وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلۡإِيمَٰنَ مِن قَبۡلِهِمۡ يُحِبُّونَ مَنۡ هَاجَرَ إِلَيۡهِمۡ وَلَا يَجِدُونَ فِي صُدُورِهِمۡ حَاجَةٗ مِّمَّآ أُوتُواْ وَيُؤۡثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ وَلَوۡ كَانَ بِهِمۡ خَصَاصَةٞۚ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفۡسِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
Da kuma waxanda suka tanadi gida (mutanen Madina) suka kuma (karvi) imani gabaninsu (masu hijira), suna son waxanda suka yi hijira zuwa gare su, ba sa samun wani qyashi a zukatansu game da abin da aka ba su (masu hijira), suna kuma fifita (masu hijira) a kan kawunansu, ko da kuwa suna da tsananin buqata. Duk kuwa wanda aka kiyaye shi daga son kansa, to waxannan su ne masu babban rabo
وَٱلَّذِينَ جَآءُو مِنۢ بَعۡدِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱغۡفِرۡ لَنَا وَلِإِخۡوَٰنِنَا ٱلَّذِينَ سَبَقُونَا بِٱلۡإِيمَٰنِ وَلَا تَجۡعَلۡ فِي قُلُوبِنَا غِلّٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ رَبَّنَآ إِنَّكَ رَءُوفٞ رَّحِيمٌ
Duk kuma waxanda suka zo daga bayansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana mu da ‘yan’uwanmu waxanda suka rigaye mu yin imani, kada kuma Ka sanya wata qullata a zukatanmu game da waxanda suka yi imani, ya Ubangijinmu, lalle Kai Mai tausayawa ne, Mai jin qai.”
۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُواْ يَقُولُونَ لِإِخۡوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَئِنۡ أُخۡرِجۡتُمۡ لَنَخۡرُجَنَّ مَعَكُمۡ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمۡ أَحَدًا أَبَدٗا وَإِن قُوتِلۡتُمۡ لَنَنصُرَنَّكُمۡ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ
Ba ka ga waxanda suka yi munafunci suna ce wa ‘yan’uwansu waxanda suka kafirta daga ma’abota littafi: “Tabbas idan aka fitar da ku, lalle za mu fita tare da ku, ba kuma za mu bi wani mutum game da ku ba har adaba, kuma idan aka yaqe ku tabbas za mu taimake ku.” Allah kuma Ya san tabbas qarya suke yi
لَئِنۡ أُخۡرِجُواْ لَا يَخۡرُجُونَ مَعَهُمۡ وَلَئِن قُوتِلُواْ لَا يَنصُرُونَهُمۡ وَلَئِن نَّصَرُوهُمۡ لَيُوَلُّنَّ ٱلۡأَدۡبَٰرَ ثُمَّ لَا يُنصَرُونَ
Tabbas idan aka fitar da su ba za su fita tare da su ba, kuma tabbas idan aka yaqe su ba za su taimake su ba, tabbas kuwa idan ma sun taimake su xin, lalle za su gudu su ba da baya, sannan kuma ba za a ba su nasara ba
لَأَنتُمۡ أَشَدُّ رَهۡبَةٗ فِي صُدُورِهِم مِّنَ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَفۡقَهُونَ
Tabbas ku suka fi tsoro a zukatansu fiye da Allah. Wannan kuwa saboda su mutane ne da ba sa fahimta
لَا يُقَٰتِلُونَكُمۡ جَمِيعًا إِلَّا فِي قُرٗى مُّحَصَّنَةٍ أَوۡ مِن وَرَآءِ جُدُرِۭۚ بَأۡسُهُم بَيۡنَهُمۡ شَدِيدٞۚ تَحۡسَبُهُمۡ جَمِيعٗا وَقُلُوبُهُمۡ شَتَّىٰۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡقِلُونَ
Ba sa yaqar ku a tare sai a cikin wasu alqaryu katangaggu ko ta bayan katangu. Yaqi a tsakaninsu mai tsanani ne. Za ka tsammaci kansu a haxe yake, alhali zukatansu a rarrabe suke. Wannan kuwa saboda cewar su mutane ne da ba sa hankalta
كَمَثَلِ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ قَرِيبٗاۖ ذَاقُواْ وَبَالَ أَمۡرِهِمۡ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Sun yi kama da waxanda suke a gabaninsu ba da daxewa ba, sun xanxani azabar al’amarinsu, suna kuma da (sakamakon) azaba mai raxaxi
كَمَثَلِ ٱلشَّيۡطَٰنِ إِذۡ قَالَ لِلۡإِنسَٰنِ ٱكۡفُرۡ فَلَمَّا كَفَرَ قَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Sun yi kama da Shaixan lokacin da ya ce wa mutum: “Ka kafirta.” To yayin da ya kafirta sai ya ce: “Lalle ni ba ruwana da kai, lalle ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai.”
فَكَانَ عَٰقِبَتَهُمَآ أَنَّهُمَا فِي ٱلنَّارِ خَٰلِدَيۡنِ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَـٰٓؤُاْ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Sai qarshen al’amarinsu ya kasance cewa su duka biyun masu dawwama ne cikin wuta. Wannan kuwa shi ne sakamakon azzalumai
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلۡتَنظُرۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ لِغَدٖۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma kowane rai ya dubi abin da ya gabatar don gobe (lahira); ku kuma kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ نَسُواْ ٱللَّهَ فَأَنسَىٰهُمۡ أَنفُسَهُمۡۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ
Kada kuma ku zama kamar waxanda suka manta da Allah, sai Ya mantar da su kawunansu. Waxannan su ne fasiqai
لَا يَسۡتَوِيٓ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۚ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ
‘Yan wuta da ‘yan Aljanna ba za su yi daidai ba. ‘Yan Aljanna su ne masu rabauta
لَوۡ أَنزَلۡنَا هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ عَلَىٰ جَبَلٖ لَّرَأَيۡتَهُۥ خَٰشِعٗا مُّتَصَدِّعٗا مِّنۡ خَشۡيَةِ ٱللَّهِۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَمۡثَٰلُ نَضۡرِبُهَا لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ
Da za Mu saukar da wannan Alqur’ani ga wani dutse, da lalle ka gan shi yana mai qasqantar da kai mai tsattsagewa don tsoron Allah. Waxannan misalan Muna buga wa mutane su ne don su yi tunani
هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ
Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Masanin voye da sarari; kuma Shi ne Mai rahama, Mai jin qai
هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Shi ne Allah wanda babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi; Shi ne Sarki, Mai tsarki, Amintacce, Mai amintarwa, Mai kula da komai, Mabuwayi, Mai tsananin qarfi; Mai nuna isa. Allah Ya tsarkaka daga abin da suke tara (Shi da shi)
هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Shi ne Allah Mahalicci, Mai qagawa Mai surantawa[1]; Yana da sunaye mafiya kyau. Duk abin da yake cikin sammai da qasa yana tsarkake Shi; kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima
1- Watau mai suranta kamannin abin da ya halitta yadda ya ga dama.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُواْ عَدُوِّي وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِيَآءَ تُلۡقُونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَقَدۡ كَفَرُواْ بِمَا جَآءَكُم مِّنَ ٱلۡحَقِّ يُخۡرِجُونَ ٱلرَّسُولَ وَإِيَّاكُمۡ أَن تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ رَبِّكُمۡ إِن كُنتُمۡ خَرَجۡتُمۡ جِهَٰدٗا فِي سَبِيلِي وَٱبۡتِغَآءَ مَرۡضَاتِيۚ تُسِرُّونَ إِلَيۡهِم بِٱلۡمَوَدَّةِ وَأَنَا۠ أَعۡلَمُ بِمَآ أَخۡفَيۡتُمۡ وَمَآ أَعۡلَنتُمۡۚ وَمَن يَفۡعَلۡهُ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku riqi maqiyana kuma maqiyanku masoya, kuna nuna musu soyayya, alhali kuwa sun kafirce wa abin da ya zo muku na gaskiya, suna fitar da Manzo har da ku kanku don kun yi imani da Allah Ubangijinku, idan har kun zamanto kun fito don yin jihadi saboda Ni da kuma neman yardata. Kuna voye qaunarku gare su, alhali kuwa Ina sane da abin da kuka voye da kuma abin da kuka bayyana. Duk kuwa wanda ya aikata haka daga cikinku, to haqiqa ya vace wa hanya madaidaiciya
إِن يَثۡقَفُوكُمۡ يَكُونُواْ لَكُمۡ أَعۡدَآءٗ وَيَبۡسُطُوٓاْ إِلَيۡكُمۡ أَيۡدِيَهُمۡ وَأَلۡسِنَتَهُم بِٱلسُّوٓءِ وَوَدُّواْ لَوۡ تَكۡفُرُونَ
Idan suka samu nasara a kanku za su zama abokan gabanku, kuma za su miqa hannayensu da harsunansu zuwa gare ku don munanawa, sun kuma yi burin ina ma da za ku kafirta
لَن تَنفَعَكُمۡ أَرۡحَامُكُمۡ وَلَآ أَوۡلَٰدُكُمۡۚ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَفۡصِلُ بَيۡنَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Danginku da ‘ya’yanku ba za su amfana muku komai ba. A ranar alqiyama kuma za a yi hukunci a tsakaninku da su. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne
قَدۡ كَانَتۡ لَكُمۡ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ إِذۡ قَالُواْ لِقَوۡمِهِمۡ إِنَّا بُرَءَـٰٓؤُاْ مِنكُمۡ وَمِمَّا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ كَفَرۡنَا بِكُمۡ وَبَدَا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةُ وَٱلۡبَغۡضَآءُ أَبَدًا حَتَّىٰ تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥٓ إِلَّا قَوۡلَ إِبۡرَٰهِيمَ لِأَبِيهِ لَأَسۡتَغۡفِرَنَّ لَكَ وَمَآ أَمۡلِكُ لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۖ رَّبَّنَا عَلَيۡكَ تَوَكَّلۡنَا وَإِلَيۡكَ أَنَبۡنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ
Haqiqa kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku game da Ibrahimu da waxanda suke tare da shi, lokacin da suka ce da mutanensu: “Lalle mu ba ruwanmu da ku, har ma da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, mun kafirce muku, kuma gaba da qiyayya sun bayyana a tsakaninmu da ku har abada, har sai kun yi imani da Allah Shi kaxai, in ban da faxar Ibrahimu ga babansa cewa: ‘Lalle zan nema maka gafara, ba na kuma amfana maka komai game da (sakamakon) Allah’; ya Ubangijinmu gare Ka muka dogara, kuma zuwa wurinka muka mayar da lamuranmu, kuma makoma zuwa gare Ka ne
رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ وَٱغۡفِرۡ لَنَا رَبَّنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
“Ya Ubangijinmu, kada Ka sanya mu fitina ga waxanda suka kafirta, Ka kuma gafarta mana ya Ubangijinmu; lalle Kai ne Mabuwayi, Mai hikima.”
لَقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِيهِمۡ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَۚ وَمَن يَتَوَلَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ
Haqiqa abin koyi kyakkyawa ya kasance a gare ku game da su, ga duk wanda ya kasance yana kyakkyawan fatar haxuwa da Allah da ranar lahira. Duk kuma wanda ya ba da baya, to lalle Allah Shi ne Mawadaci, Sha-Yabo
۞عَسَى ٱللَّهُ أَن يَجۡعَلَ بَيۡنَكُمۡ وَبَيۡنَ ٱلَّذِينَ عَادَيۡتُم مِّنۡهُم مَّوَدَّةٗۚ وَٱللَّهُ قَدِيرٞۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Zai yiwu Allah Ya sanya qauna tsakaninku da waxanda kuka yi gaba da su. Allah kuwa Mai ikon (yin haka) ne. Allah kuma Mai gafara ne Mai jin qai
لَّا يَنۡهَىٰكُمُ ٱللَّهُ عَنِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يُقَٰتِلُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَلَمۡ يُخۡرِجُوكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ أَن تَبَرُّوهُمۡ وَتُقۡسِطُوٓاْ إِلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُقۡسِطِينَ
Allah bai hana ku ba game da waxanda ba su yaqe ku don addini ba, ba su kuma fitar da ku daga gidajenku ba, kan ku kyautata musu, ku kuma yi musu adalci. Lalle Allah Yana son masu adalci
إِنَّمَا يَنۡهَىٰكُمُ ٱللَّهُ عَنِ ٱلَّذِينَ قَٰتَلُوكُمۡ فِي ٱلدِّينِ وَأَخۡرَجُوكُم مِّن دِيَٰرِكُمۡ وَظَٰهَرُواْ عَلَىٰٓ إِخۡرَاجِكُمۡ أَن تَوَلَّوۡهُمۡۚ وَمَن يَتَوَلَّهُمۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ
Allah kawai Yana hana ku ne a kan ku qaunaci waxanda suka yaqe ku don addini, suka kuma fitar da ku daga gidajenku, suka kuma taimaka a kan fitar da ku. Duk kuwa wanda ya qaunace su, to waxannan su ne azzalumai
