin Allah ya kasance abin zartarwa ne


1- Su ne Yahuduwa waxanda Allah ya hana su kamun kifi duk ranar Assabar, amma sai suka riqa yin dabara suna sava wa umarninsa. Duba Suratul A’araf, aya ta 163-166.


Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 48

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغۡفِرُ أَن يُشۡرَكَ بِهِۦ وَيَغۡفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَآءُۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدِ ٱفۡتَرَىٰٓ إِثۡمًا عَظِيمًا

Lalle Allah ba Ya gafarta a yi shirka da Shi, amma Yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda Ya ga dama. Kuma duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa ya qirqiri wani gagarumin laifi



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 49

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يُزَكُّونَ أَنفُسَهُمۚ بَلِ ٱللَّهُ يُزَكِّي مَن يَشَآءُ وَلَا يُظۡلَمُونَ فَتِيلًا

Shin ba ka ganin waxannan da suke tsarkake kawunansu? Ba haka ba ne, Allah ne Yake tsarkake wanda Ya ga dama, kuma ba za a zalunce su ba ko da gwargwadon zaren qwallon dabino ne



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 50

ٱنظُرۡ كَيۡفَ يَفۡتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَۖ وَكَفَىٰ بِهِۦٓ إِثۡمٗا مُّبِينًا

Duba ka ga yadda suke qirqirar qarya su jingina wa Allah; kuma yin haka kaxai ya isa zama wani zunubi mabayyani



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 51

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ نَصِيبٗا مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡجِبۡتِ وَٱلطَّـٰغُوتِ وَيَقُولُونَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ هَـٰٓؤُلَآءِ أَهۡدَىٰ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ سَبِيلًا

Shin ba ka ganin waxanda aka ba su wani rabo na ilimin Littafi, suna yin imani da Jibtu da Xagutu, kuma suna faxa wa waxanda suka kafirta cewa: “Waxannan su suka fi waxanda suka yi imani shiriya.”?



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 52

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَمَن يَلۡعَنِ ٱللَّهُ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ نَصِيرًا

Waxannan su ne waxanda Allah Ya la’ance su; duk kuwa wanda Allah Ya la’anta, to ba za ka tava sama masa wani mataimaki ba



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 53

أَمۡ لَهُمۡ نَصِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُلۡكِ فَإِذٗا لَّا يُؤۡتُونَ ٱلنَّاسَ نَقِيرًا

Shin suna da wani kaso ne na mulki? To da haka ne da kuwa ba za su ba wa mutane ko da gwargwadon xigon bayan dabino ba



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 54

أَمۡ يَحۡسُدُونَ ٱلنَّاسَ عَلَىٰ مَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۖ فَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ ءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَءَاتَيۡنَٰهُم مُّلۡكًا عَظِيمٗا

Shin yanzu za su riqa yi wa mutane hassada ne a kan abin da Allah Ya ba su na falalarsa? To haqiqa Mun bai wa zurriyar gidan Ibrahimu Littafi da kuma hikima, kuma Mun ba su wani mulki mai girma



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 55

فَمِنۡهُم مَّنۡ ءَامَنَ بِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن صَدَّ عَنۡهُۚ وَكَفَىٰ بِجَهَنَّمَ سَعِيرًا

To daga cikinsu akwai wanda ya yi imani da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya bijire masa. Jahannama kuwa ta isa wurin quna



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 56

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا سَوۡفَ نُصۡلِيهِمۡ نَارٗا كُلَّمَا نَضِجَتۡ جُلُودُهُم بَدَّلۡنَٰهُمۡ جُلُودًا غَيۡرَهَا لِيَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَزِيزًا حَكِيمٗا

Lalle waxanda suka kafirce wa ayoyinmu, za Mu shigar da su wata wuta, duk lokacin da fatunsu suka qone, sai Mu musanya musu da wasu fatun daban, don su xanxani azaba. Lalle Allah Ya kasance Mabuwayi ne, Mai hikima



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 57

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَنُدۡخِلُهُمۡ ظِلّٗا ظَلِيلًا

Waxanda suka yi imani kuwa, kuma suka yi aiki nagari, to za Mu shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada; suna da mata tsarkaka a cikinsu; kuma za Mu shigar da su cikin wata inuwa, inuwa mayalwaciya marar gushewa



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 58

۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

Lalle Allah Yana umartar ku da ku mayar da amanoni ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to ku yi hukunci da adalci. Lalle kam madalla da abin da Allah Yake muku wa’azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 59

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ وَأُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنكُمۡۖ فَإِن تَنَٰزَعۡتُمۡ فِي شَيۡءٖ فَرُدُّوهُ إِلَى ٱللَّهِ وَٱلرَّسُولِ إِن كُنتُمۡ تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلًا

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi xa’a ga Allah, kuma ku yi xa’a ga Manzo da kuma majivinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar qarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyan makoma



Sure: Suratun Nisa’i

Vers : 60

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ يَزۡعُمُونَ أَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ يُرِيدُونَ أَن يَتَحَاكَمُوٓاْ إِلَى ٱلطَّـٰغُوتِ وَقَدۡ أُمِرُوٓاْ أَن يَكۡفُرُواْ بِهِۦۖ وَيُرِيدُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَن يُضِلَّهُمۡ ضَلَٰلَۢا بَعِيدٗا

Shin ba ka ganin waxannan da suke riya cewa sun yi imani da abin da aka saukar maka, da abin da aka saukar gabaninka, suna nufin su kai hukunci gaban Xagutu[1] (wanin Allah), alhalin an umarce su da su kafirce masa, Shaixan kuma yana nufin ya vatar da su vata mai nisa?


1- Xagutu, shi ne duk wani abu da bawa zai qetare iyakokin Allah a sanadiyyarsa; mutum ne ko gunki ko wata doka.