السورة: Suratul Kahf 

الآية : 70

قَالَ فَإِنِ ٱتَّبَعۡتَنِي فَلَا تَسۡـَٔلۡنِي عَن شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ أُحۡدِثَ لَكَ مِنۡهُ ذِكۡرٗا

Ya ce, “To idan ka bi ni kada ka tambaye ni game da kowane abu har sai na ba ka labari game da shi.”



السورة: Suratul Kahf 

الآية : 71

فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا رَكِبَا فِي ٱلسَّفِينَةِ خَرَقَهَاۖ قَالَ أَخَرَقۡتَهَا لِتُغۡرِقَ أَهۡلَهَا لَقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـًٔا إِمۡرٗا

Sai suka tafi, har lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, to sai ya huda shi; sai (Musa) ya ce: “Yanzu ka huda shi ne don ka nutsar da waxanda suke cikinsa? Haqiqa ka zo da babban abu.”



السورة: Suratul Kahf 

الآية : 72

قَالَ أَلَمۡ أَقُلۡ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا

Ya ce: “Ban faxa maka ba cewa kai ba za ka iya haquri da ni ba?”



السورة: Suratul Kahf 

الآية : 73

قَالَ لَا تُؤَاخِذۡنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرۡهِقۡنِي مِنۡ أَمۡرِي عُسۡرٗا

(Musa) ya ce: “Kada ka kama ni da abin da na manta, kada kuma ka xora mini abu mai wahala game da al’amarina.”



السورة: Suratul Kahf 

الآية : 74

فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا لَقِيَا غُلَٰمٗا فَقَتَلَهُۥ قَالَ أَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا زَكِيَّةَۢ بِغَيۡرِ نَفۡسٖ لَّقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـٔٗا نُّكۡرٗا

Sai suka ci gaba da tafiya har dai suka gamu da wani yaro, to sai ya kashe shi, (Musa) ya ce: “Yanzu ka kashe rai tsarkakakke ba tare da (ya kashe) wani rai ba? Haqiqa ka zo da wani abu mummuna!”