Sure: Suratu Abasa

Vers : 1

عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ

Ya xaure fuska[1], ya kuma ba da baya


1- Shi ne Manzon Allah ().


Sure: Suratu Abasa

Vers : 2

أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ

Don makaho[1] ya zo masa


1- Shi ne Abdullahi xan Ummu Maktum, ya zo yana yi wa Annabi () tambaya a lokacin shi kuma yana qoqarin janyo hankalin shugabannin Quraishawa zuwa ga Musulunci.


Sure: Suratu Abasa

Vers : 3

وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ

Me kuma zai sanar da kai cewa wataqila shi ne zai tsarkaka?



Sure: Suratu Abasa

Vers : 4

أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ

Ko ya wa’azantu, sai wa’azin ya amfane shi?



Sure: Suratu Abasa

Vers : 5

أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ

Amma wanda ya wadatu (daga wa’azinka)



Sure: Suratu Abasa

Vers : 6

فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ

To kai shi kake fuskanta



Sure: Suratu Abasa

Vers : 7

وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ

Babu kuwa komai a kanka don ya qi ya tsarkaka



Sure: Suratu Abasa

Vers : 8

وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ

Amma kuma wanda ya zo maka yana sauri



Sure: Suratu Abasa

Vers : 9

وَهُوَ يَخۡشَىٰ

Alhali kuma shi yana tsoron (Allah)



Sure: Suratu Abasa

Vers : 10

فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ

To kai shi kake kawar wa da kai



Sure: Suratu Abasa

Vers : 11

كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ

Abin ba haka yake ba, lalle (wannan da’awar) wa’azi ne



Sure: Suratu Abasa

Vers : 12

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ

Don haka wanda ya ga dama ya wa’azantu



Sure: Suratu Abasa

Vers : 13

فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ

(Wannan Alqur’ani) yana cikin takardu ababan girmamawa



Sure: Suratu Abasa

Vers : 14

مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ

Maxaukaka, tsarkaka



Sure: Suratu Abasa

Vers : 15

بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ

A hannayen jakadu (mala’iku)



Sure: Suratu Abasa

Vers : 16

كِرَامِۭ بَرَرَةٖ

Manya masu biyayya



Sure: Suratu Abasa

Vers : 17

قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ

An la’anci mutum, me ya kai tsananin kafircinsa!



Sure: Suratu Abasa

Vers : 18

مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ

Shin daga wane abu ne (Allah) Ya halicce shi?



Sure: Suratu Abasa

Vers : 19

مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ

Daga maniyyi ne Ya halicce shi, sannan Ya qaddara shi (matakai a halitta)



Sure: Suratu Abasa

Vers : 20

ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ

Sannan tafarki (na rayuwa) Ya hore masa shi



Sure: Suratu Abasa

Vers : 21

ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ

Sannan Ya kashe shi, sai Ya sa shi cikin qabarinsa



Sure: Suratu Abasa

Vers : 22

ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ

Sannan in Ya ga dama Ya tashe shi



Sure: Suratu Abasa

Vers : 23

كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ

Fafau (zaton mutum) ba haka ne ba, har yanzu bai aikata abin da (Allah) Ya umarce shi ba



Sure: Suratu Abasa

Vers : 24

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ

To mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa mana?



Sure: Suratu Abasa

Vers : 25

أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا

Cewa lalle Mu Muka zubo da ruwan sama zubowa



Sure: Suratu Abasa

Vers : 26

ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا

Sannan Muka tsaga qasa tsagawa



Sure: Suratu Abasa

Vers : 27

فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا

Sai Muka tsiro da qwaya daga cikinta



Sure: Suratu Abasa

Vers : 28

وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا

Da inabai da ciyayi



Sure: Suratu Abasa

Vers : 29

وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا

Da zaitun da dabino



Sure: Suratu Abasa

Vers : 30

وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا

Da gonaki cike da itatuwa