وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن مَّنَعَ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ أَن يُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ وَسَعَىٰ فِي خَرَابِهَآۚ أُوْلَـٰٓئِكَ مَا كَانَ لَهُمۡ أَن يَدۡخُلُوهَآ إِلَّا خَآئِفِينَۚ لَهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا خِزۡيٞ وَلَهُمۡ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٞ
Wane ne mafi zalunci kamar wanda ya hana masallatan Allah a riqa ambaton sunansa a cikinsu, ya yi ta qoqari wajen rushe su? Waxannan bai kamata su shige su ba sai a cikin halin tsoro. Za su gamu da wulaqanci a duniya a lahira kuma suna da wata azaba mai girma
وَلِلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ فَأَيۡنَمَا تُوَلُّواْ فَثَمَّ وَجۡهُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ
Gabas da yamma kuma na Allah ne. Duk inda aka fuskantar da ku to can ma alqiblar Allah ce. Lalle Allah Mai yalwar falala ne, kuma Mai yawan sani
وَقَالُواْ ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ وَلَدٗاۗ سُبۡحَٰنَهُۥۖ بَل لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ
Kuma suka ce: “Allah Yana da xa”. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Bari (wannan magana)! Duk abin da yake cikin sammai da qasa nasa ne, kuma dukkansu masu biyayya ne a gare Shi
بَدِيعُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Shi ne Maqirqirin halittar sammai da qasa; kuma idan zai zartar da wani al’amari sai kawai Ya ce da shi: “Kasance”, sai ya kasance
وَقَالَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ لَوۡلَا يُكَلِّمُنَا ٱللَّهُ أَوۡ تَأۡتِينَآ ءَايَةٞۗ كَذَٰلِكَ قَالَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّثۡلَ قَوۡلِهِمۡۘ تَشَٰبَهَتۡ قُلُوبُهُمۡۗ قَدۡ بَيَّنَّا ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
Waxanda ba su da ilimi kuma suka ce, “Me zai hana Allah Ya yi magana da mu ko kuma wata aya ta zo mana?” Kamar haka ne waxanda suka gabace su suka faxi irin wannan maganar tasu. Zukatansu sun yi kama da juna. Haqiqa mun yi bayanin ayoyi ga mutane masu sakankancewa
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ بَشِيرٗا وَنَذِيرٗاۖ وَلَا تُسۡـَٔلُ عَنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡجَحِيمِ
Lalle Mu Mun aiko ka da gaskiya, kana mai albishir kuma kana mai gargaxi, ba kuma za a tambaye ka ba game da ‘yan wutar Jahima
وَلَن تَرۡضَىٰ عَنكَ ٱلۡيَهُودُ وَلَا ٱلنَّصَٰرَىٰ حَتَّىٰ تَتَّبِعَ مِلَّتَهُمۡۗ قُلۡ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلۡهُدَىٰۗ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ ٱلَّذِي جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٍ
Yahudawa da Nasara ba za su tava yarda da kai ba har sai ka bi addininsu. Ka ce: “Shiriyar Allah lalle ita ce shiriya”. Idan har ka bi son zuciyarsu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to ba ka da wani majivinci ko mai taimakonka wajen Allah
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَتۡلُونَهُۥ حَقَّ تِلَاوَتِهِۦٓ أُوْلَـٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ
Waxanda Muka saukar musu da littafi suna karanta shi yadda ya cancanta a karanta shi, waxannan su ne suke yin imani da shi. Kuma waxanda suka kafirce masa to waxannan su ne hasararru
يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتِيَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ وَأَنِّي فَضَّلۡتُكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ya ku Banu Isra’ila, ku tuna ni’imar da Na yi muku, kuma lalle Ni Na fifita ku a kan sauran mutanen duniya (na zamaninku)
وَٱتَّقُواْ يَوۡمٗا لَّا تَجۡزِي نَفۡسٌ عَن نَّفۡسٖ شَيۡـٔٗا وَلَا يُقۡبَلُ مِنۡهَا عَدۡلٞ وَلَا تَنفَعُهَا شَفَٰعَةٞ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ
Kuma ku kiyayi wani yini da wani rai ba zai isar wa da wani rai komai ba, kuma ba za a karvi wata fansa daga gare shi ba, kuma ceto ba zai amfane shi ba, kuma su ba za a taimaka musu ba
۞وَإِذِ ٱبۡتَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ رَبُّهُۥ بِكَلِمَٰتٖ فَأَتَمَّهُنَّۖ قَالَ إِنِّي جَاعِلُكَ لِلنَّاسِ إِمَامٗاۖ قَالَ وَمِن ذُرِّيَّتِيۖ قَالَ لَا يَنَالُ عَهۡدِي ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma ka tuna lokacin da Ubangijin Ibrahimu Ya jarrabe shi da wasu kalmomi, sai ya cika su, sai Ya ce: “Ni zan naxa ka shugaba ga mutane”. Sai (Ibrahimu) ya ce: “Har da kuma zurriyata”; Sai (Allah) Ya ce: “Alqawarina ba zai shafi azzalumai ba.”
وَإِذۡ جَعَلۡنَا ٱلۡبَيۡتَ مَثَابَةٗ لِّلنَّاسِ وَأَمۡنٗا وَٱتَّخِذُواْ مِن مَّقَامِ إِبۡرَٰهِـۧمَ مُصَلّٗىۖ وَعَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيۡتِيَ لِلطَّآئِفِينَ وَٱلۡعَٰكِفِينَ وَٱلرُّكَّعِ ٱلسُّجُودِ
Kuma ka tuna lokacin da Muka sanya wannan Xaki ya zama matattara ga mutane da kuma aminci; kuma ku mayar da Maqamu Ibrahim wajen salla; kuma Muka yi umarni ga Ibrahim da Isma’ila da cewa: “Ku tsarkake Xakina don masu xawafi da masu i’itikafi da masu ruku’u da sujjada”
وَإِذۡ قَالَ إِبۡرَٰهِـۧمُ رَبِّ ٱجۡعَلۡ هَٰذَا بَلَدًا ءَامِنٗا وَٱرۡزُقۡ أَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلثَّمَرَٰتِ مَنۡ ءَامَنَ مِنۡهُم بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ قَالَ وَمَن كَفَرَ فَأُمَتِّعُهُۥ قَلِيلٗا ثُمَّ أَضۡطَرُّهُۥٓ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلنَّارِۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu ya ce: “Ya Ubangijina, Ka sanya wannan (wuri) ya zama gari mai aminci, kuma Ka arzuta mutanensa da kayan marmari, (amma) wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira daga cikinsu”. Sai (Allah) Ya ce: “Har ma wanda ya kafirta, zan jiyar da shi daxi kaxan, sannan in tilasa masa shiga azabar wuta, tir da wannan makoma.”
وَإِذۡ يَرۡفَعُ إِبۡرَٰهِـۧمُ ٱلۡقَوَاعِدَ مِنَ ٱلۡبَيۡتِ وَإِسۡمَٰعِيلُ رَبَّنَا تَقَبَّلۡ مِنَّآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Kuma ka tuna lokacin da Ibrahimu yake xaga harsashen ginin Xakin Ka’aba tare da Isma’ila, suna cewa: “Ya Ubangijinmu Ka karva mana; lalle Kai Mai ji ne Mai gani.”
رَبَّنَا وَٱجۡعَلۡنَا مُسۡلِمَيۡنِ لَكَ وَمِن ذُرِّيَّتِنَآ أُمَّةٗ مُّسۡلِمَةٗ لَّكَ وَأَرِنَا مَنَاسِكَنَا وَتُبۡ عَلَيۡنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلتَّوَّابُ ٱلرَّحِيمُ
“Ya Ubangijinmu, Ka sanya mu masu miqa wuya gare Ka, kuma a cikin zurriyarmu ma (Ka samar) da wata al’umma mai miqa wuya gare Ka, kuma Ka nuna mana ayyaukan ibadarmu, kuma Ka karvi tubanmu, lalle Kai Mai yawan karvar tuba ne Mai jin qai.”
رَبَّنَا وَٱبۡعَثۡ فِيهِمۡ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِكَ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَيُزَكِّيهِمۡۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
“Ya Ubangijinmu, Ka aiko da wani manzo daga cikinsu, da zai riqa karanta musu ayoyinka, kuma yana koyar da su Littafi da hikima, kuma ya riqa yi musu tarbiyya. Lalle kai Mabuwayi ne, Mai hikima.”
وَمَن يَرۡغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبۡرَٰهِـۧمَ إِلَّا مَن سَفِهَ نَفۡسَهُۥۚ وَلَقَدِ ٱصۡطَفَيۡنَٰهُ فِي ٱلدُّنۡيَاۖ وَإِنَّهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Babu kuma wanda zai qi addinin Ibrahimu sai wanda bai san ciwon kansa ba. Kuma haqiqa Mun zave shi a duniya, kuma shi a lahira yana cikin mutanen qwarai
إِذۡ قَالَ لَهُۥ رَبُّهُۥٓ أَسۡلِمۡۖ قَالَ أَسۡلَمۡتُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ka tuna lokacin da Ubangijijinsa Ya ce masa: “Ka miqa wuya”, sai ya ce: “Na miqa wuya ga Ubangijin talikai.”
