تَبَّتۡ يَدَآ أَبِي لَهَبٖ وَتَبَّ
Hannayen Abu Lahabi[1] sun halaka, shi ma kuma ya halaka
1- Abu Lahab, xaya ne daga baffannin Manzon Allah wanda ya nuna wa Annabi () qiyayya ya mutu yana kafiri.
Compartilhar :
مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُ مَالُهُۥ وَمَا كَسَبَ
Dukiyarsa da abin da ya tsuwurwurta ba su amfana masa komai ba
سَيَصۡلَىٰ نَارٗا ذَاتَ لَهَبٖ
Ba da daxewa ba zai shiga wuta mai balbali
وَٱمۡرَأَتُهُۥ حَمَّالَةَ ٱلۡحَطَبِ
Da kuma matarsa mai yawan xaukar kayan qaya[1]
1- Watau Ummu Jamil, ta kasance tana zuba wa Annabi () qaya a kan hanyarsa domin ya taka.
فِي جِيدِهَا حَبۡلٞ مِّن مَّسَدِۭ
A wuyanta akwai igiyar kaba mai ingantacciyar tukka. (a ranar alqiyama)