Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 31

وَجَعَلۡنَا فِي ٱلۡأَرۡضِ رَوَٰسِيَ أَن تَمِيدَ بِهِمۡ وَجَعَلۡنَا فِيهَا فِجَاجٗا سُبُلٗا لَّعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ

Muka kuma sanya kafaffun duwatsu a qasa don kar ta yi tangal-tangal da su, Muka kuma sanya wuraren tafiya a cikinta (su zama) hanyoyi don su gane (inda za su)



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 32

وَجَعَلۡنَا ٱلسَّمَآءَ سَقۡفٗا مَّحۡفُوظٗاۖ وَهُمۡ عَنۡ ءَايَٰتِهَا مُعۡرِضُونَ

Muka kuma sanya sama (ta zama) rufi tsararre; su kuwa (duk da haka) masu bijire wa ayoyinta (watau sama) ne



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 33

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ

Shi ne kuma Wanda Ya halicci dare da rana, da kuma rana da wata; kowannensu yana ninqaya cikin falakinsa



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 34

وَمَا جَعَلۡنَا لِبَشَرٖ مِّن قَبۡلِكَ ٱلۡخُلۡدَۖ أَفَإِيْن مِّتَّ فَهُمُ ٱلۡخَٰلِدُونَ

Ba Mu kuma sanya wa wani mutum dawwama ba a gabaninka; to yanzu idan ka mutu su xin masu dawwama ne?



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 35

كُلُّ نَفۡسٖ ذَآئِقَةُ ٱلۡمَوۡتِۗ وَنَبۡلُوكُم بِٱلشَّرِّ وَٱلۡخَيۡرِ فِتۡنَةٗۖ وَإِلَيۡنَا تُرۡجَعُونَ

Kowanne rai zai xanxani mutuwa. Muna kuwa jarrabar ku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gare Mu ne za a dawo da ku



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 36

وَإِذَا رَءَاكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِن يَتَّخِذُونَكَ إِلَّا هُزُوًا أَهَٰذَا ٱلَّذِي يَذۡكُرُ ءَالِهَتَكُمۡ وَهُم بِذِكۡرِ ٱلرَّحۡمَٰنِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

Idan kuma waxanda suka kafirta su ka gan ka, ba abin da suke yi maka sai izgili (suna cewa): “Yanzu wannan shi ne wanda yake aibata allolinku?” Alhali kuwa su suna kafirce wa ambaton (Allah) Mai rahama



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 37

خُلِقَ ٱلۡإِنسَٰنُ مِنۡ عَجَلٖۚ سَأُوْرِيكُمۡ ءَايَٰتِي فَلَا تَسۡتَعۡجِلُونِ

An halicci mutum da son gaggawa. Ba da daxewa ba zan nuna muku ayoyina, to don haka kada ku nemi gaggauto da (zuwansu)



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 38

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Suna kuma cewa: “Wai yaushe ne wannan alqawarin (na alqiyama zai zo) idan kun kasance masu gaskiya?”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 39

لَوۡ يَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ حِينَ لَا يَكُفُّونَ عَن وُجُوهِهِمُ ٱلنَّارَ وَلَا عَن ظُهُورِهِمۡ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Da waxanda suka kafirta za su san lokacin da za su kasa kare fuskokinsu daga wuta, da kuma bayansu, ba kuma za a taimake su ba (to da ba su faxi haka ba)



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 40

بَلۡ تَأۡتِيهِم بَغۡتَةٗ فَتَبۡهَتُهُمۡ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ رَدَّهَا وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

A’a, za ta zo musu ne ta farat- xaya sai ta rikirkita su, ba kuwa za su iya kawar da ita ba, kuma su ba za a saurara musu ba



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 41

وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَحَاقَ بِٱلَّذِينَ سَخِرُواْ مِنۡهُم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Haqiqa kuma an yi izgili ga manzannin da suka gabace ka, sai sakamakon abin da suke yin izgili da shi ya aukar wa masu yin izgilin



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 42

قُلۡ مَن يَكۡلَؤُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ مِنَ ٱلرَّحۡمَٰنِۚ بَلۡ هُمۡ عَن ذِكۡرِ رَبِّهِم مُّعۡرِضُونَ

Ka ce (da su): “Wane ne yake kare ku dare da rana daga (azabar Allah) Mai rahama?” A’a su dai masu bijire wa ambaton Ubangijinsu ne



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 43

أَمۡ لَهُمۡ ءَالِهَةٞ تَمۡنَعُهُم مِّن دُونِنَاۚ لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَ أَنفُسِهِمۡ وَلَا هُم مِّنَّا يُصۡحَبُونَ

Ko kuwa suna da ababen bauta ne da za su kare su (daga azaba) ba Mu ba? Ba za su iya taimakon kansu ba, kuma ba za a kiyaye su (daga azabarmu) ba



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 44

بَلۡ مَتَّعۡنَا هَـٰٓؤُلَآءِ وَءَابَآءَهُمۡ حَتَّىٰ طَالَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡعُمُرُۗ أَفَلَا يَرَوۡنَ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَآۚ أَفَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ

A’a, Mun dai jiyar da waxannan daxi ne su da iyayensu, har dai rayuwa ta tsawaita a gare su. Yanzu ba sa ganin cewa Mu Muna zo wa qasa Muna cinye iyakokinta da kaxan-kaxan[1]? Yanzu su ne masu yin rinjaye?


