Sure: Suratul Ahzab

Vers : 31

۞وَمَن يَقۡنُتۡ مِنكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا نُّؤۡتِهَآ أَجۡرَهَا مَرَّتَيۡنِ وَأَعۡتَدۡنَا لَهَا رِزۡقٗا كَرِيمٗا

Duk kuwa wadda ta yi biyayya ga Allah da Manzonsa daga cikinku ta kuma yi aiki nagari, to za Mu ba ta ladanta sau biyu, kuma Mun tanadar mata arziki mai girma



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 32

يَٰنِسَآءَ ٱلنَّبِيِّ لَسۡتُنَّ كَأَحَدٖ مِّنَ ٱلنِّسَآءِ إِنِ ٱتَّقَيۡتُنَّۚ فَلَا تَخۡضَعۡنَ بِٱلۡقَوۡلِ فَيَطۡمَعَ ٱلَّذِي فِي قَلۡبِهِۦ مَرَضٞ وَقُلۡنَ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

Ya ku matan Annabi, ku fa ba kamar sauran mata kuke ba. Idan kun kiyaye dokokin Allah, to kada ku tausasa murya har yadda wani mai raunin imani a zuciyarsa zai yi kwaxayin (wani abu), kuma ku yi Magana irin maganar da ta dace da shari’a



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 33

وَقَرۡنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجۡنَ تَبَرُّجَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ ٱلۡأُولَىٰۖ وَأَقِمۡنَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتِينَ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِعۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓۚ إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذۡهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجۡسَ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِ وَيُطَهِّرَكُمۡ تَطۡهِيرٗا

Ku kuma zauna a cikin gidajenku, kada kuma ku riqa fita (da bayyana ado) irin ta jahiliyyar farko; ku kuma tsayar da salla, ku ba da zakka, ku kuma bi Allah da Manzonsa. Abin da Allah Yake nufi kawai shi ne Ya kawar muku da duk wata qazanta, ya ku iyalin gidan Annabi, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 34

وَٱذۡكُرۡنَ مَا يُتۡلَىٰ فِي بُيُوتِكُنَّ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ وَٱلۡحِكۡمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا

Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin gidajenku na ayoyin Allah da kuma hikima. Lalle Allah Ya kasance Mai tausayawa ne, Masani



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 35

إِنَّ ٱلۡمُسۡلِمِينَ وَٱلۡمُسۡلِمَٰتِ وَٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ وَٱلۡقَٰنِتِينَ وَٱلۡقَٰنِتَٰتِ وَٱلصَّـٰدِقِينَ وَٱلصَّـٰدِقَٰتِ وَٱلصَّـٰبِرِينَ وَٱلصَّـٰبِرَٰتِ وَٱلۡخَٰشِعِينَ وَٱلۡخَٰشِعَٰتِ وَٱلۡمُتَصَدِّقِينَ وَٱلۡمُتَصَدِّقَٰتِ وَٱلصَّـٰٓئِمِينَ وَٱلصَّـٰٓئِمَٰتِ وَٱلۡحَٰفِظِينَ فُرُوجَهُمۡ وَٱلۡحَٰفِظَٰتِ وَٱلذَّـٰكِرِينَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا وَٱلذَّـٰكِرَٰتِ أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمٗا

Lalle Musulmi maza da Musulmi mata, da muminai maza da muminai mata, da masu biyayya maza da masu biyayya mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haquri maza da masu haquri mata, da masu qasqantar da kai maza da masu qasqantar da kai mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da maza masu kiyaye farjinsu da mata masu kiyaye farjinsu, da maza masu ambaton Allah da yawa da mata masu ambaton Allah (da yawa, dukkaninsu) Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 36

وَمَا كَانَ لِمُؤۡمِنٖ وَلَا مُؤۡمِنَةٍ إِذَا قَضَى ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥٓ أَمۡرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ ٱلۡخِيَرَةُ مِنۡ أَمۡرِهِمۡۗ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلٗا مُّبِينٗا

Bai kamata ga wani mumini ko wata mumina ba, idan Allah da Manzonsa suka yi hukunci a kan wani al’amari su zama suna da wani zavi game da al’amarinsu. Wanda kuwa ya sava wa Allah da Manzonsa, to haqiqa ya vata, bayyanannen vata



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 37

وَإِذۡ تَقُولُ لِلَّذِيٓ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَأَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِ أَمۡسِكۡ عَلَيۡكَ زَوۡجَكَ وَٱتَّقِ ٱللَّهَ وَتُخۡفِي فِي نَفۡسِكَ مَا ٱللَّهُ مُبۡدِيهِ وَتَخۡشَى ٱلنَّاسَ وَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَىٰهُۖ فَلَمَّا قَضَىٰ زَيۡدٞ مِّنۡهَا وَطَرٗا زَوَّجۡنَٰكَهَا لِكَيۡ لَا يَكُونَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ حَرَجٞ فِيٓ أَزۡوَٰجِ أَدۡعِيَآئِهِمۡ إِذَا قَضَوۡاْ مِنۡهُنَّ وَطَرٗاۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولٗا

(Ka tuna) lokacin da kake ce wa wannan da Allah Ya yi wa ni’ima, kai ma ka yi masa ni’ima[1]: “Riqe matarka, kuma ka kiyaye dokokin Allah”, alhali kuwa kana voyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kana kuma tsoron mutane[2], alhali kuma Allah ne Ya fi cancanta ka ji tsoron Sa; to lokacin da Zaidu ya gama buqatarsa da ita (matarsa Zainab), Mun aurar maka ita, don saboda kada ya zama akwai quntatawa ga muminai game da (auren) matan ‘ya’yansu na riqo lokacin da suka gama bukata da su. Al’amarin Allah kuwa ya kasance abin zartarwa ne


1- Shi ne Zaidu xan Harisa da Annabi () ya ‘yanta shi, ya aura masa Zainab ‘yar Jahshi ().


2- Watau tsoron abin da mutane za su riqa faxa na cewa ya auri matar xansa na riqo.


Sure: Suratul Ahzab

Vers : 38

مَّا كَانَ عَلَى ٱلنَّبِيِّ مِنۡ حَرَجٖ فِيمَا فَرَضَ ٱللَّهُ لَهُۥۖ سُنَّةَ ٱللَّهِ فِي ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلُۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قَدَرٗا مَّقۡدُورًا

Babu wani laifi a kan Annabi game da abin da Allah Ya halatta masa; (wannan kuwa) Sunnar Allah ce ga waxanda suka gabace ka (daga annabawa). Al’amarin Allah kuwa ya kasance mai tabbata ne ba makawa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 39

ٱلَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَٰلَٰتِ ٱللَّهِ وَيَخۡشَوۡنَهُۥ وَلَا يَخۡشَوۡنَ أَحَدًا إِلَّا ٱللَّهَۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ حَسِيبٗا

Waxanda suke isar da saqon Allah suke kuma tsoron Sa, ba sa kuwa tsoron kowa sai Allah. Allah kuwa Ya isa Mai yin hisabi



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 40

مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَآ أَحَدٖ مِّن رِّجَالِكُمۡ وَلَٰكِن رَّسُولَ ٱللَّهِ وَخَاتَمَ ٱلنَّبِيِّـۧنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

(Annabi) Muhammadu bai kasance uban xaya daga cikin mazajenku ba, sai dai (shi) ya kasance Manzon Allah ne kuma cikamakin annabawa. Allah kuma Ya kasance Masanin komai ne



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 41

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ ذِكۡرٗا كَثِيرٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 42

وَسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا

Kuma ku yi tasbihi a gare Shi safe da yamma



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 43

هُوَ ٱلَّذِي يُصَلِّي عَلَيۡكُمۡ وَمَلَـٰٓئِكَتُهُۥ لِيُخۡرِجَكُم مِّنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَكَانَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ رَحِيمٗا

Shi ne wanda Yake yi muku salati da mala’ikunsa don Ya fitar da ku daga duffai zuwa haske, Allah kuwa Ya kasance Mai rahama ga muminai



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 44

تَحِيَّتُهُمۡ يَوۡمَ يَلۡقَوۡنَهُۥ سَلَٰمٞۚ وَأَعَدَّ لَهُمۡ أَجۡرٗا كَرِيمٗا

Gaisuwarsu a ranar da za su haxu da Shi (ita ce) ‘Salamun Alaikum’. Ya kuma tanadar musu da lada na karamci



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 45

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Ya kai wannan Annabi, lalle Mu Mun aiko ka kana mai shaida, kuma mai albishir kuma mai gargaxi



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 46

وَدَاعِيًا إِلَى ٱللَّهِ بِإِذۡنِهِۦ وَسِرَاجٗا مُّنِيرٗا

Kuma mai kira zuwa ga Allah da izininsa, kuma fitila mai haskakawa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 47

وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ بِأَنَّ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَضۡلٗا كَبِيرٗا

Ka kuma yi wa muminai albishir cewa, suna da wata falala mai girma daga wurin Allah



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 48

وَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَدَعۡ أَذَىٰهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا

Kada kuma ka yi wa kafirai da munafukai xa’a, ka kuma bar cutarsu (da suke yi maka), ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa Ya zama abin dogara



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 49

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نَكَحۡتُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ فَمَا لَكُمۡ عَلَيۡهِنَّ مِنۡ عِدَّةٖ تَعۡتَدُّونَهَاۖ فَمَتِّعُوهُنَّ وَسَرِّحُوهُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا

Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka auri mata muminai, sannan kuka sake su tun kafin ku sadu da su, to babu wata idda taku a kansu da za ku nemi cikar adadin (kwanakinta); sai ku jiyar da su daxi[1], kuma ku sake su kyakkyawan saki


1- Watau su ba su abin da zai daxaxa musu rai, don ya rage musu raxaxin sakin da aka yi musu.


