Sure: Suratul Kahf 

Vers : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya saukar wa da Bawansa Littafi, bai kuma sanya masa wata karkata ba



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 2

قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا

Daidaitacce ne, don ya yi gargaxi game da azaba mai tsanani daga gare Shi (wato Allah), ya kuma yi wa muminai waxanda suke aiki nagari albishir cewa suna da lada kyakkyawa



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 3

مَّـٰكِثِينَ فِيهِ أَبَدٗا

Madawwama a cikinsa har abada



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 4

وَيُنذِرَ ٱلَّذِينَ قَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗا

Ya kuma gargaxi waxanda suka ce Allah Yana da xa



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 5

مَّا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٖ وَلَا لِأٓبَآئِهِمۡۚ كَبُرَتۡ كَلِمَةٗ تَخۡرُجُ مِنۡ أَفۡوَٰهِهِمۡۚ إِن يَقُولُونَ إِلَّا كَذِبٗا

Ba su da wani ilimi game da shi (wannan zance) kuma iyayensu ma ba su da (ilimi game da shi). Kalmar da take fitowa daga bakunansu ta yi girma. Ba abin da suke faxa sai qarya



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 6

فَلَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ إِن لَّمۡ يُؤۡمِنُواْ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَسَفًا

To ko mai yiwuwa ne za ka kashe kanka da baqin ciki, in ba su yi imani da wannan zancen ba (watau Alqur’ani)



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 7

إِنَّا جَعَلۡنَا مَا عَلَى ٱلۡأَرۡضِ زِينَةٗ لَّهَا لِنَبۡلُوَهُمۡ أَيُّهُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗا

Lalle Mu Mun sanya abin da yake bayan qasa ya zama ado a gare ta, don (kuma) Mu jarraba su, wane ne daga cikinsu ya fi kyakkyawan aiki?



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 8

وَإِنَّا لَجَٰعِلُونَ مَا عَلَيۡهَا صَعِيدٗا جُرُزًا

Lalle kuma Mu za Mu mai da abin da yake kanta (ya zama) turvaya qeqasasshiya



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 9

أَمۡ حَسِبۡتَ أَنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡكَهۡفِ وَٱلرَّقِيمِ كَانُواْ مِنۡ ءَايَٰتِنَا عَجَبًا

Shin ka yi tsammanin cewa lalle Mutanen Kogo da Raqimu[1] sun kasance daga ayoyinmu masu ban mamaki?


1- An yi savani wajen fassara ma’anar arraqimu. Wasu sun ce sunan dutsen da suka kasance a cikinsa ne; wasu kuma sun ce sunan allon da aka rubuta sunayensu a ciki; wasu kuma sun ce mutanen nan uku ne da suka shiga kogo dutse ya rufe da su.


Sure: Suratul Kahf 

Vers : 10

إِذۡ أَوَى ٱلۡفِتۡيَةُ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ فَقَالُواْ رَبَّنَآ ءَاتِنَا مِن لَّدُنكَ رَحۡمَةٗ وَهَيِّئۡ لَنَا مِنۡ أَمۡرِنَا رَشَدٗا

Lokacin da samarin nan suka fake a Kogon, sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu rahama daga gare Ka, Ka kuma tanadar mana shiriya cikin lamarinmu



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 11

فَضَرَبۡنَا عَلَىٰٓ ءَاذَانِهِمۡ فِي ٱلۡكَهۡفِ سِنِينَ عَدَدٗا

Sai Muka sanya (shamaki) a kan kunnuwansu (suka yi barci) shekaru masu yawa a cikin Kogon



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 12

ثُمَّ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِنَعۡلَمَ أَيُّ ٱلۡحِزۡبَيۡنِ أَحۡصَىٰ لِمَا لَبِثُوٓاْ أَمَدٗا

Sannan Muka tashe su don Mu san wane ne daga qungiyoyin nan biyu (masu savani game da lamarin samarin) ya fi kiyayewa da tsawon zamaninsu?



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 13

نَّحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ نَبَأَهُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّهُمۡ فِتۡيَةٌ ءَامَنُواْ بِرَبِّهِمۡ وَزِدۡنَٰهُمۡ هُدٗى

Mu ne za Mu ba ka labarinsu da gaskiya. Lalle su samari ne da suka yi imani da Ubangijinsu, Muka kuwa qara musu shiriya



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 14

وَرَبَطۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ إِذۡ قَامُواْ فَقَالُواْ رَبُّنَا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَن نَّدۡعُوَاْ مِن دُونِهِۦٓ إِلَٰهٗاۖ لَّقَدۡ قُلۡنَآ إِذٗا شَطَطًا

Muka kuma xaure zukatansu lokacin da suka tsaya suka ce: “Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da qasa; ba za mu bauta wa wani abin bauta ba in ban da Shi; idan muka yi haka kuwa to haqiqa mun faxi qarya



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 15

هَـٰٓؤُلَآءِ قَوۡمُنَا ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةٗۖ لَّوۡلَا يَأۡتُونَ عَلَيۡهِم بِسُلۡطَٰنِۭ بَيِّنٖۖ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا

“Waxannan mutanenmu ne da suka riqi wasu alloli ba Shi ba; me ya hana ba su zo musu da wata hujja mabayyaniya (kan haka) ba? To ba wanda ya fi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah qarya



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 16

وَإِذِ ٱعۡتَزَلۡتُمُوهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ فَأۡوُۥٓاْ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ يَنشُرۡ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَيُهَيِّئۡ لَكُم مِّنۡ أَمۡرِكُم مِّرۡفَقٗا

“Tun da kun qaurace musu tare da abin da suke bauta wa sai Allah, to sai ku tare a kogon, Ubangijinku zai yalwata muku rahamarsa ya kuma shirya muku hanyar rayuwa mai sauqi ga al’amuranku.”



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 17

۞وَتَرَى ٱلشَّمۡسَ إِذَا طَلَعَت تَّزَٰوَرُ عَن كَهۡفِهِمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَإِذَا غَرَبَت تَّقۡرِضُهُمۡ ذَاتَ ٱلشِّمَالِ وَهُمۡ فِي فَجۡوَةٖ مِّنۡهُۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِۗ مَن يَهۡدِ ٱللَّهُ فَهُوَ ٱلۡمُهۡتَدِۖ وَمَن يُضۡلِلۡ فَلَن تَجِدَ لَهُۥ وَلِيّٗا مُّرۡشِدٗا

(Sai) kuma ka ga rana idan za ta vullo tana kauce wa kogonsu ta vangaren dama, idan kuma za ta faxi sai ta riqa kauce musu ta vangaren hagu, su kuwa suna tsakiyarsa. Wannan yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar to shi ne shiryayye, wanda kuwa Ya vatar to ba za ka sami wani majivinci da zai shirye shi ba



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 18

وَتَحۡسَبُهُمۡ أَيۡقَاظٗا وَهُمۡ رُقُودٞۚ وَنُقَلِّبُهُمۡ ذَاتَ ٱلۡيَمِينِ وَذَاتَ ٱلشِّمَالِۖ وَكَلۡبُهُم بَٰسِطٞ ذِرَاعَيۡهِ بِٱلۡوَصِيدِۚ لَوِ ٱطَّلَعۡتَ عَلَيۡهِمۡ لَوَلَّيۡتَ مِنۡهُمۡ فِرَارٗا وَلَمُلِئۡتَ مِنۡهُمۡ رُعۡبٗا

Za kuma ka zaci a farke suke alhali kuwa suna bacci ne. Muka kuma riqa juya su ta varin dama da kuma ta varin hagu; karensu kuwa ya shimfixa qafafunsa na gaba a mashigar kogon. Da abin ka leqa su ne to lalle da ka fita a guje, lalle kuma da ka cika da tsoron su



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 19

وَكَذَٰلِكَ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِيَتَسَآءَلُواْ بَيۡنَهُمۡۚ قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ كَمۡ لَبِثۡتُمۡۖ قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۚ قَالُواْ رَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثۡتُمۡ فَٱبۡعَثُوٓاْ أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمۡ هَٰذِهِۦٓ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ فَلۡيَنظُرۡ أَيُّهَآ أَزۡكَىٰ طَعَامٗا فَلۡيَأۡتِكُم بِرِزۡقٖ مِّنۡهُ وَلۡيَتَلَطَّفۡ وَلَا يُشۡعِرَنَّ بِكُمۡ أَحَدًا

Kamar haka Muka tashe su don su riqa tambayar junansu. Wani mai tambaya daga cikinsu ya ce: “Mene ne tsawon zamanku (a nan)?” Suka ce: “Mun yi zaman yini xaya ne ko kuma rabin yini.” (Sannan kuma) suka ce: “Ubangijinku ne Ya fi sanin tsawon zaman da kuka yi, sai ku aiki xayanku da wannan kuxin naku cikin gari, sai ya duba ya ga wanne irin abinci ne ya fi tsarki, to sai ya zo muku da abin da za ku ci da shi (kuxin), kuma ya yi taka-tsantsan kada wani ya shaida ku



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 20

إِنَّهُمۡ إِن يَظۡهَرُواْ عَلَيۡكُمۡ يَرۡجُمُوكُمۡ أَوۡ يُعِيدُوكُمۡ فِي مِلَّتِهِمۡ وَلَن تُفۡلِحُوٓاْ إِذًا أَبَدٗا

“Lalle idan suka yi galaba a kanku to za su jefe ku ko kuma su mai da ku cikin addininsu, to shi ke nan ba za ku rabauta ba har abada.”



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 21

وَكَذَٰلِكَ أَعۡثَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ لِيَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَأَنَّ ٱلسَّاعَةَ لَا رَيۡبَ فِيهَآ إِذۡ يَتَنَٰزَعُونَ بَيۡنَهُمۡ أَمۡرَهُمۡۖ فَقَالُواْ ٱبۡنُواْ عَلَيۡهِم بُنۡيَٰنٗاۖ رَّبُّهُمۡ أَعۡلَمُ بِهِمۡۚ قَالَ ٱلَّذِينَ غَلَبُواْ عَلَىٰٓ أَمۡرِهِمۡ لَنَتَّخِذَنَّ عَلَيۡهِم مَّسۡجِدٗا

Kamar haka kuwa Muka nuna wa (mutanen nasu) su don su san cewa lalle alqawarin Allah gaskiya ne, kuma ita alqiyama babu kokwanto a cikinta, kuma ka tuna lokacin da su (mutanen) suke ta jayayya a tsakaninsu game da al’amarinsu (watau samarin); sai (wasu daga cikinsu) suka ce: “Ku tayar da gini a kansu (wanda zai toshe qofar kogon).” Ubangijinsu Shi Ya fi sanin lamarinsu. Waxanda suka yi rinjaye kan al’amarinsu suka ce: “Lalle tabbas za mu yi masallaci a kansu (watau a kan qabarinsu)[1].”


1- Wannan magana ce ta masu iko a garin, ba ta masu ilimi ba. Musulunci yah ana gina masallaci a maqabarta ko salla a kan qabari ko ana fuskantar sa.


Sure: Suratul Kahf 

Vers : 22

سَيَقُولُونَ ثَلَٰثَةٞ رَّابِعُهُمۡ كَلۡبُهُمۡ وَيَقُولُونَ خَمۡسَةٞ سَادِسُهُمۡ كَلۡبُهُمۡ رَجۡمَۢا بِٱلۡغَيۡبِۖ وَيَقُولُونَ سَبۡعَةٞ وَثَامِنُهُمۡ كَلۡبُهُمۡۚ قُل رَّبِّيٓ أَعۡلَمُ بِعِدَّتِهِم مَّا يَعۡلَمُهُمۡ إِلَّا قَلِيلٞۗ فَلَا تُمَارِ فِيهِمۡ إِلَّا مِرَآءٗ ظَٰهِرٗا وَلَا تَسۡتَفۡتِ فِيهِم مِّنۡهُمۡ أَحَدٗا

