السورة: Suratul Kafirun

الآية : 6

لَكُمۡ دِينُكُمۡ وَلِيَ دِينِ

“Addininku na gare ku, ni ma kuma addinina na gare ni[1].”


1- Annabi () ya ga wani yana karanta wannan Surar sai ya ce: “Amma dai wannan haqiqa ya kuvuta daga shirka”.


السورة: Suratun Nasr

الآية : 1

إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ وَٱلۡفَتۡحُ

Idan nasarar Allah ta zo da kuma buxe (Makka)



السورة: Suratun Nasr

الآية : 2

وَرَأَيۡتَ ٱلنَّاسَ يَدۡخُلُونَ فِي دِينِ ٱللَّهِ أَفۡوَاجٗا

Ka kuma ga mutane suna shiga addinin Allah qungiya-qungiya



السورة: Suratun Nasr

الآية : 3

فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَٱسۡتَغۡفِرۡهُۚ إِنَّهُۥ كَانَ تَوَّابَۢا

To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karvar tuba ne



السورة: Suratul Masad

الآية : 1

تَبَّتۡ يَدَآ أَبِي لَهَبٖ وَتَبَّ

Hannayen Abu Lahabi[1] sun halaka, shi ma kuma ya halaka


1- Abu Lahab, xaya ne daga baffannin Manzon Allah wanda ya nuna wa Annabi () qiyayya ya mutu yana kafiri.


السورة: Suratul Masad

الآية : 2

مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُ مَالُهُۥ وَمَا كَسَبَ

Dukiyarsa da abin da ya tsuwurwurta ba su amfana masa komai ba



السورة: Suratul Masad

الآية : 3

سَيَصۡلَىٰ نَارٗا ذَاتَ لَهَبٖ

Ba da daxewa ba zai shiga wuta mai balbali



السورة: Suratul Masad

الآية : 4

وَٱمۡرَأَتُهُۥ حَمَّالَةَ ٱلۡحَطَبِ

Da kuma matarsa mai yawan xaukar kayan qaya[1]


1- Watau Ummu Jamil, ta kasance tana zuba wa Annabi () qaya a kan hanyarsa domin ya taka.


السورة: Suratul Masad

الآية : 5

فِي جِيدِهَا حَبۡلٞ مِّن مَّسَدِۭ

A wuyanta akwai igiyar kaba mai ingantacciyar tukka. (a ranar alqiyama)



السورة: Suratul Ikhlas

الآية : 1

قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ

Ka ce: “Shi Allah Xaya ne[1]


1- Watau a Zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, kuma shi kaxai ya cancanci a bauta masa.


السورة: Suratul Ikhlas

الآية : 2

ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ

“Allah Abin nufa da buqatu[1]


1- Watau wanda shugabanci ya tuqe zuwa gare shi, domin ya tattara dukkan siffofin kamala da xaukaka.


السورة: Suratul Ikhlas

الآية : 3

لَمۡ يَلِدۡ وَلَمۡ يُولَدۡ

“Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba



السورة: Suratul Ikhlas

الآية : 4

وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ

“Kuma babu wani da ya kasance kini a gare Shi[1].”


1- Domin babu mai kama da shi a sunayensa da siffofinsa da ayyukansa.


السورة: Suratul Falaq

الآية : 1

قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ

Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin asuba



السورة: Suratul Falaq

الآية : 2

مِن شَرِّ مَا خَلَقَ

“Daga sharrin abin da Ya halitta[1]


1- Watau duk wani mahluqi mai cutarwa, mutum ne ko aljani ko dabba.


السورة: Suratul Falaq

الآية : 3

وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ

“Da kuma sharrin dare idan ya lulluve da duhu



السورة: Suratul Falaq

الآية : 4

وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَٰتِ فِي ٱلۡعُقَدِ

“Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin qulle-qulle



السورة: Suratul Falaq

الآية : 5

وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ

“Da kuma sharrin mai hassada yayin da ya yi hassadar.”



السورة: Suratun Nas

الآية : 1

قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ

Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin mutane



السورة: Suratun Nas

الآية : 2

مَلِكِ ٱلنَّاسِ

“Sarkin mutane



السورة: Suratun Nas

الآية : 3

إِلَٰهِ ٱلنَّاسِ

“Abin bautar mutane



السورة: Suratun Nas

الآية : 4

مِن شَرِّ ٱلۡوَسۡوَاسِ ٱلۡخَنَّاسِ

“Daga sharrin mai sa waswasi[1], mai noqewa[2]


1- Watau kowane shaixani.


2- Watau duk sanda xan’adam ya ambaci Allah.


السورة: Suratun Nas

الآية : 5

ٱلَّذِي يُوَسۡوِسُ فِي صُدُورِ ٱلنَّاسِ

“Wanda yake yin waswasi a cikin qirazan mutane



السورة: Suratun Nas

الآية : 6

مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ

“Daga aljannu da na mutane[1].”


1- Watau shi wannan shaixani ana samun sa cikin mutane da aljanu.

---------------

------------------------------------------------------------

---------------

------------------------------------------------------------