Sure: Suratul Ahzab

Vers : 50

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِنَّآ أَحۡلَلۡنَا لَكَ أَزۡوَٰجَكَ ٱلَّـٰتِيٓ ءَاتَيۡتَ أُجُورَهُنَّ وَمَا مَلَكَتۡ يَمِينُكَ مِمَّآ أَفَآءَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ وَبَنَاتِ عَمِّكَ وَبَنَاتِ عَمَّـٰتِكَ وَبَنَاتِ خَالِكَ وَبَنَاتِ خَٰلَٰتِكَ ٱلَّـٰتِي هَاجَرۡنَ مَعَكَ وَٱمۡرَأَةٗ مُّؤۡمِنَةً إِن وَهَبَتۡ نَفۡسَهَا لِلنَّبِيِّ إِنۡ أَرَادَ ٱلنَّبِيُّ أَن يَسۡتَنكِحَهَا خَالِصَةٗ لَّكَ مِن دُونِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۗ قَدۡ عَلِمۡنَا مَا فَرَضۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ وَمَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ لِكَيۡلَا يَكُونَ عَلَيۡكَ حَرَجٞۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Ya kai wannan Annabi, lalle Mun halatta maka matanka waxanda ka ba da sadakinsu, da kuma kuyanginka daga abin da Allah Ya ba ka na ganima, da ‘ya’yan baffanka mata da ‘ya’yan gwaggwaninka mata da ‘ya’yan kawunka mata, da ‘ya’yan yagwalgwalanka mata waxanda suka yi hijira tare da kai, da kuma duk wata mace mumina, idan ta ba da kanta ga Annabi (shi) Annabin kuwa yana nufin ya aure ta, (wannan) kevantacce ne a gare ka[1], ban da sauran muminai. Haqiqa Mun san abin da Muka xora musu game da matansu da kuma kuyanginsu, don kada a samu wata quntatawa a kanka. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Allah () ya halatta wa Annabi () auren duk wata mace mumina wadda za ta ba da kanta kyauta a gare shi ba tare da sadaki ba.


Sure: Suratul Ahzab

Vers : 51

۞تُرۡجِي مَن تَشَآءُ مِنۡهُنَّ وَتُـٔۡوِيٓ إِلَيۡكَ مَن تَشَآءُۖ وَمَنِ ٱبۡتَغَيۡتَ مِمَّنۡ عَزَلۡتَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكَۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن تَقَرَّ أَعۡيُنُهُنَّ وَلَا يَحۡزَنَّ وَيَرۡضَيۡنَ بِمَآ ءَاتَيۡتَهُنَّ كُلُّهُنَّۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا فِي قُلُوبِكُمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَلِيمٗا

Ka dakatar da duk wadda ka ga dama daga cikinsu, ka kuma jawo duk wadda ka ga dama[1]; (duk) wadda kuwa ka nema daga waxanda ka dakatar, to babu wani laifi a kanka. (Yin) wannan kuwa shi ya fi kusantar da kwanciyar ransu da kuma rashin yin baqin ciki, su kuma yarda da duk abin da ka ba su dukkansu[2]. Allah kuwa Yana sane da abin da yake cikin zukatanku. Allah kuwa Ya kasance Masani ne, Mai haquri


1- Watau Allah () bai wajabta masa rabon kwana a tsakanin matansa ba, yana iya dakatar da kwanan wadda ya ga dama ko ya jawo da kwananta.


2- Domin sun tabbatar ba zai hana musu haqqoqinsu ba ko ya qi yi musu adalci.


Sure: Suratul Ahzab

Vers : 52

لَّا يَحِلُّ لَكَ ٱلنِّسَآءُ مِنۢ بَعۡدُ وَلَآ أَن تَبَدَّلَ بِهِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجٖ وَلَوۡ أَعۡجَبَكَ حُسۡنُهُنَّ إِلَّا مَا مَلَكَتۡ يَمِينُكَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ رَّقِيبٗا

Bayan (waxannan) wasu mata ba su halatta gare ka ba, ko kuma ka musanya waxansu (matan) da su, ko da kuwa kyansu ya qayatar da kai, sai dai abin da ka mallaka na kuyangi. Allah kuwa Ya kasance Mai lura ne da komai



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 53

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتَ ٱلنَّبِيِّ إِلَّآ أَن يُؤۡذَنَ لَكُمۡ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيۡرَ نَٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَٰكِنۡ إِذَا دُعِيتُمۡ فَٱدۡخُلُواْ فَإِذَا طَعِمۡتُمۡ فَٱنتَشِرُواْ وَلَا مُسۡتَـٔۡنِسِينَ لِحَدِيثٍۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ يُؤۡذِي ٱلنَّبِيَّ فَيَسۡتَحۡيِۦ مِنكُمۡۖ وَٱللَّهُ لَا يَسۡتَحۡيِۦ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ وَإِذَا سَأَلۡتُمُوهُنَّ مَتَٰعٗا فَسۡـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٖۚ ذَٰلِكُمۡ أَطۡهَرُ لِقُلُوبِكُمۡ وَقُلُوبِهِنَّۚ وَمَا كَانَ لَكُمۡ أَن تُؤۡذُواْ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓاْ أَزۡوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعۡدِهِۦٓ أَبَدًاۚ إِنَّ ذَٰلِكُمۡ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku shiga gidajen Annabi sai idan an yi muku izini zuwa (cin) abinci, alhali ba tare da kuna jiran dahuwarsa ba, sai dai kuma idan aka kira ku, to ku shiga, sannan idan kuka ci sai ku fice, ba tare da yin wata hira ta xebe kewa ba. Lalle wannan ya kasance yana cutar Annabi, sai yakan ji kunyar ku; Allah kuwa ba Ya jin kunyar (faxar) gaskiya. Idan kuma za ku tambaye su (wato matan Annabi) wani abu na amfani, sai ku tambaye su ta bayan shamaki. Yin wannan shi ya fi tsarki ga zukatanku da kuma zukatansu. Kuma bai kamace ku ba ku cuci Manzon Allah ko kuma ku auri matansa a bayansa har abada. Lalle (yin) wannan ya kasance abu mai girma a wurin Allah



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 54

إِن تُبۡدُواْ شَيۡـًٔا أَوۡ تُخۡفُوهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٗا

Idan kuma kuka bayyana wani abu ko kuka voye shi, to Allah Ya kasance Masanin komai ne



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 55

لَّا جُنَاحَ عَلَيۡهِنَّ فِيٓ ءَابَآئِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآئِهِنَّ وَلَآ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ إِخۡوَٰنِهِنَّ وَلَآ أَبۡنَآءِ أَخَوَٰتِهِنَّ وَلَا نِسَآئِهِنَّ وَلَا مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّۗ وَٱتَّقِينَ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدًا

Babu laifi a kansu (matan) game da iyayensu maza (su gan su kuma su yi magana da su ba tare da shamaki ba) da kuma ‘ya’yansu maza da ‘ya’uwansu da ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza da ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata, da kuma matansu da bayinsu. Ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Ya kasance Mai ganin komai ne



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 56

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَـٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا

Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama mai yawa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 57

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ لَعَنَهُمُ ٱللَّهُ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَأَعَدَّ لَهُمۡ عَذَابٗا مُّهِينٗا

Lalle waxanda suke cutar Allah da Manzonsa, to Allah Ya la’ance su a duniya da lahira, Ya kuma tanadar musu azaba mai wulaqantarwa



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 58

وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ بِغَيۡرِ مَا ٱكۡتَسَبُواْ فَقَدِ ٱحۡتَمَلُواْ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

Waxanda suke cutar muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to haqiqa sun xauki nauyin qage da kuma zunubi bayyananne



Sure: Suratul Ahzab

Vers : 59

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَآءِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ يُدۡنِينَ عَلَيۡهِنَّ مِن جَلَٰبِيبِهِنَّۚ ذَٰلِكَ أَدۡنَىٰٓ أَن يُعۡرَفۡنَ فَلَا يُؤۡذَيۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Ya kai wannan Annabi, faxa wa matanka da ‘ya’yanka mata da kuma matan muminai (cewa) su sanya lulluvinsu. Wannan shi ya fi sanya wa a gane su[1], don kada a cuce su. Allah kuma Ya kasance Mai gafara ne, Mai rahama


1- Watau a tantance tsakaninsu da mata marasa kamun kai.


Sure: Suratul Ahzab

Vers : 60

۞لَّئِن لَّمۡ يَنتَهِ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡمُرۡجِفُونَ فِي ٱلۡمَدِينَةِ لَنُغۡرِيَنَّكَ بِهِمۡ ثُمَّ لَا يُجَاوِرُونَكَ فِيهَآ إِلَّا قَلِيلٗا

Tabbas munafukai da waxanda suke da raunin imani a zukatansu da kuma masu yaxa qarairayi a Madina, idan ba su bari ba, lalle za Mu cuna ka a kansu (don ka hukunta su), sannan kuma ba za su zauna da kai a cikinta ba sai xan lokaci qanqani