1- Watau mutanen cikinta suna ta raguwa saboda mutuwa. Ko kuma Musulmi suna qara cinye su da yaqi.


Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 45

قُلۡ إِنَّمَآ أُنذِرُكُم بِٱلۡوَحۡيِۚ وَلَا يَسۡمَعُ ٱلصُّمُّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا مَا يُنذَرُونَ

Ka ce (da su): “Ni kawai ina yi muku gargaxi ne da wahayi.” Kurame kuwa ba za su ji kira ba idan ma ana gargaxin su



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 46

وَلَئِن مَّسَّتۡهُمۡ نَفۡحَةٞ مِّنۡ عَذَابِ رَبِّكَ لَيَقُولُنَّ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ

Wallahi da wani xan furji na azabar Ubangijinka ya shafe su da tabbas za su ce: “Kaiconmu, lalle mu mun tabbata azzalumai.”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 47

وَنَضَعُ ٱلۡمَوَٰزِينَ ٱلۡقِسۡطَ لِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَلَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗاۖ وَإِن كَانَ مِثۡقَالَ حَبَّةٖ مِّنۡ خَرۡدَلٍ أَتَيۡنَا بِهَاۗ وَكَفَىٰ بِنَا حَٰسِبِينَ

Za Mu kuma sanya ma’aunai na adalci a ranar alqiyama, sannan ba za a zalunci kowanne rai da komai ba, ko da ya zama gwargwadon qwayar komayya ne, za Mu zo da shi. Kuma Mun isa Masu hisabi!



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 48

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ٱلۡفُرۡقَانَ وَضِيَآءٗ وَذِكۡرٗا لِّلۡمُتَّقِينَ

Haqiqa Mun ba wa Musa da Haruna (Attaura) mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya) da kuma haske da shiriya ga masu taqawa



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 49

ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ وَهُم مِّنَ ٱلسَّاعَةِ مُشۡفِقُونَ

(Su ne) waxanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da sun gan Shi ba, kuma su suna masu fargaba game da tashin alqiyama



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 50

وَهَٰذَا ذِكۡرٞ مُّبَارَكٌ أَنزَلۡنَٰهُۚ أَفَأَنتُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ

Wannan (Alqur’ani) kuwa tunatarwa ne mai albarka da Muka saukar da shi. Shin ku yanzu kwa riqa musun sa?



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 51

۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ إِبۡرَٰهِيمَ رُشۡدَهُۥ مِن قَبۡلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَٰلِمِينَ

Haqiqa kuma Mun bai wa Ibrahimu shiriyarsa tun da farko, Mun kuma zamanto Muna sane da shi



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 52

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا هَٰذِهِ ٱلتَّمَاثِيلُ ٱلَّتِيٓ أَنتُمۡ لَهَا عَٰكِفُونَ

(Ka tuna) lokacin da ya ce da babansa da kuma jama’arsa: “Mene ne (amfanin) waxannan gumakan da kuka duqufa a bautar su?”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 53

قَالُواْ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا لَهَا عَٰبِدِينَ

Suka ce: “Mun sami iyayenmu suna bauta musu ne.”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 54

قَالَ لَقَدۡ كُنتُمۡ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمۡ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

(Ibrahimu) ya ce: “Haqiqa ku da iyayen naku kun tabbata a kan vata bayyananne.”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 55

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا بِٱلۡحَقِّ أَمۡ أَنتَ مِنَ ٱللَّـٰعِبِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana da gaskiya ne ko kuwa kai ma kana cikin masu wasa (da mu) ne?”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 56

قَالَ بَل رَّبُّكُمۡ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ ٱلَّذِي فَطَرَهُنَّ وَأَنَا۠ عَلَىٰ ذَٰلِكُم مِّنَ ٱلشَّـٰهِدِينَ

(Ibrahimu) ya ce: “A’a, Ubangijinku dai (Shi ne) Ubangijin sammai da qasa, Wanda Ya halicce su, kuma ni ina daga masu shaida a kan wannan



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 57

وَتَٱللَّهِ لَأَكِيدَنَّ أَصۡنَٰمَكُم بَعۡدَ أَن تُوَلُّواْ مُدۡبِرِينَ

“Na rantse da Allah tabbas zan shirya wa gumakanku kaidi bayan kun tafi kun ba da baya!



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 58

فَجَعَلَهُمۡ جُذَٰذًا إِلَّا كَبِيرٗا لَّهُمۡ لَعَلَّهُمۡ إِلَيۡهِ يَرۡجِعُونَ

Sai ya mayar da su guntu-guntu in ban da babbansu (da ya bari) don ko sa dawo masa (su tambaye shi)



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 59

قَالُواْ مَن فَعَلَ هَٰذَا بِـَٔالِهَتِنَآ إِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Suke ce: “Wane ne ya yi wa ababen bautarmu wannan (aika-aika)? Lallai shi yana daga azzalumai!”



Surata: Suratul Anbiya

O versículo : 60

قَالُواْ سَمِعۡنَا فَتٗى يَذۡكُرُهُمۡ يُقَالُ لَهُۥٓ إِبۡرَٰهِيمُ

(Wasu daga cikinsu) suka ce: “Mun ji wani saurayi yana ambaton su, ana ce da shi Ibrahimu.”