أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصۡحَٰبِ ٱلۡفِيلِ
Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya yi wa ma’abota giwa[1] ba?
1- Watau runduna ce ta mayaqa daga qasar Yaman qarqashin jagorancin Abrahata, suka nufo Makka da niyyar rushe Xakin Ka’aba. A tare da su akwai wata babbar giwa. Allah ya hallaka su baki xaya..
أَلَمۡ يَجۡعَلۡ كَيۡدَهُمۡ فِي تَضۡلِيلٖ
Ashe bai mayar da makircinsu cikin watsewa ba?
وَأَرۡسَلَ عَلَيۡهِمۡ طَيۡرًا أَبَابِيلَ
Ya kuma aiko musu da tsuntsaye dodo-dodo?
تَرۡمِيهِم بِحِجَارَةٖ مِّن سِجِّيلٖ
Suna jifan su da duwatsu na qonanniyar laka?
فَجَعَلَهُمۡ كَعَصۡفٖ مَّأۡكُولِۭ
Sai da Ya mayar da su kamar karmami da aka cinye[1]?
1- Wannan babban abu ya auku ne a shekara ta 571 bayan haihuwar Annabi Isa (). A shekarar ne aka haifi Manzon Allah ().
لِإِيلَٰفِ قُرَيۡشٍ
Domin sabon da Quraishawa suka yi
إِۦلَٰفِهِمۡ رِحۡلَةَ ٱلشِّتَآءِ وَٱلصَّيۡفِ
Sabonsu na yin safara a lokacin xari (zuwa qasar Yaman) da lokacin bazara (zuwan qasar Sham)[1]
1- A cikin aminci ba tare da tsoron komai ba.
فَلۡيَعۡبُدُواْ رَبَّ هَٰذَا ٱلۡبَيۡتِ
To sai su bauta wa Ubangijin wannan Xakin[1]
1- Watau Xakin Ka’aba mai alfarma.
ٱلَّذِيٓ أَطۡعَمَهُم مِّن جُوعٖ وَءَامَنَهُم مِّنۡ خَوۡفِۭ
Wanda Ya ciyar da su daga yunwa, Ya kuma amintar da su daga tsoro
أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ
Shin ka ga wanda yake qaryata ranar sakamako?
فَذَٰلِكَ ٱلَّذِي يَدُعُّ ٱلۡيَتِيمَ
To shi ne wanda yake ingije maraya (daga haqqinsa)
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Ba kuma ya kwaxaitarwa wajen ciyar da miskini
فَوَيۡلٞ لِّلۡمُصَلِّينَ
To tsananin azaba ya tabbata ga masallata
ٱلَّذِينَ هُمۡ عَن صَلَاتِهِمۡ سَاهُونَ
Waxanda suke masu rafkana su bar sallarsu[1]
1- Watau ba sa yin ta a kan lokaci, ko ma su bar sallar a wasu lokuta ba tare da sun yi ta ba.
ٱلَّذِينَ هُمۡ يُرَآءُونَ
Waxanda su ne suke yin riya
وَيَمۡنَعُونَ ٱلۡمَاعُونَ
Suke kuma hana kayan taimako[1]
1- Watau ba sa bayar da zakkar dukiyoyinsu, ba sa taimaka wa masu buqata, ko kayan aro ba sa bayarwa.
إِنَّآ أَعۡطَيۡنَٰكَ ٱلۡكَوۡثَرَ
Lalle Mu Mun ba ka alheri mai yawa[1]
1- Watau qoramar Alkausara ta gidan Aljanna.
فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَٱنۡحَرۡ
To sai ka yi salla don Ubangijinka, ka kuma soke (abin hadayarka)
إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ ٱلۡأَبۡتَرُ
Lalle mai qin ka shi ne mai yankakken alheri[1]
1- Watau wanda a duk sanda aka tuna da shi za a yi tir da shi.
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ
Ka ce: “Ya ku waxannan kafirai
لَآ أَعۡبُدُ مَا تَعۡبُدُونَ
“Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba
وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ
“Ku kuma ba masu bautar abin da nake bauta wa ba ne
وَلَآ أَنَا۠ عَابِدٞ مَّا عَبَدتُّمۡ
“Ni kuma ba mai bauta wa abin da kuka bauta wa ba ne
وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ
“Ku ma ba za ku bauta wa abin da nake bauta wa ba
لَكُمۡ دِينُكُمۡ وَلِيَ دِينِ
“Addininku na gare ku, ni ma kuma addinina na gare ni[1].”
1- Annabi () ya ga wani yana karanta wannan Surar sai ya ce: “Amma dai wannan haqiqa ya kuvuta daga shirka”.
إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ وَٱلۡفَتۡحُ
Idan nasarar Allah ta zo da kuma buxe (Makka)
وَرَأَيۡتَ ٱلنَّاسَ يَدۡخُلُونَ فِي دِينِ ٱللَّهِ أَفۡوَاجٗا
Ka kuma ga mutane suna shiga addinin Allah qungiya-qungiya
فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَٱسۡتَغۡفِرۡهُۚ إِنَّهُۥ كَانَ تَوَّابَۢا
To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karvar tuba ne
تَبَّتۡ يَدَآ أَبِي لَهَبٖ وَتَبَّ
Hannayen Abu Lahabi[1] sun halaka, shi ma kuma ya halaka
1- Abu Lahab, xaya ne daga baffannin Manzon Allah wanda ya nuna wa Annabi () qiyayya ya mutu yana kafiri.
مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُ مَالُهُۥ وَمَا كَسَبَ
Dukiyarsa da abin da ya tsuwurwurta ba su amfana masa komai ba