وَوَصَّىٰ بِهَآ إِبۡرَٰهِـۧمُ بَنِيهِ وَيَعۡقُوبُ يَٰبَنِيَّ إِنَّ ٱللَّهَ ٱصۡطَفَىٰ لَكُمُ ٱلدِّينَ فَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنتُم مُّسۡلِمُونَ
Kuma Ibrahimu da Ya’aqubu suka yi wasiyya da wannan ga ‘ya’yansu cewa: “Ya ‘ya’yana, lalle Allah Ya zava muku addini, don haka kada ku mutu face kuna Musulmi.”
أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ حَضَرَ يَعۡقُوبَ ٱلۡمَوۡتُ إِذۡ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعۡبُدُونَ مِنۢ بَعۡدِيۖ قَالُواْ نَعۡبُدُ إِلَٰهَكَ وَإِلَٰهَ ءَابَآئِكَ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ إِلَٰهٗا وَٰحِدٗا وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Ko kuna nan ne lokacin da mutuwa ta zo wa Ya’aqubu, lokacin da ya ce wa ‘ya’yansa: “Me za ku bauta wa a bayana?” Sai suka ce: “Za mu bauta wa abin bautarka kuma abin bautar iyayenka, Ibrahim da Isma’il da Ishaq, abin bauta guda xaya, kuma mu gare Shi muke miqa wuya.”
تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Waccan al’umma ce da ta riga ta wuce; abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku ba game da abin da suka kasance suna aikatawa.”
وَقَالُواْ كُونُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰ تَهۡتَدُواْۗ قُلۡ بَلۡ مِلَّةَ إِبۡرَٰهِـۧمَ حَنِيفٗاۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ
Kuma suka ce: “Ku zama Yahudawa ko Nasara za ku shiriya”. Ka ce: “A’a! (Za mu bi) addinin Ibrahimu ne wanda yake miqe totar, kuma bai zamo daga cikin masu shirka ba.”
قُولُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡنَا وَمَآ أُنزِلَ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَمَآ أُوتِيَ مُوسَىٰ وَعِيسَىٰ وَمَآ أُوتِيَ ٱلنَّبِيُّونَ مِن رَّبِّهِمۡ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّنۡهُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُسۡلِمُونَ
Ku ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar mana, da abin da aka saukar wa Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki da abin da aka ba wa Musa da Isa da abin da aka ba annabawa duka daga Ubangijinsu, kuma ba ma nuna bambanci tsakanin wani daga cikinsu, kuma mu gare Shi muke miqa wuya.”
فَإِنۡ ءَامَنُواْ بِمِثۡلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا هُمۡ فِي شِقَاقٖۖ فَسَيَكۡفِيكَهُمُ ٱللَّهُۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Don haka idan sun yi imani da irin abin da kuka yi imani da shi, to haqiqa sun shiriya, idan kuwa suka juya da baya, to haqiqa su suna cikin savani. To da sannu Allah zai isar maka da su, kuma Shi Mai ji ne, Mai gani
صِبۡغَةَ ٱللَّهِ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ صِبۡغَةٗۖ وَنَحۡنُ لَهُۥ عَٰبِدُونَ
Rinin Allah, wane ne kuwa ya fi Allah kyan rini? Kuma mu masu bauta ne a gare Shi
قُلۡ أَتُحَآجُّونَنَا فِي ٱللَّهِ وَهُوَ رَبُّنَا وَرَبُّكُمۡ وَلَنَآ أَعۡمَٰلُنَا وَلَكُمۡ أَعۡمَٰلُكُمۡ وَنَحۡنُ لَهُۥ مُخۡلِصُونَ
Ka ce, “Shin za ku yi jayayya da mu ne game da sha’anin Allah, alhalin Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku? Kuma ayyukanmu namu ne, ayyukanku kuma naku ne, kuma mu masu tsarkake ayyuka ne gare Shi (Allah)
أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Ko kuma kuna cewa ne, “Lalle Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da jikoki sun kasance Yahudawa ne ko Nasara?” Ka ce: “Ku ne kuka fi sani ko kuma Allah?” Kuma ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya voye shaidar da take wajensa daga Allah, kuma Allah ba rafkananne ne ba game da abin da kuke aikatawa
تِلۡكَ أُمَّةٞ قَدۡ خَلَتۡۖ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَلَكُم مَّا كَسَبۡتُمۡۖ وَلَا تُسۡـَٔلُونَ عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Waccan al’umma ce da ta riga ta wuce, abin da ta aikata mallakarta ne, ku ma abin da kuka aikata naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba.”