السورة: Suratul Furqan

الآية : 51

وَلَوۡ شِئۡنَا لَبَعَثۡنَا فِي كُلِّ قَرۡيَةٖ نَّذِيرٗا

Da kuma Mun ga dama, lalle da mun aiko wani mai gargaxi cikin kowacce alqarya[1]


1- Amma bai yi haka ba, sai ya aiko Annabi Muhammadu () shi kaxai zuwa ga talikai baki xaya.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 52

فَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَجَٰهِدۡهُم بِهِۦ جِهَادٗا كَبِيرٗا

To kada ka bi son ran kafirai kuma ka yaqe su da shi (Alqur’ani) yaqi mai girma



السورة: Suratul Furqan

الآية : 53

۞وَهُوَ ٱلَّذِي مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ هَٰذَا عَذۡبٞ فُرَاتٞ وَهَٰذَا مِلۡحٌ أُجَاجٞ وَجَعَلَ بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٗا وَحِجۡرٗا مَّحۡجُورٗا

Shi ne kuma wanda Ya haxa koguna biyu: wannan mai tsananin daxi wannan kuma mai tsananin zartsi, Ya kuma sanya shamaki a tsakaninsu da kuma kariya mai karewa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 54

وَهُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ مِنَ ٱلۡمَآءِ بَشَرٗا فَجَعَلَهُۥ نَسَبٗا وَصِهۡرٗاۗ وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرٗا

Shi ne kuma wanda Ya halicci mutum daga ruwa sannan Ya mayar da shi dangantaka da surukuta. Ubangijinka Ya kasance Mai iko ne



السورة: Suratul Furqan

الآية : 55

وَيَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُهُمۡ وَلَا يَضُرُّهُمۡۗ وَكَانَ ٱلۡكَافِرُ عَلَىٰ رَبِّهِۦ ظَهِيرٗا

Kuma suna bauta wa wanin Allah abin da ba zai amfane su ba kuma ba zai cuce su ba. Kafiri kuwa ya kasance mai taimaka wa (Shaixan ne) a kan bijire wa Ubangijinsa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 56

وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Kuma ba Mu aiko ka ba sai kawai don ka zama mai albishir mai gargaxi



السورة: Suratul Furqan

الآية : 57

قُلۡ مَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍ إِلَّا مَن شَآءَ أَن يَتَّخِذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا

Ka ce (da su): “Ba na tambayar ku wani lada a kansa (gargaxin), sai dai ya rage ga wanda ya ga dama ya riqi hanya (ta gari) zuwa ga Ubangijinsa.”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 58

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡحَيِّ ٱلَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِهِۦۚ وَكَفَىٰ بِهِۦ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًا

Kuma ka dogara ga (Allah) Rayayye Wanda ba zai mutu ba, kuma ka yi tasbihi da godiyar sa, kuma Ya isa Masani ga zunuban bayinsa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 59

ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَسۡـَٔلۡ بِهِۦ خَبِيرٗا

(Shi ne) wanda Ya halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu cikin kwana shida, sannan Ya daidaita a kan Al’arshi. (Shi ne) Arrahmanu, sai ka tambayi Masani game da Shi



السورة: Suratul Furqan

الآية : 60

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱسۡجُدُواْۤ لِلرَّحۡمَٰنِ قَالُواْ وَمَا ٱلرَّحۡمَٰنُ أَنَسۡجُدُ لِمَا تَأۡمُرُنَا وَزَادَهُمۡ نُفُورٗا۩

Idan kuwa aka ce da su: “Ku yi sujjada ga Arrahmanu” sai su ce: “Mene ne Arrahmanu[1]? Yanzu ma yi sujjada ga abin da kake umartar mu?” (Wannan umarnin) kuma ya qara musu fanxarewa


1- Watau kafirai ba su yarda da sunan Allah Arrahmanu ba, kamar yadda ya zo a cikin Suratur Ra’ad, aya ta 30.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 61

تَبَارَكَ ٱلَّذِي جَعَلَ فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَجَعَلَ فِيهَا سِرَٰجٗا وَقَمَرٗا مُّنِيرٗا

Wanda Ya sanya wuraren saukar taurari cikin sama, Ya kuma sanya mata rana mai haske da wata mai haskakawa[1], albarkatunsa sun yawaita


1- Watau rana mai xauke da haske a karan-kanta da kuma wata wanda yake samun haskensa daga hasken rana.


السورة: Suratul Furqan

الآية : 62

وَهُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَ خِلۡفَةٗ لِّمَنۡ أَرَادَ أَن يَذَّكَّرَ أَوۡ أَرَادَ شُكُورٗا

Shi ne kuma wanda Ya sanya dare da rana masu maye wa juna ga wanda ya yi nufin ya wa’azantu ko kuma ya yi nufin godiya



السورة: Suratul Furqan

الآية : 63

وَعِبَادُ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلَّذِينَ يَمۡشُونَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ هَوۡنٗا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ ٱلۡجَٰهِلُونَ قَالُواْ سَلَٰمٗا

Bayin (Allah) Mai rahama kuwa (su ne) waxanda suke tafiya a bayan qasa a natse; idan kuma wawaye sun yi musu magana (sai) su faxa (musu) magana ta aminci



السورة: Suratul Furqan

الآية : 64

وَٱلَّذِينَ يَبِيتُونَ لِرَبِّهِمۡ سُجَّدٗا وَقِيَٰمٗا

(Su ne) kuma waxanda suke kwana suna masu sujjada da tsayuwa ga Ubangijinsu



السورة: Suratul Furqan

الآية : 65

وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا ٱصۡرِفۡ عَنَّا عَذَابَ جَهَنَّمَۖ إِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًا

(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka kawar mana da azabar Jahannama; lalle azabarta ta kasance halaka ce mai xorewa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 66

إِنَّهَا سَآءَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

“Lalle ita (Jahannama) ta kasance mummunar matabbata kuma mazauna (ga kafirai).”



