Surata: Suratun Nahl

O versículo : 31

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ لَهُمۡ فِيهَا مَا يَشَآءُونَۚ كَذَٰلِكَ يَجۡزِي ٱللَّهُ ٱلۡمُتَّقِينَ

Aljannatai ne na jin daxi za su shige su, qoramu suna gudana ta qarqashinsu; suna da duk abin da suka ga dama cikinsu. Kamar haka Allah Yake saka wa masu taqawa



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 32

ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ يَقُولُونَ سَلَٰمٌ عَلَيۡكُمُ ٱدۡخُلُواْ ٱلۡجَنَّةَ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Waxanda mala’iku suke xaukar ransu suna tsarkaka, suna cewa: “Aminci ya tabbata a gare ku, ku shiga Aljanna saboda abin da kuka zamanto kuna aikatawa (a duniya)



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 33

هَلۡ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأۡتِيَهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ أَوۡ يَأۡتِيَ أَمۡرُ رَبِّكَۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ ٱللَّهُ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Shin akwai abin da (mushrikai) suke sauraro in ban da mala’iku su zo musu, ko kuma umarnin Ubangijinka ya zo? Kamar haka waxanda ke gabaninsu suka aikata. Allah bai zalunce su ba, sai dai kuma kawunansu suka kasance suna zalunta



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 34

فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Sai (sakamakon) mummunan abin da suka aikata ya same su, kuma abin da suke yi wa izgili ya rutsa da su



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 35

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ لَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا عَبَدۡنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖ نَّحۡنُ وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمۡنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَيۡءٖۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ فَهَلۡ عَلَى ٱلرُّسُلِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Waxanda kuma suka yi shirka suka ce: “Da Allah Ya ga dama da ba mu bauta wa komai ba sai Shi, daga mu har iyayenmu, da kuma ba mu haramta komai ba wanda bai haramta ba.” Kamar haka waxanda suka gabace su suka aikata. Shin akwai abin da yake a kan manzanni in ban da isar da aike a fili?



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 36

وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِي كُلِّ أُمَّةٖ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُواْ ٱلطَّـٰغُوتَۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنۡهُم مَّنۡ حَقَّتۡ عَلَيۡهِ ٱلضَّلَٰلَةُۚ فَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِينَ

Haqiqa kuma Mun aiko manzo a kowacce al’umma cewa,: “Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci Xagutu[1].” To akwai daga cikinsu waxanda Allah Ya shiryar, akwai kuma daga cikinsu wanda vata ya tabbata a kansa. To ku yi tafiya a bayan qasa ku ga yadda qarshen masu qaryatawa ya kasance


1- Xagutu ana nufin duk wani abu da aka qetare iyakokin Allah saboda shi, ta hanyar bautar sa, mutum ne ko aljani ko dutse ko itace.


Surata: Suratun Nahl

O versículo : 37

إِن تَحۡرِصۡ عَلَىٰ هُدَىٰهُمۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي مَن يُضِلُّۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Idan ma kana kwaxayin shiriyarsu ne, to lalle Allah fa ba Ya shiryar da wanda Ya vatar; ba su da kuma wasu mataimaka



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 38

وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَا يَبۡعَثُ ٱللَّهُ مَن يَمُوتُۚ بَلَىٰ وَعۡدًا عَلَيۡهِ حَقّٗا وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

Suka kuma rantse da Allah iya rantsuwarsu, (cewa) Allah ba zai tashi wanda ya mutu ba. A’a, ba haka ba ne, alqawari ne a kansa na gaskiya, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka)



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 39

لِيُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِي يَخۡتَلِفُونَ فِيهِ وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ كَانُواْ كَٰذِبِينَ

(Zai tashe su) don Ya bayyana musu abin da suke savani game da shi, don kuma kafirai su san cewa, su sun tabbata maqaryata



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 40

إِنَّمَا قَوۡلُنَا لِشَيۡءٍ إِذَآ أَرَدۡنَٰهُ أَن نَّقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Abin da kawai Muke cewa da abu idan Mun nufe shi, sai Mu ce da shi: “Kasance”, sai kawai ya kasance



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 41

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْ لَنُبَوِّئَنَّهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Waxanda kuma suka yi hijira saboda Allah bayan an zalunce su lalle za Mu shirya musu kyakkyawar (rayuwa) a duniya; ladan lahira kuma ya fi girma da a ce sun kasance suna sane da (haka)



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 42

ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Waxanda suka yi haquri kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogaro



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 43

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ إِلَّا رِجَالٗا نُّوحِيٓ إِلَيۡهِمۡۖ فَسۡـَٔلُوٓاْ أَهۡلَ ٱلذِّكۡرِ إِن كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Ba Mu tava aiko (wasu manzanni) ba a gabaninka sai mazaje waxanda Muke yi wa wahayi. Don haka ku tambayi ma’abota ilimi idan kun kasance ba ku sani ba



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 44

بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

(Mun aiko su) da hujjoji bayyanannu da littattafai. Mun kuma saukar maka da Alqur’ani don ka yi wa mutane bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 45

أَفَأَمِنَ ٱلَّذِينَ مَكَرُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَخۡسِفَ ٱللَّهُ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضَ أَوۡ يَأۡتِيَهُمُ ٱلۡعَذَابُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَشۡعُرُونَ

Yanzu waxanda suka shirya mummunan makirci ba sa gudun Allah Ya kife qasa da su, ko kuma azaba ta zo musu ta inda ba sa zato?



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 46

أَوۡ يَأۡخُذَهُمۡ فِي تَقَلُّبِهِمۡ فَمَا هُم بِمُعۡجِزِينَ

Ko kuwa Ya kama su a cikin kai-kawonsu, ba kuwa za su gagara ba?



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 47

أَوۡ يَأۡخُذَهُمۡ عَلَىٰ تَخَوُّفٖ فَإِنَّ رَبَّكُمۡ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٌ

Ko kuma Ya kama su a lokacin da suke cike da tsoron (Sa)? To lalle Ubangijinka Mai tausayi ne, Mai jin qai



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 48

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَىٰ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٖ يَتَفَيَّؤُاْ ظِلَٰلُهُۥ عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَٱلشَّمَآئِلِ سُجَّدٗا لِّلَّهِ وَهُمۡ دَٰخِرُونَ

Shin yanzu ba sa ganin abubuwan da Allah Ya halitta kowane iri ne, inuwowinsa suna bazuwa dama da hagu, suna masu sujjada ga Allah suna kuma masu qasqantar da kai[1]?


1- Malamai sun ce, idan rana ta gushe daga tsakiyar sama, to komai yana faxuwa ya yi sujjada ga Allah.


Surata: Suratun Nahl

O versículo : 49

وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ مِن دَآبَّةٖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُمۡ لَا يَسۡتَكۡبِرُونَ

Abin da yake cikin sammai da abin da yake bayan qasa na kowace dabba da mala’iku suna yin sujjada ne ga Allah, su kuma ba sa girman kai



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 50

يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوۡقِهِمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ۩

Suna tsoron Ubangijnsu daga samansu kuma suna aikata abin da ake umartar su da shi



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 51

۞وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓاْ إِلَٰهَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَإِيَّـٰيَ فَٱرۡهَبُونِ

Allah kuma Ya ce: “Kada ku riqi abubuwan bauta guda biyu[1]. Abin bauta Xaya Yake Tilo; to sai ku ji tsoro na Ni kaxai.”


1- Watau kamar Majusawa masu cewa, wai akwai ubangijin alheri shi ne haske, akwai kuma na sharri shi ne duhu.


Surata: Suratun Nahl

O versículo : 52

وَلَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلدِّينُ وَاصِبًاۚ أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَتَّقُونَ

Kuma abin da ke sammai da qasa nasa ne, kuma gare Shi ake biyayya tutur. Shin yanzu wanin Allah ne kuke yi wa taqawa?



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 53

وَمَا بِكُم مِّن نِّعۡمَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيۡهِ تَجۡـَٔرُونَ

Kuma duk abin da kuke da shi na ni’ima to daga Allah ne; sannan kuma idan cuta ta same ku to wurinsa kuke kai kuka



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 54

ثُمَّ إِذَا كَشَفَ ٱلضُّرَّ عَنكُمۡ إِذَا فَرِيقٞ مِّنكُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ

Sannan kuma lokacin da Ya yaye muku cutar sai a samu wata qungiya daga cikinku suna yin shirka da Ubangijinsu



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 55

لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Don su butulce wa abin da Muka ba su. To ku xan ji daxi a (duniya), sai dai ba da daxewa ba za ku sani



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 56

وَيَجۡعَلُونَ لِمَا لَا يَعۡلَمُونَ نَصِيبٗا مِّمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡۗ تَٱللَّهِ لَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَفۡتَرُونَ

Suna kuma sanya wani kaso daga abin da Muka arzuta su da shi ga abubuwan da ba su san komai ba. Wallahi tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna qirqira



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 57

وَيَجۡعَلُونَ لِلَّهِ ٱلۡبَنَٰتِ سُبۡحَٰنَهُۥ وَلَهُم مَّا يَشۡتَهُونَ

Suna kuma jingina wa Allah ‘ya’ya mata[1], tsarki ya tabbata a gare Shi, su kuma suna da abin da suke sha’awa (na ‘ya’ya maza)


1- Suna cewa mala’iku mata ne kuma ‘ya’yan Allah ne.


Surata: Suratun Nahl

O versículo : 58

وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلۡأُنثَىٰ ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٞ

Kuma idan aka yi wa xayansu albishir da (‘ya) mace sai fuskarsa ta yi baqi qirin yana cike da tsananin baqin ciki



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 59

يَتَوَٰرَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ مِن سُوٓءِ مَا بُشِّرَ بِهِۦٓۚ أَيُمۡسِكُهُۥ عَلَىٰ هُونٍ أَمۡ يَدُسُّهُۥ فِي ٱلتُّرَابِۗ أَلَا سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Yana vuya daga (idon) mutane saboda munin abin da aka yi masa albishir da shi. Shin zai riqe shi ne a wulaqance ko kuwa zai binne shi ne a cikin qasa? Ku saurara, abin da suke hukuntawa kam ya munana



Surata: Suratun Nahl

O versículo : 60

لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ مَثَلُ ٱلسَّوۡءِۖ وَلِلَّهِ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Waxanda ba sa imani da ranar lahira suna da mummunar siffa. Allah kuwa Yana da maxaukakiyar siffa. Kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima