السورة: Suratun Nahl

الآية : 52

وَلَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلدِّينُ وَاصِبًاۚ أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ تَتَّقُونَ

Kuma abin da ke sammai da qasa nasa ne, kuma gare Shi ake biyayya tutur. Shin yanzu wanin Allah ne kuke yi wa taqawa?



السورة: Suratun Nahl

الآية : 53

وَمَا بِكُم مِّن نِّعۡمَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيۡهِ تَجۡـَٔرُونَ

Kuma duk abin da kuke da shi na ni’ima to daga Allah ne; sannan kuma idan cuta ta same ku to wurinsa kuke kai kuka



السورة: Suratun Nahl

الآية : 54

ثُمَّ إِذَا كَشَفَ ٱلضُّرَّ عَنكُمۡ إِذَا فَرِيقٞ مِّنكُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ

Sannan kuma lokacin da Ya yaye muku cutar sai a samu wata qungiya daga cikinku suna yin shirka da Ubangijinsu



السورة: Suratun Nahl

الآية : 55

لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Don su butulce wa abin da Muka ba su. To ku xan ji daxi a (duniya), sai dai ba da daxewa ba za ku sani



السورة: Suratun Nahl

الآية : 56

وَيَجۡعَلُونَ لِمَا لَا يَعۡلَمُونَ نَصِيبٗا مِّمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡۗ تَٱللَّهِ لَتُسۡـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمۡ تَفۡتَرُونَ

Suna kuma sanya wani kaso daga abin da Muka arzuta su da shi ga abubuwan da ba su san komai ba. Wallahi tabbas za a tambaye ku game da abin da kuka kasance kuna qirqira



السورة: Suratun Nahl

الآية : 57

وَيَجۡعَلُونَ لِلَّهِ ٱلۡبَنَٰتِ سُبۡحَٰنَهُۥ وَلَهُم مَّا يَشۡتَهُونَ

Suna kuma jingina wa Allah ‘ya’ya mata[1], tsarki ya tabbata a gare Shi, su kuma suna da abin da suke sha’awa (na ‘ya’ya maza)


1- Suna cewa mala’iku mata ne kuma ‘ya’yan Allah ne.


السورة: Suratun Nahl

الآية : 58

وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلۡأُنثَىٰ ظَلَّ وَجۡهُهُۥ مُسۡوَدّٗا وَهُوَ كَظِيمٞ

Kuma idan aka yi wa xayansu albishir da (‘ya) mace sai fuskarsa ta yi baqi qirin yana cike da tsananin baqin ciki



السورة: Suratun Nahl

الآية : 59

يَتَوَٰرَىٰ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ مِن سُوٓءِ مَا بُشِّرَ بِهِۦٓۚ أَيُمۡسِكُهُۥ عَلَىٰ هُونٍ أَمۡ يَدُسُّهُۥ فِي ٱلتُّرَابِۗ أَلَا سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ

Yana vuya daga (idon) mutane saboda munin abin da aka yi masa albishir da shi. Shin zai riqe shi ne a wulaqance ko kuwa zai binne shi ne a cikin qasa? Ku saurara, abin da suke hukuntawa kam ya munana



السورة: Suratun Nahl

الآية : 60

لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ مَثَلُ ٱلسَّوۡءِۖ وَلِلَّهِ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Waxanda ba sa imani da ranar lahira suna da mummunar siffa. Allah kuwa Yana da maxaukakiyar siffa. Kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima



السورة: Suratun Nahl

الآية : 61

وَلَوۡ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلۡمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيۡهَا مِن دَآبَّةٖ وَلَٰكِن يُؤَخِّرُهُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ

Da kuwa Allah Yana kama mutane da laifukansu ne to da bai bar wata dabba (mai tafiya) a bayanta ba (wato qasa), sai dai kuma Yana saurara musu ne har zuwa wani lokaci qayyadajje. To idan ajalinsu ya zo ba za su jinkirta daidai da sa’a guda ba, kuma ba za su gabata ba



السورة: Suratun Nahl

الآية : 62

وَيَجۡعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكۡرَهُونَۚ وَتَصِفُ أَلۡسِنَتُهُمُ ٱلۡكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ لَا جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ ٱلنَّارَ وَأَنَّهُم مُّفۡرَطُونَ

Suna kuma sanya wa Allah abin da suke qi, kuma harsunansu suna bayanin qaryar cewa, suna da mafi kyan sakamako; ba shakka, lalle suna da (sakamakon) wuta, kuma haqiqa su waxanda za a bar su ne (cikinta har abada)



السورة: Suratun Nahl

الآية : 63

تَٱللَّهِ لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٖ مِّن قَبۡلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ ٱلۡيَوۡمَ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Wallahi haqiqa Mun aiko (manzanni) zuwa ga al’ummun da suke gabaninka, sai Shaixan ya qawata musu ayyukansu, kuma shi ne majivincin al’amuransu a yau, kuma suna da azaba mai raxaxi



السورة: Suratun Nahl

الآية : 64

وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِي ٱخۡتَلَفُواْ فِيهِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٗ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Kuma ba Mu saukar maka da Littafi ba sai don ka yi musu bayanin abin da suka yi savani game da shi, kuma shiriya ne da rahama ga mutanen da suke yin imani



السورة: Suratun Nahl

الآية : 65

وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ

Allah kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke ji



السورة: Suratun Nahl

الآية : 66

وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةٗۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهِۦ مِنۢ بَيۡنِ فَرۡثٖ وَدَمٖ لَّبَنًا خَالِصٗا سَآئِغٗا لِّلشَّـٰرِبِينَ

Lalle kuma kuna da wata izina a game da dabbobin ni’ima; Muna shayar da ku da abin da yake cikin cikkunansu (mai fitowa) ta tsakankanin uwar hanji da jinni; nono tatacce mai daxin kwankwaxa ga masu sha



السورة: Suratun Nahl

الآية : 67

وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلۡأَعۡنَٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنۡهُ سَكَرٗا وَرِزۡقًا حَسَنًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Daga kuma ‘ya’yan dabinai da na inabai kuna yin giya da shi[1], da kuma arziki mai kyau. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutanen da suke hankalta


1- Wannan ayar ta sauka kafin a haramta shan giya. Daga baya Allah () ya haramta duk wani abu mai gusar da hankali.


السورة: Suratun Nahl

الآية : 68

وَأَوۡحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحۡلِ أَنِ ٱتَّخِذِي مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتٗا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعۡرِشُونَ

Ubangijinka kuma Ya kimsa wa qudan zuma cewa,: “Ki gina gidaje a duwatsu da kan bishiyoyi da kuma rufin da (mutane) suke yi”



السورة: Suratun Nahl

الآية : 69

ثُمَّ كُلِي مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ فَٱسۡلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلٗاۚ يَخۡرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٞ مُّخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٞ لِّلنَّاسِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

“Sannan kuma ki ci daga kowanne ‘ya’yan itace, kuma ki shiga hanyoyin Ubangijinki horarru (gare ki).” Abin sha mai launi daban-daban yana fitowa daga cikin cikinta; a cikinsa (kuma) da akwai waraka ga mutane. Lalle a game da wannan akwai aya ga mutane masu tunani



السورة: Suratun Nahl

الآية : 70

وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ ثُمَّ يَتَوَفَّىٰكُمۡۚ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرۡذَلِ ٱلۡعُمُرِ لِكَيۡ لَا يَعۡلَمَ بَعۡدَ عِلۡمٖ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٞ قَدِيرٞ

Kuma Allah ne Ya halicce ku, sannan kuma Shi zai kashe ku. Daga cikinku akwai wanda zai zama tsoho tukuf don kada ya san komai bayan (da can yana da) sani. Lalle Allah Masani ne, Mai iko



السورة: Suratun Nahl

الآية : 71

وَٱللَّهُ فَضَّلَ بَعۡضَكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلرِّزۡقِۚ فَمَا ٱلَّذِينَ فُضِّلُواْ بِرَآدِّي رِزۡقِهِمۡ عَلَىٰ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَهُمۡ فِيهِ سَوَآءٌۚ أَفَبِنِعۡمَةِ ٱللَّهِ يَجۡحَدُونَ

Allah kuma Ya fifita sashenku a kan wani sashi a arziki. Waxanda aka fifita xin ba za su ba da arzikin nasu ga bayinsu ba don su zama daidai a cikinsa[1]. Shin da ni’imar Allah ne suke jayayya?


1- To me ya sa kafirai suka yarda su sanya wa Allah kishiyoyi daga cikin bayinsa, amma su ba su amince bayinsu su yi tarayya da su a cikin dukiyoyinsu ba?


السورة: Suratun Nahl

الآية : 72

وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةٗ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ أَفَبِٱلۡبَٰطِلِ يُؤۡمِنُونَ وَبِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ هُمۡ يَكۡفُرُونَ

Allah kuma Ya sanya muku matan aure daga jinsinku, Ya kuma sanya muku ‘ya’yaye da jikoki daga matayen naku, Ya kuma arzuta ku da abubuwa tsarkaka. Yanzu da qarya suke yin imani kuma suke kafirce wa ni’imar Allah?