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا جَآءَكُمُ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ مُهَٰجِرَٰتٖ فَٱمۡتَحِنُوهُنَّۖ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِإِيمَٰنِهِنَّۖ فَإِنۡ عَلِمۡتُمُوهُنَّ مُؤۡمِنَٰتٖ فَلَا تَرۡجِعُوهُنَّ إِلَى ٱلۡكُفَّارِۖ لَا هُنَّ حِلّٞ لَّهُمۡ وَلَا هُمۡ يَحِلُّونَ لَهُنَّۖ وَءَاتُوهُم مَّآ أَنفَقُواْۚ وَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ أَن تَنكِحُوهُنَّ إِذَآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ أُجُورَهُنَّۚ وَلَا تُمۡسِكُواْ بِعِصَمِ ٱلۡكَوَافِرِ وَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقۡتُمۡ وَلۡيَسۡـَٔلُواْ مَآ أَنفَقُواْۚ ذَٰلِكُمۡ حُكۡمُ ٱللَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَكُمۡۖ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan muminai mata sun zo muku suna masu yin hijira, sai ku jarraba su; Allah ne Ya fi sanin imaninsu; to idan kuka san cewa su muminai ne, to kada ku mayar da su wurin kafirai; su ba halal ba ne gare su (kafirai), su ma (kafiran) ba halal ba ne a gare su; kuma ku ba su abin da suka kashe. Kuma babu laifi a kanku ku aure su idan kun ba su sadakinsu. Kada kuma ku riqe igiyar auren mata kafirai, ku tambayi abin da kuka kashe, su ma su tambayi abin da suka kashe[1]. Wannan shi ne hukuncin Allah da Yake hukuntawa a tsakaninku. Allah kuma Masani ne, Mai hikima
1- Watau duk matan da suka yi ridda suka gudu zuwa wajen kafirai, to Musulmi su nemi kafiran su biya su abin da suka kashe wajen auren su. Su ma kafiran su nemi Musulmi su biya su sadakin matansu da suka musulunta suka gudo wajen Musulmi.
وَإِن فَاتَكُمۡ شَيۡءٞ مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ إِلَى ٱلۡكُفَّارِ فَعَاقَبۡتُمۡ فَـَٔاتُواْ ٱلَّذِينَ ذَهَبَتۡ أَزۡوَٰجُهُم مِّثۡلَ مَآ أَنفَقُواْۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ أَنتُم بِهِۦ مُؤۡمِنُونَ
Idan wasu matanku sun guje muku zuwa ga kafirai, sai kuka yi yaqi kuka samu galaba, to ku bai wa waxanda matansu suka guje musu kamar abin da suka kashe[1]. Ku kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda kuke imani da Shi
1- Watau daga ganimar da aka samu ta yaqi.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ يُبَايِعۡنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشۡرِكۡنَ بِٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡرِقۡنَ وَلَا يَزۡنِينَ وَلَا يَقۡتُلۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ وَلَا يَأۡتِينَ بِبُهۡتَٰنٖ يَفۡتَرِينَهُۥ بَيۡنَ أَيۡدِيهِنَّ وَأَرۡجُلِهِنَّ وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي مَعۡرُوفٖ فَبَايِعۡهُنَّ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُنَّ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Ya kai wannan Annabi, idan muminai mata suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirka da Allah ba, kuma ba za su yi sata ba, ba kuma za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kuma ba za su zo da wani qage ba wanda za su qirqira (game da xan da suka haifa) a tsakanin hannayensu da qafafuwansu[1], kuma ba za su sava maka ba game da wani aiki na kirki, to sai ka yi musu mubaya’a, ka kuma nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
1- Kamar yadda suke yi a jahiliyya idan mace ta yi zina da mazaje da yawa sai ta zavi xaya ta danganta masa xan da ta haifa.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ قَدۡ يَئِسُواْ مِنَ ٱلۡأٓخِرَةِ كَمَا يَئِسَ ٱلۡكُفَّارُ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡقُبُورِ
Ya ku waxanda kuka yi imani, kada ku jivinci mutanen da Allah ya yi fushi da su[1], haqiqa sun xebe qauna daga lahira kamar yadda kafirai suka xebe qauna daga na qabarurruka[2]
1- Su ne Yahudawan, waxanda saboda yawan savonsu da kafircinsu har Allah ya yi fushi da su.
2- Watau bayan an nuna musu makomarsu a wutar jahannama suka fitar da tsammanin samun kuvuta a ranar alqiyama.
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa ya yi tasbihi ga Allah; Shi kuma Mabuwayi ne, Mai hikima