Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 31

قُلۡ إِن كُنتُمۡ تُحِبُّونَ ٱللَّهَ فَٱتَّبِعُونِي يُحۡبِبۡكُمُ ٱللَّهُ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Ka ce: “In kun kasance kuna son Allah, to ku yi mini biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin qai.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 32

قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ka ce: “Ku yi xa’a ga Allah da Manzo; to in kuwa kuka juya baya, to lalle Allah ba Ya son kafirai.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 33

۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰٓ ءَادَمَ وَنُوحٗا وَءَالَ إِبۡرَٰهِيمَ وَءَالَ عِمۡرَٰنَ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Lalle Allah Ya zavi Adamu, da Nuhu da iyalan gidan Ibrahimu da iyalan gidan Imrana Ya fifita su a kan sauran talikai



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 34

ذُرِّيَّةَۢ بَعۡضُهَا مِنۢ بَعۡضٖۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Wata zurriya ce, sashinsu ‘ya’ya ne ga sashi. Kuma Allah Mai ji ne, Mai yawan sani



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 35

إِذۡ قَالَتِ ٱمۡرَأَتُ عِمۡرَٰنَ رَبِّ إِنِّي نَذَرۡتُ لَكَ مَا فِي بَطۡنِي مُحَرَّرٗا فَتَقَبَّلۡ مِنِّيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Tuna lokacin da matar Imrana ta ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na yi maka bakancen abin da yake cikina ya zamanto ‘yantacce, don haka Ka karva daga gare ni, lalle Kai ne Mai ji, Mai yawan sani.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 36

فَلَمَّا وَضَعَتۡهَا قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي وَضَعۡتُهَآ أُنثَىٰ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا وَضَعَتۡ وَلَيۡسَ ٱلذَّكَرُ كَٱلۡأُنثَىٰۖ وَإِنِّي سَمَّيۡتُهَا مَرۡيَمَ وَإِنِّيٓ أُعِيذُهَا بِكَ وَذُرِّيَّتَهَا مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

To yayin da ta haife ta sai ta ce: “Ya Ubangijina, lalle ni na haife ta ‘ya mace,” kuma Allah ne Ya fi sanin abin da ta haifa “Kuma xa namiji ba daidai yake da ‘ya mace ba; kuma lalle ni na raxa mata suna Maryamu, kuma lalle ni ina nema mata tsarinka da zurriyarta daga Shaixan korarre.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 37

فَتَقَبَّلَهَا رَبُّهَا بِقَبُولٍ حَسَنٖ وَأَنۢبَتَهَا نَبَاتًا حَسَنٗا وَكَفَّلَهَا زَكَرِيَّاۖ كُلَّمَا دَخَلَ عَلَيۡهَا زَكَرِيَّا ٱلۡمِحۡرَابَ وَجَدَ عِندَهَا رِزۡقٗاۖ قَالَ يَٰمَرۡيَمُ أَنَّىٰ لَكِ هَٰذَاۖ قَالَتۡ هُوَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٍ

Sai Ubangijinta Ya karve ta da kyakkyawar karva, kuma Ya yi mata kyakkyawar tarbiyya, kuma Ya danqa renonta a hannun Zakariyya; duk lokacin da Zakariyya ya shiga wurinta a xakin ibada, sai ya sami abinci a wurinta, sai ya ce: “Ya ke Maryamu, wannan daga ina kika samu?” Sai ta ce: “Wannan daga Allah ne; lalle Allah Yana arzurta wanda Ya ga dama ba tare da lissafi ba.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 38

هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُۥۖ قَالَ رَبِّ هَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ ذُرِّيَّةٗ طَيِّبَةًۖ إِنَّكَ سَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

A wannan lokacin sai Zakariyya ya roqi Ubangijinsa, ya ce: “Ya Ubangijina, Ka ba ni zurriyya ta gari daga gare Ka, lalle Kai Mai amsa roqo ne.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 39

فَنَادَتۡهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُوَ قَآئِمٞ يُصَلِّي فِي ٱلۡمِحۡرَابِ أَنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحۡيَىٰ مُصَدِّقَۢا بِكَلِمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَسَيِّدٗا وَحَصُورٗا وَنَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Sai mala’iku suka kira shi, lokacin yana tsaye yana salla a cikin xakin ibada, (suka ce): “Lalle Allah Yana yi maka albishir da Yahya, wanda yake mai gaskatawa da wata kalma daga Allah, kuma zai zama shugaba, kuma mai tsare kansa daga mata, kuma Annabi daga cikin salihan bayi.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 40