(Wasu) suka riqa cewa su uku ne na huxunsu shi ne karensu; (wasu) kuma suna cewa biyar ne na shidansu ne karensu don lalube cikin duhu; (wasu) kuma suna cewa su bakwai ne na takwas xinsu kuma karensu ne. Ka ce (da su): “Ubangiji Shi Ya fi sanin yawansu, ba wanda ya san lamarinsu sai ‘yan kaxan.” To kada ka yi jayayya game da (al’amarinsu) sai dai a kan abin da yake a fili, kada kuma ka nemi fatawar xaya daga cikinsu game da su (samarin)



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 23

وَلَا تَقُولَنَّ لِشَاْيۡءٍ إِنِّي فَاعِلٞ ذَٰلِكَ غَدًا

Kada kuma ka ce da kowane abu: “Lalle zan aikata wannan gobe.”



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 24

إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَهۡدِيَنِ رَبِّي لِأَقۡرَبَ مِنۡ هَٰذَا رَشَدٗا

Sai dai (tare da cewa): ‘In sha Allah’; ka kuma ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: “Ina fatan Ubangijina Ya nuna mini abin da ya fi wannan zama shiriya.”



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 25

وَلَبِثُواْ فِي كَهۡفِهِمۡ ثَلَٰثَ مِاْئَةٖ سِنِينَ وَٱزۡدَادُواْ تِسۡعٗا

Sun kuwa zauna cikin kogonsu shekara xari uku, suka kuma qara tara[1]


1- A lissafin shekarar shamsiyya, watau lissafi da fitowar rana da faxuwarta shi ne 300. A lissafin qamariyya kuwa, watau lissafin ganin wata shi ne 309.


Sure: Suratul Kahf 

Vers : 26

قُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثُواْۖ لَهُۥ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَبۡصِرۡ بِهِۦ وَأَسۡمِعۡۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا يُشۡرِكُ فِي حُكۡمِهِۦٓ أَحَدٗا

Ka ce: “Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.” Gaibun da yake sammai da qasa nasa ne. Wa ya yi gani irin nasa, wa kuma ya yi ji irin nasa (watau Allah). Ba su da wani majivinci in ban da Shi; ba Ya kuma tarayya da wani a cikin hukuncinsa



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 27

وَٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَۖ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدٗا

Kuma ka karanta abin da aka yiwo maka wahayi da shi daga littafin Ubangijinka: Ba mai canja kalmominsa; ba kuma za ka sami wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 28

وَٱصۡبِرۡ نَفۡسَكَ مَعَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ وَلَا تَعۡدُ عَيۡنَاكَ عَنۡهُمۡ تُرِيدُ زِينَةَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَا تُطِعۡ مَنۡ أَغۡفَلۡنَا قَلۡبَهُۥ عَن ذِكۡرِنَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ وَكَانَ أَمۡرُهُۥ فُرُطٗا

Ka kuma haqurqurtar da kanka (da zama) tare da waxanda suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma suna neman yardarsa; kar kuma ka kawar da idanuwanka daga gare su kana neman adon rayuwar duniya; kada kuma ka bi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu ya kuma bi son ransa, wanda kuma al’amarinsa ya zama a sukurkuce



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 29

وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّـٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَاۚ وَإِن يَسۡتَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَآءٖ كَٱلۡمُهۡلِ يَشۡوِي ٱلۡوُجُوهَۚ بِئۡسَ ٱلشَّرَابُ وَسَآءَتۡ مُرۡتَفَقًا

Kuma ka ce: “Gaskiya daga Ubangijinku take;” to wanda ya ga dama ya yi imani, wanda kuma ya ga dama sai ya kafirta. Lalle kam Mun tanadar wa azzalumai wata wuta wadda katangarta ta kewaye su. Idan kuma suka nemi taimako to za a taimake su ne da ruwa kamar tafasasshen mai da zai riqa toye fuskoki. Tir da wannan abin shan, makoma kuma ta munana



Sure: Suratul Kahf 

Vers : 30

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ مَنۡ أَحۡسَنَ عَمَلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari tabbas Mu ba ma tozarta ladan wanda ya kyautata aiki