السورة: Suratul Furqan

الآية : 67

وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَنفَقُواْ لَمۡ يُسۡرِفُواْ وَلَمۡ يَقۡتُرُواْ وَكَانَ بَيۡنَ ذَٰلِكَ قَوَامٗا

(Su ne) kuma waxanda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin qwauro, (ciyarwarsu) kuwa ta kasance tsaka-tsaki ce



السورة: Suratul Furqan

الآية : 68

وَٱلَّذِينَ لَا يَدۡعُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ وَلَا يَقۡتُلُونَ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَا يَزۡنُونَۚ وَمَن يَفۡعَلۡ ذَٰلِكَ يَلۡقَ أَثَامٗا

(Su ne) kuma waxanda ba sa bauta wa wani tare da Allah, kuma ba sa kashe ran da Allah Ya hana kashewa sai da haqqi, kuma ba sa yin zina. Wanda kuwa ya aikata hakan to zai haxu da (uqubar) laifinsa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 69

يُضَٰعَفۡ لَهُ ٱلۡعَذَابُ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَيَخۡلُدۡ فِيهِۦ مُهَانًا

Za a ninninka masa azaba ranar alqiyama, kuma ya dawwama a cikinta a wulaqance



السورة: Suratul Furqan

الآية : 70

إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ عَمَلٗا صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يُبَدِّلُ ٱللَّهُ سَيِّـَٔاتِهِمۡ حَسَنَٰتٖۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Sai dai wanda ya tuba ya kuma yi imani, kuma ya yi aiki na gari, to waxannan Allah zai musanya munanan ayyukansu da kyawawa. Allah kuwa ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



السورة: Suratul Furqan

الآية : 71

وَمَن تَابَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَإِنَّهُۥ يَتُوبُ إِلَى ٱللَّهِ مَتَابٗا

Wanda kuwa ya tuba ya kuma yi aiki na gari, to lalle shi ne wanda yake tuba na gaskiya zuwa ga Allah



السورة: Suratul Furqan

الآية : 72

وَٱلَّذِينَ لَا يَشۡهَدُونَ ٱلزُّورَ وَإِذَا مَرُّواْ بِٱللَّغۡوِ مَرُّواْ كِرَامٗا

(Su ne) kuma waxanda ba sa halartar wuraren baxala, idan kuma suka wuce ta wurin aikin assha to sai su wuce suna masu mutunta kansu



السورة: Suratul Furqan

الآية : 73

وَٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَمۡ يَخِرُّواْ عَلَيۡهَا صُمّٗا وَعُمۡيَانٗا

(Su ne) kuma waxanda idan aka yi musu wa’azi da ayoyin Ubangijinsu ba sa fuskantar su suna kurame kuma makafi



السورة: Suratul Furqan

الآية : 74

وَٱلَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبۡ لَنَا مِنۡ أَزۡوَٰجِنَا وَذُرِّيَّـٰتِنَا قُرَّةَ أَعۡيُنٖ وَٱجۡعَلۡنَا لِلۡمُتَّقِينَ إِمَامًا

(Su ne) kuma waxanda suke cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka ba mu masu sanyaya mana zukata daga matayenmu da zuri’armu, kuma Ka sanya mu abin koyi ga masu taqawa



السورة: Suratul Furqan

الآية : 75

أُوْلَـٰٓئِكَ يُجۡزَوۡنَ ٱلۡغُرۡفَةَ بِمَا صَبَرُواْ وَيُلَقَّوۡنَ فِيهَا تَحِيَّةٗ وَسَلَٰمًا

Waxannan su ne ake saka wa da xakuna na Aljanna saboda haqurin da suka yi, za kuma a tare su a cikinta da gaisuwa da sallama



السورة: Suratul Furqan

الآية : 76

خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ حَسُنَتۡ مُسۡتَقَرّٗا وَمُقَامٗا

Suna madawwama a cikinta. Matabbata da mazauni sun kyautata



السورة: Suratul Furqan

الآية : 77

قُلۡ مَا يَعۡبَؤُاْ بِكُمۡ رَبِّي لَوۡلَا دُعَآؤُكُمۡۖ فَقَدۡ كَذَّبۡتُمۡ فَسَوۡفَ يَكُونُ لِزَامَۢا

Ka ce: “Ba ruwan Ubangijina da ku in ba don ibadarku ba; to ga shi kun qaryata, to wannan (sakamakonsa) zai zama azaba ce mai xorewa[1].”


1- Watau ba domin bayinsa na gari waxanda suke bauta masa kuma suna roqon sa ba, da ba ruwansa da su domin sun qaryata Manzon Allah ().


السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 1

طسٓمٓ

XA SIN MIM



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 2

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ

Waxannan ayoyi ne na Littafi mabayyani



السورة: Suratus Shu’ara

الآية : 3

لَعَلَّكَ بَٰخِعٞ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ

Ko za ka kashe kanka ne don ba su zama muminai ba?