مَّلۡعُونِينَۖ أَيۡنَمَا ثُقِفُوٓاْ أُخِذُواْ وَقُتِّلُواْ تَقۡتِيلٗا
(Su) la’anannu ne; duk inda aka gamu da su a kama su, kuma a yi musu mummunan kisa
سُنَّةَ ٱللَّهِ فِي ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلُۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّةِ ٱللَّهِ تَبۡدِيلٗا
(Wannan) Sunnar Allah ce ga waxanda suka gabata a da; ba kuma za ka sami wani canji ba game da sunnar Allah
يَسۡـَٔلُكَ ٱلنَّاسُ عَنِ ٱلسَّاعَةِۖ قُلۡ إِنَّمَا عِلۡمُهَا عِندَ ٱللَّهِۚ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ تَكُونُ قَرِيبًا
Mutane suna tambayar ka game da (ranar) alqiyama; ka ce (da su): “Saninta a wajen Allah kawai yake.” Ba ka sani ba ko watakila alqiyamar za ta kasance kusa
إِنَّ ٱللَّهَ لَعَنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمۡ سَعِيرًا
Lalle Allah Ya la’anci kafirai Ya kuma tanadar musu da (wutar) Sa’ira
خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا
Masu dawwama ne a cikinta har abada; ba kuma za su sami wani majivinci ko mataimaki ba
يَوۡمَ تُقَلَّبُ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ يَقُولُونَ يَٰلَيۡتَنَآ أَطَعۡنَا ٱللَّهَ وَأَطَعۡنَا ٱلرَّسُولَا۠
A ranar da za a riqa jujjuya fuskokinsu cikin wuta, suna cewa: “Kaiconmu, ina ma da mun bi Allah mun bi Manzo!”
وَقَالُواْ رَبَّنَآ إِنَّآ أَطَعۡنَا سَادَتَنَا وَكُبَرَآءَنَا فَأَضَلُّونَا ٱلسَّبِيلَا۠
Suka kuma ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu mun bi shugabanninmu da manyanmu sai suka vatar da mu hanya
رَبَّنَآ ءَاتِهِمۡ ضِعۡفَيۡنِ مِنَ ٱلۡعَذَابِ وَٱلۡعَنۡهُمۡ لَعۡنٗا كَبِيرٗا
“Ya Ubangijinmu, Ka ba su azaba rivi biyu, Ka kuma la’ance su babbar la’ana.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ ءَاذَوۡاْ مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ ٱللَّهُ مِمَّا قَالُواْۚ وَكَانَ عِندَ ٱللَّهِ وَجِيهٗا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku zamanto kamar waxanda suka cuci Musa sai Allah Ya wanke shi daga abin da suka faxa (a kansa). Ya kuma kasance mai alfarma ne a wurin Allah
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَقُولُواْ قَوۡلٗا سَدِيدٗا
Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku faxi Magana wadda take daidai ce
يُصۡلِحۡ لَكُمۡ أَعۡمَٰلَكُمۡ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَقَدۡ فَازَ فَوۡزًا عَظِيمًا
Zai kyautata muku ayyukanku, Ya kuma gafarta muku zunubanku. Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa, to haqiqa ya rabauta rabauta mai girma
إِنَّا عَرَضۡنَا ٱلۡأَمَانَةَ عَلَى ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡجِبَالِ فَأَبَيۡنَ أَن يَحۡمِلۡنَهَا وَأَشۡفَقۡنَ مِنۡهَا وَحَمَلَهَا ٱلۡإِنسَٰنُۖ إِنَّهُۥ كَانَ ظَلُومٗا جَهُولٗا
Lalle Mun bijiro da amana[1] ga sammai da qasa da duwatsu sai suka qi xaukar ta suka ji tsoron ta, sai kuwa mutum ya xauke ta; lalle shi (mutum) ya kasance mai zaluntar kansa ne, mai jahilci
1- Amana a nan, su ne dokokin shari’a na umarni da hani.
لِّيُعَذِّبَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ وَيَتُوبَ ٱللَّهُ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمَۢا
Don Allah Ya azabtar da munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata, Ya kuma karvi tubar muminai maza da muminai mata. Allah kuwa Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai
ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلۡأٓخِرَةِۚ وَهُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡخَبِيرُ
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Wanda duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne, kuma godiya ta tabbata a gare Shi a lahira. Shi kuwa Mai hikima ne, Masani
يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۚ وَهُوَ ٱلرَّحِيمُ ٱلۡغَفُورُ
Yana sane da abin da yake shiga cikin qasa da abin da yake fitowa daga cikinta, da kuma abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa cikinta. Kuma Shi Mai rahama ne, Mai gafara
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَأۡتِينَا ٱلسَّاعَةُۖ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتَأۡتِيَنَّكُمۡ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِۖ لَا يَعۡزُبُ عَنۡهُ مِثۡقَالُ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَآ أَصۡغَرُ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكۡبَرُ إِلَّا فِي كِتَٰبٖ مُّبِينٖ
Kuma waxanda suka kafirta suka ce: “Ranar alqiyama ba za ta zo mana ba.” Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina, tabbas za ta zo muku, (Allah) Shi ne Masanin gaibu; ba abin da yake voye a gare Shi; daidai da qwayar zarra a cikin sammai ko a qasa, ko wanda ya fi wannan qanqanta ko ya fi girma, face yana nan (a rubuce) a cikin Lauhul-Mahafuzu
لِّيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ
“Don Ya saka wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka kyawawa. Waxannan suna da gafara da arziki na karamci.”
وَٱلَّذِينَ سَعَوۡ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مِّن رِّجۡزٍ أَلِيمٞ
Waxanda kuwa suka yi varna a cikin ayoyinmu don su nuna gazawarmu[1], waxannan suna da mummunar azaba mai raxaxi
1- Watau suna sukar ayoyin Allah da cewa sihiri ne ko bokanci ko waqa.
وَيَرَى ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ هُوَ ٱلۡحَقَّ وَيَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Waxanda aka bai wa ilimi kuma suna ganin abin da aka saukar maka daga Ubangijinka shi ne gaskiya, kuma yana shiryarwa ne zuwa hanyar (Allah) Mabuwayi, Sha-yabo
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هَلۡ نَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ يُنَبِّئُكُمۡ إِذَا مُزِّقۡتُمۡ كُلَّ مُمَزَّقٍ إِنَّكُمۡ لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدٍ
Waxanda suka kafirta suka ce: “Shin ma nuna muku wani mutum da zai ba ku labarin cewa, idan an yayyaga ku yugu-yugu lallai za ku dawo cikin wata halitta sabuwa?
أَفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا أَم بِهِۦ جِنَّةُۢۗ بَلِ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ فِي ٱلۡعَذَابِ وَٱلضَّلَٰلِ ٱلۡبَعِيدِ
“Shin ya yi wa Allah qarya ne, ko kuma yana da wani tavin hankali ne?” Ba haka ba ne, waxanda ba sa yin imani da lahira suna cikin azaba da vata mai nisa
أَفَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَىٰ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِن نَّشَأۡ نَخۡسِفۡ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضَ أَوۡ نُسۡقِطۡ عَلَيۡهِمۡ كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّكُلِّ عَبۡدٖ مُّنِيبٖ
Ba sa dubawa su ga abin da yake gabansu da abin da yake bayansu na sama da qasa? In da Mun ga dama sai Mu nutsar da su cikin qasa ko kuma Mu rufto musu da wani yanki daga sama. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga duk wani bawa mai komawa ga Allah
۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ مِنَّا فَضۡلٗاۖ يَٰجِبَالُ أَوِّبِي مَعَهُۥ وَٱلطَّيۡرَۖ وَأَلَنَّا لَهُ ٱلۡحَدِيدَ
Kuma haqiqa Mun bai wa Dawuda falala daga gare Mu; cewa: “Ya ku duwatsu ku riqa amsa tasbihi tare da shi,” da kuma tsuntsaye; Muka kuma tausasa masa qarfe
أَنِ ٱعۡمَلۡ سَٰبِغَٰتٖ وَقَدِّرۡ فِي ٱلسَّرۡدِۖ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
(Muka ce da shi): “Ka riqa yin cikakken silke, kuma ka kintata wajen yin saqar; kuma (kai Dawuda da iyalinka) ku yi ayyuka nagari; lalle Ni Mai ganin abin da kuke aikatawa ne.”
وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ غُدُوُّهَا شَهۡرٞ وَرَوَاحُهَا شَهۡرٞۖ وَأَسَلۡنَا لَهُۥ عَيۡنَ ٱلۡقِطۡرِۖ وَمِنَ ٱلۡجِنِّ مَن يَعۡمَلُ بَيۡنَ يَدَيۡهِ بِإِذۡنِ رَبِّهِۦۖ وَمَن يَزِغۡ مِنۡهُمۡ عَنۡ أَمۡرِنَا نُذِقۡهُ مِنۡ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ
Kuma (Muka hore wa) Sulaimanu iska, tafiyarta ta safe wata guda ce, ta yamma ma kuma wata guda ce; Muka kuma vuvvugo masa da narkakkiyar tagulla tana gudana. Daga aljannu kuma akwai masu aiki a wajensa da umarnin Ubangijinsa; wanda kuwa ya kauce wa umarninmu daga cikinsu, to za Mu xanxana masa azabar wutar Sa’ira
يَعۡمَلُونَ لَهُۥ مَا يَشَآءُ مِن مَّحَٰرِيبَ وَتَمَٰثِيلَ وَجِفَانٖ كَٱلۡجَوَابِ وَقُدُورٖ رَّاسِيَٰتٍۚ ٱعۡمَلُوٓاْ ءَالَ دَاوُۥدَ شُكۡرٗاۚ وَقَلِيلٞ مِّنۡ عِبَادِيَ ٱلشَّكُورُ
Suna aikata masa abubuwan da yake bukata na manya-manyan gine-gine[1] da mutum-mutumi[2] da akusa manya-manya kamar tafkuna da kafaffun tukwane. Ya ku iyalin Dawuda, ku yi aikin (xa’a) domin godiya. Masu godiya daga bayina kuwa kaxan ne
1- Watau wuraren ibada.
2- A wancan lokacin ba a haramta yin su ba. Sai bayan zuwan Annabi () ne ya haramta suranta su ko gina su.
فَلَمَّا قَضَيۡنَا عَلَيۡهِ ٱلۡمَوۡتَ مَا دَلَّهُمۡ عَلَىٰ مَوۡتِهِۦٓ إِلَّا دَآبَّةُ ٱلۡأَرۡضِ تَأۡكُلُ مِنسَأَتَهُۥۖ فَلَمَّا خَرَّ تَبَيَّنَتِ ٱلۡجِنُّ أَن لَّوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٱلۡغَيۡبَ مَا لَبِثُواْ فِي ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ
Sannan lokacin da Muka qaddara masa mutuwa ba abin da ya nuna musu mutuwarsa sai gara da ta riqa cin sandarsa[1]; to lokacin da ya faxi sai aljannu suka gane cewa da sun san gaibu da ba su zauna cikin azabar wulaqanci ba
1- Sandarsa da yake tsaye a kanta.
لَقَدۡ كَانَ لِسَبَإٖ فِي مَسۡكَنِهِمۡ ءَايَةٞۖ جَنَّتَانِ عَن يَمِينٖ وَشِمَالٖۖ كُلُواْ مِن رِّزۡقِ رَبِّكُمۡ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥۚ بَلۡدَةٞ طَيِّبَةٞ وَرَبٌّ غَفُورٞ
Haqiqa akwai aya game da gidajen qabilar Saba’u (ta qasar Yaman); ita ce gonakai guda biyu na lambu a hagu da dama; (aka ce da su): “Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku gode masa. Qasa ce mai daxin zama da kuma Ubangiji mai gafara
فَأَعۡرَضُواْ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ سَيۡلَ ٱلۡعَرِمِ وَبَدَّلۡنَٰهُم بِجَنَّتَيۡهِمۡ جَنَّتَيۡنِ ذَوَاتَيۡ أُكُلٍ خَمۡطٖ وَأَثۡلٖ وَشَيۡءٖ مِّن سِدۡرٖ قَلِيلٖ
Sai suka bijire, sai Muka aiko musu da ambaliyar madatsar ruwan Arimu, Muka kuma musanya musu gonakin nan nasu biyu da wasu gonakin biyu ma’abota ‘ya’ya masu xaci da kuma itacen tsamiya, da wani abu kaxan na ‘ya’yan magarya
ذَٰلِكَ جَزَيۡنَٰهُم بِمَا كَفَرُواْۖ وَهَلۡ نُجَٰزِيٓ إِلَّا ٱلۡكَفُورَ
Wannan shi ne Muka saka musu (da shi) saboda kafircinsu; ba kuwa Ma yin sakamako (irin wannan) sai ga mai butulci