Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 31

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَفَلَمۡ تَكُنۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡ وَكُنتُمۡ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Amma kuma waxanda suka kafirce (za a ce da su): “Yanzu ashe ayoyina ba su kasance ana karanta muku su ba, sai kuka yi girman kai, kuka kasance mutane masu manyan laifuka?”



Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 32

وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞ وَٱلسَّاعَةُ لَا رَيۡبَ فِيهَا قُلۡتُم مَّا نَدۡرِي مَا ٱلسَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنّٗا وَمَا نَحۡنُ بِمُسۡتَيۡقِنِينَ

Idan kuma aka ce, lalle alqawarin Allah gaskiya ne, alqiyama kuma babu kokwanto a game da ita kukan ce: “Mu ba mu da sanin mece ce ma alqiyama, mu ba abin da muke tsammani (game da ita) sai zato, mu kuma ba mu da tabbas.”



Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 33

وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma irin munanan ayyukan da suka aikata suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu



Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 34

وَقِيلَ ٱلۡيَوۡمَ نَنسَىٰكُمۡ كَمَا نَسِيتُمۡ لِقَآءَ يَوۡمِكُمۡ هَٰذَا وَمَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Aka kuma ce: “A yau za Mu manta da ku[1] kamar yadda kuka manta haxuwarku da wannan rana taku, makomarku kuma wuta ce, kuma ba ku da wasu mataimaka


1- Watau zai bar su a cikin wuta ya yi watsi da su, sakamakon mantawa da suka yi da wannan ranar.


Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 35

ذَٰلِكُم بِأَنَّكُمُ ٱتَّخَذۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ هُزُوٗا وَغَرَّتۡكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ فَٱلۡيَوۡمَ لَا يُخۡرَجُونَ مِنۡهَا وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ

“Wannan kuwa saboda lalle kun xauki ayoyin Allah abin yi wa izgili, rayuwar duniya kuma ta ruxe ku.” To a yau ba za a fitar da su daga cikinta ba, kuma su ba za a nemi su kawo hanzarinsu ba



Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 36

فَلِلَّهِ ٱلۡحَمۡدُ رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَرَبِّ ٱلۡأَرۡضِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

To yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin qasa, Ubangijin talikai



Surata: Suratul Jasiya

O versículo : 37

وَلَهُ ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Girma nasa ne a cikin sammai da qasa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima