السورة: Suratun Nahl

الآية : 82

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

To idan suka ba da baya, to kai isar da aike a fili ne kawai a kanka



السورة: Suratun Nahl

الآية : 83

يَعۡرِفُونَ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Suna sane da ni’imar Allah sannan sai su musanta ta, yawancinsu kuwa kafirai ne



السورة: Suratun Nahl

الآية : 84

وَيَوۡمَ نَبۡعَثُ مِن كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدٗا ثُمَّ لَا يُؤۡذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ

Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar da mai shaida daga kowacce al’umma, sannan ba za a yi wa waxanda suka kafirta izini ba, ba kuwa za a karvi uzurin nasu ba



السورة: Suratun Nahl

الآية : 85

وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ ٱلۡعَذَابَ فَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Idan kuma waxanda suka kafirta suka ga azaba, to ba za a sauqaqa musu ba, ba kuma za a saurara musu ba



السورة: Suratun Nahl

الآية : 86

وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْ شُرَكَآءَهُمۡ قَالُواْ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ شُرَكَآؤُنَا ٱلَّذِينَ كُنَّا نَدۡعُواْ مِن دُونِكَۖ فَأَلۡقَوۡاْ إِلَيۡهِمُ ٱلۡقَوۡلَ إِنَّكُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Idan kuma waxanda suka yi tarayya (da Allah) suka ga ababen tarayyarsu (sai) su ce: “Ya Ubangijinmu, waxannan su ne ababen tarayyarmu waxanda muka zamanto muna bauta wa ba Kai ba.” Sai su jefa musu magana (cewa,): “Ku dai lalle maqaryata ne!”



السورة: Suratun Nahl

الآية : 87

وَأَلۡقَوۡاْ إِلَى ٱللَّهِ يَوۡمَئِذٍ ٱلسَّلَمَۖ وَضَلَّ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Kuma a wannan ranar suka miqa wuya ga Allah; kuma duk abin da suka zamanto suna qirqira ya vace musu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 88

ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ زِدۡنَٰهُمۡ عَذَابٗا فَوۡقَ ٱلۡعَذَابِ بِمَا كَانُواْ يُفۡسِدُونَ

Waxanda suka kafirta suka kuma toshe hanyar Allah, to Mun qara musu azaba a kan azabar (da suka cancance ta) saboda varnar da suka zamanto suna yi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 89

وَيَوۡمَ نَبۡعَثُ فِي كُلِّ أُمَّةٖ شَهِيدًا عَلَيۡهِم مِّنۡ أَنفُسِهِمۡۖ وَجِئۡنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِۚ وَنَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ تِبۡيَٰنٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ

Kuma (ka tuna) ranar da za Mu tayar wa kowace al’umma da mai ba da shaida a kansu daga jinsinsu, Mu kuma zo da kai (Annabi Muhammadu) shaida a kan waxannan (wato al’ummarka). Kuma Mun saukar maka da Littafi ne (wato Alqur’ani) don bayani ga kowanne abu, kuma shiriya da rahama da bushara ga Musulmi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 90

۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَٱلۡإِحۡسَٰنِ وَإِيتَآيِٕ ذِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَيَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِ وَٱلۡبَغۡيِۚ يَعِظُكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

Lalle Allah Yana umarni da yin adalci da kyautatawa da kuma bai wa makusanta (taimako), Yana kuma hana alfasha da mummunan aiki da zalunci. Yana gargaxin ku don ku wa’azantu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 91

وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ إِذَا عَٰهَدتُّمۡ وَلَا تَنقُضُواْ ٱلۡأَيۡمَٰنَ بَعۡدَ تَوۡكِيدِهَا وَقَدۡ جَعَلۡتُمُ ٱللَّهَ عَلَيۡكُمۡ كَفِيلًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ

Ku kuma cika alqawarin Allah idan kuka xauki alqawari, kada kuma ku warware rantsuwa bayan kun qarfafa ta, alhali kuwa kun sanya Allah shaida a kanku. Lalle Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 92

وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّتِي نَقَضَتۡ غَزۡلَهَا مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةٍ أَنكَٰثٗا تَتَّخِذُونَ أَيۡمَٰنَكُمۡ دَخَلَۢا بَيۡنَكُمۡ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِيَ أَرۡبَىٰ مِنۡ أُمَّةٍۚ إِنَّمَا يَبۡلُوكُمُ ٱللَّهُ بِهِۦۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kada kuma ku zamanto kamar (mace) wadda ta warware kaxinta wara-wara bayan qarfinsa, kuna xaukar rantse-rantsenku yaudara a tsakaninku, don ganin kasancewar wata al’umma ta fi wata yawa da qarfi. Allah dai Yana jarabtar ku da shi (cika alqawari) ne. Don kuma a ranar alqiyama Ya bayyana muku abin da kuka kasance kuna savani a game da shi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 93

وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَلَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Da kuwa Allah Ya ga dama da Ya sanya ku al’umma xaya (masu addini xaya), sai dai kuma Yana vatar da wanda Ya ga dama Yana kuma shiryar da wanda Ya ga dama. Kuma tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna aikatawa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 94

وَلَا تَتَّخِذُوٓاْ أَيۡمَٰنَكُمۡ دَخَلَۢا بَيۡنَكُمۡ فَتَزِلَّ قَدَمُۢ بَعۡدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُواْ ٱلسُّوٓءَ بِمَا صَدَدتُّمۡ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَكُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Kuma kada ku xauki rantse-rantsenku yaudara a tsakaninku, sai qafafuwanku su zame bayan tabbatarsu, kuma ku xanxani azaba saboda toshe hanyar Allah da kuka yi; kuma (a lahira) kuna da azaba mai girma



السورة: Suratun Nahl

الآية : 95

وَلَا تَشۡتَرُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ إِنَّمَا عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Kada kuma ku sayar da alqawarin Allah da xan kuxi qanqani. Lalle abin da yake wurin Allah shi ya fi muku alheri in kun kasance kun san (haka)



السورة: Suratun Nahl

الآية : 96

مَا عِندَكُمۡ يَنفَدُ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٖۗ وَلَنَجۡزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓاْ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Abin da yake wurinku yana qarewa; abin da kuwa yake wurin Allah wanzajje ne. Lalle kuwa tabbas za Mu saka wa waxanda suka yi haquri ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 97

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 98

فَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

To idan za ka karanta Alqur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaixan korarre (daga rahamar Allah)



السورة: Suratun Nahl

الآية : 99

إِنَّهُۥ لَيۡسَ لَهُۥ سُلۡطَٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ

Lalle shi (Shaixan) ba shi da iko a kan waxanda suka yi imani kuma suke dogara da Ubangijinsu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 100

إِنَّمَا سُلۡطَٰنُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَوَلَّوۡنَهُۥ وَٱلَّذِينَ هُم بِهِۦ مُشۡرِكُونَ

Ikonsa kawai yana kan waxanda suke jivintar sa da kuma waxanda suke yin tarayya da shi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 101

وَإِذَا بَدَّلۡنَآ ءَايَةٗ مَّكَانَ ءَايَةٖ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مُفۡتَرِۭۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Idan kuma Muka musanya wata aya a madadin wata ayar, alhali kuwa Allah ne Mafi sanin abin da Yake saukarwa, sai su ce: “Kai dai mai qirqirar qarya ne kawai!” A’a, ba haka ba ne, yawancinsu ba su san (komai) ba ne



السورة: Suratun Nahl

الآية : 102

قُلۡ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلۡقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ

Ka ce: “Ruhul Qudusi (watau Mala’ika Jibrilu) ne ya saukar da shi daga Ubangijinka da gaskiya don ya tabbatar da waxanda suka yi imani (a kan dugadugansu), kuma shiriya ne da albishir ga Musulmai.”



السورة: Suratun Nahl

الآية : 103

وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّهُمۡ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُهُۥ بَشَرٞۗ لِّسَانُ ٱلَّذِي يُلۡحِدُونَ إِلَيۡهِ أَعۡجَمِيّٞ وَهَٰذَا لِسَانٌ عَرَبِيّٞ مُّبِينٌ

Kuma haqiqa Mun san lalle suna cewa,: “Wani mutun ne kawai yake koya masa shi[1].” Harshen wanda suke karkata zuwa gare shi ajami ne, wannan kuwa harshe ne na Larabci bayyananne


1- Quraishawa suka riqa tuhumar Manzon Allah () yayin da suka gan shi yana magana da wani bawa matashi ba’ajame, suna cewa wai shi ne yake koya masa karatun Alqur’ani.


السورة: Suratun Nahl

الآية : 104

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ لَا يَهۡدِيهِمُ ٱللَّهُ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٌ

Lalle waxanda ba sa yin imani da ayoyin Allah, to Allah ba zai shirye su ba, kuma suna da azaba mai raxaxi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 105

إِنَّمَا يَفۡتَرِي ٱلۡكَذِبَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ

Waxanda ba sa yin imani da ayoyin Allah su ne kawai suke qirqirar qarya; kuma waxannan su ne maqaryata



السورة: Suratun Nahl

الآية : 106

مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنۡ أُكۡرِهَ وَقَلۡبُهُۥ مُطۡمَئِنُّۢ بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلۡكُفۡرِ صَدۡرٗا فَعَلَيۡهِمۡ غَضَبٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٞ

Wanda ya kafirce wa Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta wa alhali kuwa zuciyarsa ta cika da imani, amma kuma wanda ya buxe wa kafirci qirjinsa, to (waxannan) fushin Allah ya tabbata a kansu kuma suna da azaba mai girma



السورة: Suratun Nahl

الآية : 107

ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Wannan kuwa (ya faru) saboda su sun fi son rayuwar duniya a kan ta lahira, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai



السورة: Suratun Nahl

الآية : 108

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ وَسَمۡعِهِمۡ وَأَبۡصَٰرِهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡغَٰفِلُونَ

Waxannan su ne waxanda Allah Ya doxe zukatansu da jinsu da ganinsu, kuma waxannan su ne gafalallu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 109

لَا جَرَمَ أَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Ba shakka lalle su a lahira su ne tavavvu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 110

ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا فُتِنُواْ ثُمَّ جَٰهَدُواْ وَصَبَرُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sannan lalle Ubangjinka (Mai gafara ne da jin qai) ga waxanda suka yi hijira bayan an fitine su, sannan suka yi jihadi suka kuma yi haquri, lalle Ubangijinka, bayansu (waxannan ayyuka) Mai gafara ne, Mai jin qai



السورة: Suratun Nahl

الآية : 111

۞يَوۡمَ تَأۡتِي كُلُّ نَفۡسٖ تُجَٰدِلُ عَن نَّفۡسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفۡسٖ مَّا عَمِلَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Ranar da kowanne rai zai zo yana kare kansa, kuma a cika wa kowanne rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba