Idan aka zurfafa cikin littafin Allah, kowace aya da kowane misali, za su iya zana wa ruhin da yake neman shiriya hanyar shiriya.
HAKURI a Cikin Alkurani
A duniyar da take cike da sirrika da abubuwan daukar izina, Alqur’ani yana haskaka mana hanyar mu ta hanyar misalan da suka zo a cikinsa domin ya karantar da mu ya kuma shiryar da mu.
Hikimar Allah da rahamarsa suna bayyana game da wadannan misalan a cikin fadin Allah Ta’ala: Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komai qanqantarsa, sauro da abin ya fi shi. To amma waxanda suka yi imani suna sanin cewa, lalle shi (wannan misali) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Amma waxanda suka kafirta sai su riqa cewa: “Me Allah Yake nufi da wannan misalin?” Yana kuwa vatar da mutane da yawa da shi, kuma Ya shiryar da mutane da yawa da shi, kuma ba kowa Yake vatarwa da shi ba sai fasiqai”. Baqara: 26
Hikimar Allah Game Da Misalan Alqur’ani: Bayyanawa, Tuntuntuni, Ka shiriya
Ayar Alqur’ani: “Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komai qanqantarsa, sauro da abin ya fi shi...” [Baqara: 26] tana nuna zurfin hikimar Allah wurin yin amfani da misalai masu sauqi don a isar da wasu manya-manyan lamurra.
Wannan misalin da aka buga yana shiryar da mu zuwa ga cewa, Allah Ta’ala a littafinsa mai hikima yana amfani da bin abu daki-daki komai qanqantarsa tare da halittunsa don ya bayyana gaskiya. Da kuma sanar da mu cewa gaskiya ba ta taqaita a kan girman misali ko qanqantar sa ba. Wannan ayar tana karantar da mu muhimmancin duba zuwa ga halittar Allah da kallo na tuntuntuni da tadaburri, ta yadda hatta mafi qanqantar halittu suna dauke da abubuwan daukar izina da darussa ga masu tunani.
Misalan da Alqur’ani yake ba da wa don mu fahimci addini ta hanya mai zurfi mai dauke da tasiri, suna gabato mana da wata dama ce wadda ba za a iya qimanta ta da kudi ba. Ta hanyar yin tuntuntuni game da wadannan misalan ne muke koyon yadda za mu daukaka da imanin mu da qaruwar ilimin mu da taqawar zuciyoyin mu. Wannan misalin a karan-kansa yana kiran Muminai zuwa ga tabbatar da girman Allah a cikin dukkan komai, hatta sauro da muke ganinsa wani qarami ko marar amfani. Lalle imani da Allah yana nufin, yin imani hikimarsa da adalcinsa a cikin dukkan komai ba tare da duba zuwa ga girmansa ko launinsa ba.
Misalin yana nuna bambanci tsakanin Muminai masu ganin cewa, kowane misali gaskiya ne daga wurin Ubangijinsu da kuma kafirai masu tambaya game da dalilin buga irin wadannan misalan. Lalle wannan misalin yana bayyana yadda imani yake bude mana idanuwanmu game da hikima da abubuwa masu kyau game da dukkan abubuwan da suke kewaye da mu. A yayin da kafirci yake shamakance wannan hasken yake sanya zuciya ta zama a rufe game da fahimtar gaskiya.
Don haka mu sanya qasa mai taushi a zukatanmu ta yadda za su karbi misalan da Allah yake ba da wa bisa fahimta da tadabburi. Ba wai kawai mu yi qoqarin saninsu ba, a’a mu yi qoqarin yin aiki da abin da suke hukuntawa don mu yi tuntuntuni game da girman Allah da hikimarsa. Sannan a ko da yaushe mu riqa tunawa cewa, gaskiya ba ta taqaita a kan abin da ake ganin sa babba ne a idanu ba, a’a za ta iya zama a abin da yake qarami da kuma sassauqan abu. Duk wannan yana nuni zuwa ga rahamarsa da ikonsa mai isa matuqa.
A Alqur’ani Allah (SWT) yana amfani da ba da misalai a matsayin gadoji da za su hada tsakanin fahimtar dan’adam da wasu abubuwa da Allah yake so ya tabbatar. “Lalle Allah ba Ya jin kunyar buga kowanne irin misali komai qanqantarsa, sauro da abin ya fi shi....”
[Baqara: 26]. Wannan ayar tana tunatar da mu cewa babu wani abu a cikin halittun Allah da yake qarami ko wanda ba shi da muhimmanci da kuma nuna cewa, za a iya fitar da hikima hatta a cikin sassauqan halittun Allah. Misalan da Allah yake ba da wa a cikin Alqur’ani suna koyar da mu yin tuntuntuni game da halittun Allah don daukar izina da darussa wadanda za su karfafa mana imaninmu su kuma haska mana hanyar da za mu bi mu samu shiriya.
Misalan Alqur’ani suna nuna kyawu da girman Allah mahalicci, suna kuma bayyana yadda imani yake zurfafa fahimtarmu yake kuma yi mana jagora zuwa ga fahimtar gaskiya daga Ubangijinmu.
Wadannan misalan suna gabato wa da Muminai basira da haske. Yayin da a gefe guda suke bayyana wa kafirai rashin ikonsu a kan fahimtar wata haqiqa ta Ubangiji saboda nisan su da imani.
Wadannan misalan ba wai labarai ba ne kawai ko wasu abubuwa da za a hada a tsakanin wani da wani, a’a darussa ne na rayuwa da suke koyar da mu ya ya za mu rayu ta hanyar da za ta yardar da Allah ta kuma tabbatar mana da alheri garemu da wasunmu.
Allah (SWT) yana amfani da ba da misalai don ya gwada fahimtarmu da kuma imaninmu, don ya bayyana bambancin da ke tsakanin masu yin tuntuntuni game da ayoyinsa da koyonsu da kuma masu bijire musu. A kowane misali da aka ba da akwai kira zuwa ga yin tuntuntuni da lura, domin mu yi duba mu ga yadda Allah yake fuskantar da mu zuwa ga gaskiya da abin da yake daidai.
Misalan da Alqur’ani yake bugawa suna dauke da rahama da shiriya ga wanda ya yi tuntuntuni game da su ya kuma rayu bisa kan abin da suke hukuntawa.
Ku barmu mu sanya Alqur’ani da misalansa su zama masu shiryarwa a gare mu a cikin kowane taku daga cikin matakan rayuwar mu. Mu yi tuntuntuni game dasu da budaddun zuciyoyi da hankula masu kiyayewa, don mu yi rayuwa tare da hikima da imani.
Ko da yaushe mu riqa tunawa cewa, Allah ba ya jin kunyar bayyana gaskiya, da tuna cewa, a kowane misali daga cikin misalan da yake ba da wa akwai kira na gaskiya na yin tuntuntuni da yin tadabburi game da girman halittarsa da hikimarsa.
A cikin ayoyin Alqur’ani mai girma muna samun misalai da suka kai maqura wurin fito da abubuwa yadda suke da bayani, suna karantar da mu da shiryar damu zuwa ga wasu ma’aoni masu girma wadanda suka shafi aqidarmu da tauhidinmu ga Allah mai girma da daukaka. Daga cikin wadannan misalan, Allah Ta’ala yana gabatar da misali guda daya a cikin Suratun Nahli, watau fadinsa: “Allah kuma Ya ba da misali da bawan da aka mallaka, ba shi da iko a kan komai, da kuma wanda Muka bai wa arziki nagari daga gare Mu, to shi kuma yana ciyarwa daga shi (arzikin) a voye da kuma sarari; yanzu za su yi daidai? (Ai ba za su yi daidai ba). Yana mai bayyana bambanci babba dake tsakanin Allah mai halitta da abin halitta, tsakanin bawan da ake mallaka gajiyayye da mutum xa mai ‘yanci wanda yake mallakar arzuqi mai kyau yana kuma ciyar da shi a hanyar alheri.
A cikin Alqur’ani, Allah Ta’ala yana kawo misalan da suke bayyana girmansa da kadaitakar siffofinsa a yayin da yake nuna gajiyawa da tawaya ta wani wanda ba shi ba. Daga cikin wadannan misalan akwai fadin Allah Ta’ala: “Allah kuma Ya ba da wani misali da mutum biyu, xayansu bebe ne ba ya iya yin komai, kuma ya zama nauyi a kan mai gidansa, duk inda ya fuskantar da shi ba zai zo da wani alheri ba. Yanzu shi zai yi daidai da wanda yake umarni da adalci kuma yana bisa tafarki madaidaici? [Nahl: 76]
Allah ya ba da haske a kan bayyanan nan bambancin da ke tsakanin bawa bebe gajiyayye wanda ya iya amfana wa mai gidansa komai, ba ya iya zuwa da wani alheri, da bawan da yake yin umarni da adalci kuma yana kan tafarki madaidaici.
Wannan misalin yana nuna bambancin da ke tsakanin ababen bauta na qarya wadanda ba sa iya amfanarwa ko cutarwa ga kawunansu ko ga masu bauta musu, da kuma Allah mahalicci mai girma wanda yake kwadaitarwa a kan yin adalci yake kuma shiryar da bayinsa zuwa ga tafarki madaidaici.
Hakanan wannan misalin yana kiranmu da mu yi tuntuntuni da lura game da ma’anonin tauhidi da adalci a Musulunci, yana kuma qarfafa cewa, lalle ibada wajibi ne ta zama an fuskantar da ita ga Allah shi kadai tilo wanda yake mabuwayi mai iko a kan komai, mai adalci a lamarinsa. Don haka wanda yake bebe gajiyayye kamar gumaka da ababen da ake bautawa ba tare da haqqi ba, ba za su zama daidai da Allahn da a hannunsa makullan taskokin sammai da qassai suke ba, wanda yake umarni da yin alheri da adalci, yake kuma kiran bayinsa zuwa ga tafarkinsa madaidaici.
A ko da yaushe mu riqa tunawa cewa, Musulunci yana kiranmu zuwa ga yin tuntuntuni da tadabburin ayoyin Allah da misalan da yake bayarwa, wadanda suke koyar da mu hikima suke kuma haskaka mana hanya zuwa ga samun shiriya. Don haka mu dauki wannan misalin a matsayin ma’auni (kamfas) da zai fuskantar da mu zuwa ga inda za mu qarfafi imaninmu da Allah shi kadai, da yin aiki da abin da yake umarni da shi na yin adalci da nagarta, don mu kasance a kan tafarki madaidaici, watau hanyar da za ta sadar da mu zuwa ga yardar Allah da Aljannatunsa.
Qaqqarfan misali a cikin Suratul Baqara yana bayyana tare da siffanta halin wanda yake neman shiriya ba tare da gaskiya wurin neman ba ko riqo da ita (gaskiyar) ba. Allah Ta’ala yana cewa: “Misalinsu kamar misalin wanda ya wahala har ya kunna wuta ne, yayin da ta haskaka abin da yake daura da shi, sai Allah Ya tafiyar da haskensu Ya bar su cikin duffai ba sa gani.
Wannan misalin yana nuna halin wanda yake ganin gaskiya a bayyane a lokaci guda – kamar haske ne yake haskakawa a gefensa – amma nan da nan sai ya rasa wannan hasken saboda raunin imaninsa ko saboda juyawar zuciyarsa, don haka sai shiriya ta bar shi ya koma zuwa ga duffan jahilci da bata, ba tare da ya samu damar ganin ingantacciyar hanya ba.
Bari mu yi tuntuntuni game da wannan misalin mu dauki izina yayin da muke neman haske na haqiqa, watau hasken imani da yaqini da Allah. Mu sanya zukatanmu su yi riqo da shiriya, su zama cikin shiri na tafiya da tabbata a kan tafarki madaidaici. Hasken da Allah ya ke shiryar da wanda ya ga dama da shi daga cikin bayinsa, wajibi ne mu neme shi da gaske da kuma ikhlasi, kada mu bar shi ya kufce mana, a’a mu kiyaye shi ta hanyar yin ayyuka na na gari da kuma neman kusancin Allah.
Ku kasance masu neman haske yayin da ake cikin duffan rayuwa, shi ne hasken nan da ba ya bicewa, watau hasken shiriya da Alqur’ani da sunnah, don su haska mana hanya su kuma shiryar damu a kowane taku. Hasken da ke cikin zukatanmu shi ne basirar da muke ganin gaskiya da ita, muke kuma tafiya a kan ta bisa aminci da imani.