السورة: Suratun Nahl

الآية : 73

وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمۡلِكُ لَهُمۡ رِزۡقٗا مِّنَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡتَطِيعُونَ

Suna kuma bauta wa wasu ba Allah ba, waxanda ba sa mallakar musu wani arziki a sammai da qasa, ba za kuma su iya ba



السورة: Suratun Nahl

الآية : 74

فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Kada kuma ku sanya wa Allah abokan tarayya. Lalle Allah Yana sane, ku ne ba ku sani ba



السورة: Suratun Nahl

الآية : 75

۞ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا عَبۡدٗا مَّمۡلُوكٗا لَّا يَقۡدِرُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَمَن رَّزَقۡنَٰهُ مِنَّا رِزۡقًا حَسَنٗا فَهُوَ يُنفِقُ مِنۡهُ سِرّٗا وَجَهۡرًاۖ هَلۡ يَسۡتَوُۥنَۚ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Allah kuma Ya ba da misali da bawan da aka mallaka, ba shi da iko a kan komai, da kuma wanda Muka bai wa arziki nagari daga gare Mu, to shi kuma yana ciyarwa daga shi (arzikin) a voye da kuma sarari; yanzu za su yi daidai? (Ai ba za su yi daidai ba). To godiya ta tabbata ga Allah. A’a, yawancinsu dai ba su san (haka) ba ne



السورة: Suratun Nahl

الآية : 76

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا رَّجُلَيۡنِ أَحَدُهُمَآ أَبۡكَمُ لَا يَقۡدِرُ عَلَىٰ شَيۡءٖ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوۡلَىٰهُ أَيۡنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأۡتِ بِخَيۡرٍ هَلۡ يَسۡتَوِي هُوَ وَمَن يَأۡمُرُ بِٱلۡعَدۡلِ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Allah kuma Ya ba da wani misali da mutum biyu, xayansu bebe ne ba ya iya yin komai, kuma ya zama nauyi a kan mai gidansa, duk inda ya fuskantar da shi ba zai zo da wani alheri ba. Yanzu shi zai yi daidai da wanda yake umarni da adalci kuma yana bisa tafarki madaidaici?



السورة: Suratun Nahl

الآية : 77

وَلِلَّهِ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَمَآ أَمۡرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمۡحِ ٱلۡبَصَرِ أَوۡ هُوَ أَقۡرَبُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma Allah ne Masanin gaibu na sammai da qasa. Al’amarin alqiyama kuma ba komai ba ne face kamar qiftawar ido ko kuma ya fi haka kusa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



السورة: Suratun Nahl

الآية : 78

وَٱللَّهُ أَخۡرَجَكُم مِّنۢ بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Allah ne kuma Ya fito da ku daga cikkunan iyayenku, ba ku san komai ba, Ya kuma sanya muku ji da gani da kuma zukata don ku gode masa



السورة: Suratun Nahl

الآية : 79

أَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ مُسَخَّرَٰتٖ فِي جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba sa ganin tsuntsaye da aka lamunce wa (tashi) a sararin sama, ba mai riqe su sai Allah? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga mutane masu yin imani



السورة: Suratun Nahl

الآية : 80

وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۢ بُيُوتِكُمۡ سَكَنٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ ٱلۡأَنۡعَٰمِ بُيُوتٗا تَسۡتَخِفُّونَهَا يَوۡمَ ظَعۡنِكُمۡ وَيَوۡمَ إِقَامَتِكُمۡ وَمِنۡ أَصۡوَافِهَا وَأَوۡبَارِهَا وَأَشۡعَارِهَآ أَثَٰثٗا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ

Allah ne kuma Ya sanya muku gidajenku wuraren hutawarku, Ya kuma sanya muku gidaje daga fatun dabbobin ni’ima, kuna xaukar su ba nauyi a ranar tafiyarku da ranar saukarku. Daga kuma gashin (tumaki) da gashin raquma da gashin (awaki, Ya sanya muku) kayan shimfixa da kuma (kayan) jin daxi zuwa wani xan lokaci



السورة: Suratun Nahl

الآية : 81

وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَٰلٗا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡجِبَالِ أَكۡنَٰنٗا وَجَعَلَ لَكُمۡ سَرَٰبِيلَ تَقِيكُمُ ٱلۡحَرَّ وَسَرَٰبِيلَ تَقِيكُم بَأۡسَكُمۡۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُسۡلِمُونَ

Kuma Allah ne Ya sanya muku inuwoyi daga abin da Ya halitta, Ya kuma sanya muku xakuna daga duwatsu, Ya kuma sanya muku riguna da suke kare ku daga zafi, da kuma riguna (na sulke) da suke kare ku (daga makamai) a fagen daga. Kamar haka ne Yake cika muku ni’imarsa don ku miqa wuya