قَالَ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَقَدۡ بَلَغَنِيَ ٱلۡكِبَرُ وَٱمۡرَأَتِي عَاقِرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكَ ٱللَّهُ يَفۡعَلُ مَا يَشَآءُ

Ya ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami xa, ga shi tsufa ya riga ya cim mini, kuma ga shi matata juya ce?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake aikata abin da Ya ga dama.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 41

قَالَ رَبِّ ٱجۡعَل لِّيٓ ءَايَةٗۖ قَالَ ءَايَتُكَ أَلَّا تُكَلِّمَ ٱلنَّاسَ ثَلَٰثَةَ أَيَّامٍ إِلَّا رَمۡزٗاۗ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ كَثِيرٗا وَسَبِّحۡ بِٱلۡعَشِيِّ وَٱلۡإِبۡكَٰرِ

Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya mini wata alama.” Ya ce: “Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana yini uku sai dai da nuni. Kuma ka ambaci Ubangijinka ambato mai yawa, kuma ka yi tasbihi yammaci da safiya.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 42

وَإِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰكِ وَطَهَّرَكِ وَٱصۡطَفَىٰكِ عَلَىٰ نِسَآءِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma ka tuna lokacin da mala’iku suka ce: “Ya ke Maryamu, lalle Allah Ya zave ki, Ya kuma tsarkake ki, kuma Ya zave ki a kan sauran mata na talikai



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 43

يَٰمَرۡيَمُ ٱقۡنُتِي لِرَبِّكِ وَٱسۡجُدِي وَٱرۡكَعِي مَعَ ٱلرَّـٰكِعِينَ

“Ya ke Maryamu, ki yi xa’a ga Ubangijinki, kuma ki riqa yin sujada, kuma ki riqa yin ruku’u tare da masu ruku’u



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 44

ذَٰلِكَ مِنۡ أَنۢبَآءِ ٱلۡغَيۡبِ نُوحِيهِ إِلَيۡكَۚ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ يُلۡقُونَ أَقۡلَٰمَهُمۡ أَيُّهُمۡ يَكۡفُلُ مَرۡيَمَ وَمَا كُنتَ لَدَيۡهِمۡ إِذۡ يَخۡتَصِمُونَ

Wancan (abin da ya gabata a baya) yana cikin labaru na gaibi da Muke yi maka wahayinsa, kuma kai ba ka wurinsu lokacin da suka jefa alqalumansu don tantance wane ne cikinsu zai karvi renon Maryamu, kuma kai ba ka nan tare da su yayin da suke jayayya da juna



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 45

إِذۡ قَالَتِ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَٰمَرۡيَمُ إِنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٖ مِّنۡهُ ٱسۡمُهُ ٱلۡمَسِيحُ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ وَجِيهٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

Ka tuna lokacin da mala’iku suka ce: “Ya ke Maryamu, lalle Allah Yana yi miki albishir da wata kalma daga gare shi, sunansa Almasihu Isa xan Maryamu, mai daraja a duniya da lahira, kuma yana cikin bayi makusanta



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 46

وَيُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗا وَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

“Kuma zai riqa yi wa mutane magana tun yana cikin shimfixar jego da kuma lokacin da ya zama dattijo, kuma yana cikin salihan bayi.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 47

قَالَتۡ رَبِّ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي وَلَدٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞۖ قَالَ كَذَٰلِكِ ٱللَّهُ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Sai ta ce: “Ya Ubangijina, ta yaya zan sami xa alhalin wani namiji bai kusance ni ba?” Sai ya ce: “Kamar haka ne Allah Yake halittar abin da Ya ga dama. Idan Ya yi zartar da wani al’amari, sai Ya ce da shi: “Kasance” Nan take sai ya kasance



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 48

وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

“Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 49

وَرَسُولًا إِلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَنِّي قَدۡ جِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ أَنِّيٓ أَخۡلُقُ لَكُم مِّنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ فَأَنفُخُ فِيهِ فَيَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ وَأُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِ ٱللَّهِۖ وَأُنَبِّئُكُم بِمَا تَأۡكُلُونَ وَمَا تَدَّخِرُونَ فِي بُيُوتِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

“Kuma zai aiko shi a matsayin Manzo ga Banu Isra’ila (yana mai cewa): “Lalle ni na zo muku da wata aya daga Ubangijinku; lalle ni zan riqa mulmula muku tavo a siffar tsuntsu, sai in yi busa a cikinsa sai ya zama tsuntsu da izinin Allah; kuma zan warkar da wanda aka haifa makaho da mai cutar albaras, kuma in rayar da matattu da izinin Allah; kuma zan riqa ba ku labarin abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a gidajenku. Lalle a cikin hakan akwai aya a gare ku in har kun kasance muminai



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 50

وَمُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَلِأُحِلَّ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي حُرِّمَ عَلَيۡكُمۡۚ وَجِئۡتُكُم بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

“Kuma zan zama mai gaskata abin da ya gabace ni na Attaura, kuma don in halatta muku sashin abubuwan da aka haramta muku. Kuma na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, don haka ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku yi mini biyayya



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 51

إِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle Allah Shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, don haka ku bautata masa Shi kaxai. Wannan shi ne tafarki madaidaici.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 52

۞فَلَمَّآ أَحَسَّ عِيسَىٰ مِنۡهُمُ ٱلۡكُفۡرَ قَالَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَٱشۡهَدۡ بِأَنَّا مُسۡلِمُونَ

To yayin da Isa ya ga alamun kafirci a tare da su sai ya ce: “Su wane ne za su taimake ni wajen kira zuwa ga Allah?” Sai Hawariyawa suka ce: “Mu ne mataimaka addinin Allah, mun yi imani da Allah, kuma ka ba da shaida cewa, mu Musulmai ne



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 53

رَبَّنَآ ءَامَنَّا بِمَآ أَنزَلۡتَ وَٱتَّبَعۡنَا ٱلرَّسُولَ فَٱكۡتُبۡنَا مَعَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

“Ya Ubangijinmu, mun yi imani da abin da Ka saukar, kuma mun yi xa’a ga Manzo, don haka Ka rubuta mu tare da masu shaida.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 54

وَمَكَرُواْ وَمَكَرَ ٱللَّهُۖ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلۡمَٰكِرِينَ

Sai suka shirya makirci, sai Allah Ya mayar musu da martani game da makircinsu; kuma Allah Shi ne Fiyayyen masu mayar da martanin makirci



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 55

إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَىٰٓ إِنِّي مُتَوَفِّيكَ وَرَافِعُكَ إِلَيَّ وَمُطَهِّرُكَ مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَجَاعِلُ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوكَ فَوۡقَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۖ ثُمَّ إِلَيَّ مَرۡجِعُكُمۡ فَأَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡ فِيمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kuma ka tuna lokacin da Allah Ya ce: “Ya kai Isa, lalle Ni Mai karvar ranka ne, kuma Ni Mai xaukaka ka ne zuwa gare Ni, kuma zan tsarkake ka daga (cutarwar) waxanda suka kafirta, kuma zan xora waxanda suka bi ka a kan waxanda suka kafirta har zuwa ranar tashin alqiyama; sannan zuwa gare Ni ne makomarku take, sai In yi hukunci a tsakaninku game da abin da kuke savani a kansa



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 56

فَأَمَّا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَأُعَذِّبُهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗا فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Amma waxanda suka kafirce, zan yi musu azaba mai tsanani a duniya da lahira, kuma ba su da wasu mataimaka.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 57

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Amma kuma waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka nagari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 58

ذَٰلِكَ نَتۡلُوهُ عَلَيۡكَ مِنَ ٱلۡأٓيَٰتِ وَٱلذِّكۡرِ ٱلۡحَكِيمِ

“Wannan (labarin) Muna karanta maka shi ne daga ayoyi da kuma Alkur’ani mai hikima.”



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 59

إِنَّ مَثَلَ عِيسَىٰ عِندَ ٱللَّهِ كَمَثَلِ ءَادَمَۖ خَلَقَهُۥ مِن تُرَابٖ ثُمَّ قَالَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Lalle misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne; Ya halicce shi daga turvaya, sannan Ya ce da shi: “Kasance.” nan take sai ya kasance



Surata: Suratu Ali-Imran

O versículo : 60

ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ

Gaskiya ce daga wajen Ubangijinka, don haka kar ka kasance cikin masu yin kokwanto